WARWARE SHUBUHOHIN MASU GANIN KAFIRAI ZA SU SHIGA ALJANNA!(Kashi na Farko)


A cikin wannan sakin layin na farko, ya kawo shubuhohi guda 3 kamar haka:

1- Faɗinsa: "Ba kowane kafiri ne zai shiga wuta ba."

Wannan zance ne kawai, wanda ba shi da wata madogara ta ilimi, da za ta iya tabbatar da shi, ko ta ƙarfafe shi. Asali, Allah (S.W.T) wanda Ya halicci halittu duka, ya aiko Annabawa da Manzanni da saƙon TAUHIDI zuwa ga dukkan duniya:

وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ فَمِنْهُمْ مَنْ هَدَى اللَّهُ وَمِنْهُمْ مَنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ الضَّلَالَةُ فَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانْظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
(An-Nahli: 36)

Wanda ya karɓi wanann saƙon da Manzanni suka zo da shi na TAUHIDI, ya tsayu akansa, shi ne asalin musulmi mai imani. Wanda ya wanzu cikin bautar ƊAGUTU, wannan shi ne KAFIRI! Ita kuma ALJANNA, babu wata aya a cikin Alƙur'ani maigirma ko Hadisi ingantacce zuwa ga Annabi Muhammad ﷺ da suka ce KAFIRI zai shige ta, ko dai a zahirinsu ko kuma a ma'anarsu.

Don mu gane wannan da'awar ta ilimi ce, su kawo dalili da yake goyon bayan wannan zancen nasu.

2- Faɗinsa cewa: "Sanin kowa ne akwai waɗanda ba musulmi ba amma za ka same su da kyawawan halaye da ɗabi'u a rayuwarsu da jama'a."

Wannan ma zance ne da shi ma ba komai ke cikinsa sai ko dai jahilci, son zuciya ko kuma shubuha. Amma, mu tafi cikin Alƙur'ani maigirma mu gani, shin a cikin siffofin waɗanda za su shiga ALJANNA akwai wannan? Sai mu dawo gurin shugabanmu Annabi Muhammad ﷺ mu ji daga gurinsa, shin su waye za su rabauta da samun aljanna ranar alƙiyama.

Alƙur'ani maigirma ya ambaci siffofi da dama na waɗanda za su shiga aljanna, daga ciki akwai:

I- Masu taƙawa (kiyaye dokokin Allah), ta hanyar nesantar abin da ya hana saboda tsoron azabarsa da kwaɗayin rahamarSa: 

وَسَارِعُوا إِلَى مَغْفِرَةٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ
(Āli Imrān 133)


II- Masu yiwa Allah (S.W.T) biyayya, ta hanyar yin ayyuka nagari, domin neman yardar Allah: 

وَبَشِّرِ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ
(Al-Baƙarah: 25)

III- Waɗanda suke saɓawa Allah (S.W.T) sannan su tuba saboda tsoron Allah da neman yardarSa:

إِلَّا مَنْ تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَأُولَئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ
(Maryam: 60)

IV- Ka karanta farko-farkon Suratu Al-Mu'uminū, daga aya ta 1 zuwa ta 11:

قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ (1) الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ (2) وَالَّذِينَ هُم ْعَنِ اللَّغْوِ مُعْرِضُونَ (3) وَالَّذِينَ هُمْ لِلزَّكَاةِ فَاعِلُونَ (4) وَالَّذِينَ هُمْ لِفُروجِهِمْ حَافِظُونَ (5) إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (6) فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاء ذَلِكَ فَأُوْلَئِكَ هُمُ الْعَادُون َ(7) وَالَّذِينَ همْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ (8) وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَوَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ(9) أُوْلَئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ (10) الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالدُونَ (11)

Kamar haka muke so su kawo mana a cikin Alƙur'ani maigirma, ko ingantaccen hadisi zuwa ga Manzon Allah ﷺ da ya goyi bayan wannan da'awar tasu!

