MATA MUSULMI DA BATSA A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA: INA MAFITA?



• A daidai lokacin da ake tsaka da fuskantar baƙin talauci a ƙasar nan, amma a haka ƴaƴan musulmi suka mayar da hankali akan yaɗa ɓarna a tsakanin al'umma!

• Yau batsa da nuna asalin surar halittar jikin ƴa mace, ya tashi daga al'aura (privacy), ta yadda da wuya ka shiga dandalin TikTok, Instagram, Snapchat ko Facebook Reel ba ka ci karo da mace musulma budurwa ƴat musulmi tana bayyanawa duniya su ba😭

• Ba wai batun kawai kalmomin batsa da nuna surar jiki ba, ƙiri da muzu ƴan matan suke runguma da sumbatar junansu da yin abubuwa masu tada sha'awa tsakanin mace da mace (lesbianism) a idon duniya!

• Kada ma ka so ka ji labarin yadda suke tonawa kawunansu asiri na irin badaƙalar da suke yi a ɓoye, tare da ambata sunaye da adireshin gurare.

• Zagi na maguzawa kuwa, wannan kusan ya zama jikinsu. Ta kai suna iya daukar video suna zagi mara daɗin ji ga wasu, tare da nunawa duniya ba tare da wata shakka ba.

• Abin da zai ƙara firgitaka shi ne yadda maza musulmi, manya masu shekaru da ya kamata a ce sun girma da ƴan samari masu tasowa suke rububin following da nuna yabawa ga irin waɗannan matan.

• In dai mace tana batsa da nuna tsiraicinta, to yanzu za ta samu miliyoyin mabiya masu yi mata caffa da yaba mata cikin musulmi ƴan Arewacin Najeriya 😭

• In dai mace ta sanya batsa ko tsiraicinta, ka duba comment section ka ga yadda maza gardawa suke rububin yaba mata, da ajiye lambobin wayarsu, neman ya za a yi su haɗu, nuna musu suna son su. Ba kunya ba tsoron Allah!

• Duk mai hankali zai ce waɗannan matan wai ba su da iyaye da ƴan uwa da dangi ne? Ko kuwa ba su da mafaɗa a cikin zuriyar gidajen da suka fito?

• Malamai da masu wa'azi suna iya ƙoƙarinsu wajen sauke nauyin da Allah (S.W.T) Ya ɗora musu. Sauran aikin ya shafi al'umma da hukumomi, musamman a jihohi irin Kano da ke da tasirin addinin Musulunci.

• Kowannenmu da ya san yana following wasu mutanen banza masu yaɗa ɓarna da buɗe ƙofar saɓon Allah, ya je ya dirtse (unfollowing) su. Ya daina yi musu liking da comment. Hakan zai dakushe ɓarnarsu daga trending a social media. A hannu guda kuma mu ƙarfafi shafukan mata masu yaɗa alkhairi da ilimi da tarbiyya, ta hanyar following, liking da sharing.

• Dole idan muna son kawo ƙarshen wannan ɓarnar sai mun yi shirin gaske! Dole kowa sai ya zama ɗan Hizba, kowa sai ya zama malami! Kowa sai ya zama "agent" na umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna.

• Duk wanda suka san a danginsu ko gidansu suna da irin wannan jarabawar, su yi iya yin su wajen dawo da ita kan hanya. Ta hanyar nasiha da faɗa, da kyakkyawar mu'amala da kuma yi musu addu'a tagari.

• Idan akwai wata a cikinsu da take ganin girmanka, ka yi amfani da wannan damar wajen faɗakarwa da wa'azi. Kada ka ce ka fita sabgarta kwata-kwata.

• Mata masu kamala da ruhin addini kuna da matuƙar amfani wajen yaƙar wannan ɓarnar. Kada ku yi Allah wadai da su, ku riƙa kusantarsu da nasiha da wa'azi da addu'a.

Allah ya yi mana maganin wannan masifa. Allah ya sauƙaƙa mana halin ƙuncin da muke ciki.

(C) Adam Sharada
 February 7, 2024
Madinatu Kano, Nigeria

Comments

Popular Posts