GAME DA BATUN SUNAN "MUHAMMAD" A KAFET ƊIN SARKI SANUSI
• A fahimtata, bai dace ba kuma zuciyata ba za ta karɓi sanya sunan "MUHAMMADU" a ƙasa a taka ba! Ni gaskiya ba ni da wannan wayewar. Bokota ba ta kai wannan matakin ba. • Ƙurewar ADALCI shi ne ka ce; lallai Sanusi Lamiɗo ba ya sanya wancan sunan domin ɓata sunan asalin mai sunan ba! Amma fa mafi yawan musulmi ba za su iya ba, saboda sunan ba na wasa ba ne a gurinmu. • Al'ummar musulmi na masarautar Sanusi Lamiɗo sun nuna rashin jin daɗi da wannan al'amari, saboda a gurinsu "MUHAMMADU" wani suna ne da ba a wasa da shi! To, tunda Sanusi Lamiɗo ba zai cutu ba idan ya cire wannan sunan, sai ya duba maslahar al'umma ya cire don a zauna lafiya. • A wayewar boko irin ta Sanusi Lamiɗo ga kuma rawanin sarauta akansa, ba girmansa ba ne a riƙa cece-ku ce da shi akan wannan batun. Zai zama zubewar ƙima da darajar kujerar sarautarsa, ya riƙa fitowa yana yiwa al'ummar gari martani! Ina ma dai bai yi magana ba, ya yi dattaku, da lamarin bai yamutsa ha...