TATTAUNA MAS'ALOLIN SAƁANI


Wannan tambihin na malaminmu Mal. Nuhu Ubale Ibrahim (Abu Razina) Hafizahullah yana da matuƙar tsada, musamman a irin wannan yanayi da muke fama da matsaloli a sahar ilimi da harkokin da'awa a shafukan sada zumunta! Zagi, cin mutunci, habaici, gori da ƙoƙarin taɓa shakhsiyyar abokin saɓani, ko jifansa da wani mummunan laifi, su ne suka zama dalilai da ake kafa hujja da su a tsakanin ma'abota ilimi.

Su magabata suna yiwa wanda suka saɓa da shi ADALCI, da taƙaituwa cikin abin da suka saɓa na mas'aloli tare da kafa hujja da dalillai domin gamsar da juna da warware matsala a ilimance. 

Dattijon Sunnah Al-Imamu Ibnu Taimiyyah Rahimahullah a cikin مجموع الفتاوى (juz'i na 2) ya fitar da wata fa'idar mai tsadar gaske, game da yadda sahabban Manzon Allah ﷺ suka mu'amalanci junansu, bayan sun samu saɓanin cikin wata mas'ala ta ilimi:

"وأما الاختلاف في " الأحكام " فأكثر من أن ينضبط ولو كان كلما اختلف مسلمان في شيء تهاجرا لم يبق بين المسلمين عصمة ولا أخوة ولقد كان أبو بكر وعمر رضي الله عنهما سيدا المسلمين يتنازعان في أشياء لا يقصدان إلا الخير وقد قال النبي صلى الله عليه وسلم لأصحابه يوم بني قريظة : { لا يصلين أحد العصر إلا في بني قريظة فأدركتهم العصر في الطريق فقال قوم : لا نصلي إلا في بني قريظة وفاتتهم العصر . وقال قوم : لم يرد منا تأخير الصلاة فصلوا في الطريق فلم يعب واحدا من الطائفتين } . أخرجاه في الصحيحين من حديث ابن عمر . وهذا وإن كان في الأحكام فما لم يكن من الأصول المهمة فهو ملحق بالأحكام."

A ƙarƙashin wannan zance mai tsadar gaske za mu samu fa'idoji da dama. Daga cikinsu akwai:

• Saɓani cikin mas'alolin ilimi ba ya zama sababi na gaba da ƙiyayya tsakanin musulmi.

• Hatta manya-manyan sahabban Manzon Allah ﷺ mafiya daraja Sayyidina Abubakar (R.A) da Sayyidina Umar (R.A) suna samun saɓani cikin mas'alolin ilimi, amma bai taɓa zama dalili na jin haushi ko ƙiyayya ga junansu ba.

• Idan har sahabban da suka yi karatu a gaban malamin duniya bakiɗaya Annabi ﷺ za su iya samun saɓani, to ba abin mamaki ba ne don mu ƴan ƙarshen zamani mun samu saɓani cikin wata mas'ala ta addini.

• Duk yadda mas'ala ta kai ga fitowa fili ga wani cikin ma'abota ilimi, ba lallai ne ta bayyana irin haka ga wani daban ba! Ko dai saboda ilimi kogi ne, ko saboda shubuha ko kuma saboda wani dalili mai rauni da wanda ya saɓawa daidai cikin mas'alar zai iya faɗawa. Yi masa mu'amala ta ilimi ce kaɗai za ta sa ya fahimta ba aibanta shi ko jahiltar da shi ba.

• A cikin mas'alolin ilimi ba a yin zaɓi sonka, ko ƙungiyanci! Ba a ƙudirce wane shi ne akan gaskiya saboda ba tare da shi! Ko wane shi ne akan daidai tunda shi ne namu! Dalillai karɓaɓɓu daga tsotsuwar ilimi mai tsafta su ne ƙungiyar da ake zaɓa a ƙarfafa.

A ƙarshe, ƴan uwa masu albarka don Allah ku taƙaitawa gama-garin mutane kafar da za ta sanya a raina ilimi! Akwai mas'aloli masu nauyin da kwata-kwata tattauna su haka a social media yana buɗe ƙofar ɓarna musamman tsakanin waɗanda ba su san darajar ilimi ba!

#AddiniDaRayuwa #AdamSharada 

(C) Adam Sharada

Comments