RADICAL MUSLIM (MUSULMI MAI TSATTSAURAN RA'AYIN ADDINI)
A gurin ƴan boko aƙida idan kana riƙo da addinin Musulunci da gaske, sunanka "Radical Muslim" wai mai tsattsauran ra'ayin addini! Za ka ga tsangwama, da ƙiyayya da sharri kala-kala idan har za ka riƙe addinin Musulunci da gaske.
Alaji ka riƙe addininka da kyau, kada ƴan duniya su sa ka saki addininka. Duk inda ka shiga a duniya, ka nuna izzar musulunci da Sunnah.
Kada ka sake ka ji rauni ko ƙasƙanci ko kunya don ka zama musulmi nagari. Ka riƙa ɗaga kanka sama kana jin lallai kai mai daraja ne da tsada, saboda kana cikin mabiya Annabi Muhammad ﷺ.
#AddiniDaRayuwa #AdamSharada
Comments
Post a Comment