Batun "kyakkyawan hali" ba shi da tasiri wajen bawa mutum tikitin tafiya aljanna, idan ba shi da asalin IMANI! Kamar yadda ayoyin da muka ɗan tsakuro suka yi nuni ƙarara. Duk iya mu'amalar mutum, duk halinsa idan ba shi da IMANI to wannan kam ba zai taɓa jiyo ƙamshin gidan aljanna ba.

Mu dawo ma'auninsu na HANKALI, ku yanzu don Allah wannan ita ce girmamawarku ga Annabi Muhammad ﷺ? Ku ce da wanda ya yi imani da shi, da wanda bai yi imani da shi ba duk za su shiga aljanna? Wannan ce ƙaunar da ku ke masa? Kun yiwa Sayyidina Aliyyu (R.A) da ƴaƴansa sharifai da ku ke da'awar ƙarya ta ƙaunarsu adalci, ku ce da su da kafirai duk za a haɗu a gidan aljanna? Kun yiwa Nana Faɗimah (R.A) shugabar matan aljanna kuma tsokar jikin Manzon Allah ﷺ adalci da kara kenan?

Nana Faɗimah (R.A) fa, ita ce Annabi Muhammad ﷺ yake ce mata, a cikin hadisin Al-Imamul Bukhari Rahimahullah na 2753:

حَدَّثَنَا أَبُو الْيَمَانِ ، أَخْبَرَنَا شُعَيْبٌ ، عَنِ الزُّهْرِيِّ ، قَالَ : أَخْبَرَنِي سَعِيدُ بْنُ الْمُسَيَّبِ ، وَأَبُو سَلَمَةَ بْنُ عَبْدِ الرَّحْمَنِ ، أَنَّ أَبَا هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ : قَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حِينَ أَنْزَلَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ : { وَأَنْذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ } قَالَ : " يَا مَعْشَرَ قُرَيْشٍ - أَوْ كَلِمَةً نَحْوَهَا - اشْتَرُوا أَنْفُسَكُمْ، لَا أُغْنِي عَنْكُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا، يَا بَنِي عَبْدِ مَنَافٍ، لَا أُغْنِي عَنْكُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا، يَا عَبَّاسُ بْنَ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، لَا أُغْنِي عَنْكَ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا، وَيَا صَفِيَّةُ عَمَّةَ رَسُولِ اللَّهِ، لَا أُغْنِي عَنْكِ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا، وَيَا فَاطِمَةُ بِنْتَ مُحَمَّدٍ، سَلِينِي مَا شِئْتِ مِنْ مَالِي، لَا أُغْنِي عَنْكِ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا ". تَابَعَهُ أَصْبَغُ ، عَنِ ابْنِ وَهْبٍ ، عَنْ يُونُسَ ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ 

Annabi ﷺ yana faɗawa Nana Faɗimah (R.A) cewa idan ba ta yi imani ba, ba zai iya fitar da ita a gaban Allah (S.W.T) ba! Kai kuma kana laluben hanyar da kafiri zai haɗu da su Nana Faɗimah a ALJANNA! Wane irin zalunci da jahilci ne wannan?

3- Bayan ya kawo batun ƙere-ƙere da cigaban kimiyya da fasaha da wasu cikin KAFIRAI suka kawo, sai ya cike da tambaya: "To yanzu waɗanda suka kawo wannan gagarumin cigaba ga al'umma, shin ba su cancanci wani sakamako daga Allah ba?"

AMSA
Wane sakamako ka ke tunanin su samu daga gurin Allah (S.W.T) wanda ba su samu ba? Wai ma shin sakamakon a nan duniya ka ke nufi ko a lahira? Idan a nan duniya ne, ga amsar tambayarka daga bakin Manzon Allah ﷺ kamar haka:

Al-Imamu Muslim rahimahullah ya fitar da hadisin Nana A'ishah (R.A) a lamba ta 214 da isnadinsa, Nana A'ishah tana cewa:

عن عائشة رضي الله عنها قالت: يا رسول الله، إن ابن جدعان كان في الجاهلية يصل الرحم ويطعم المسكين فهل ذاك نافعه؟ قال: لا ينفعه إنه لم يقل يوما رب اغفر لي خطيئتي يوم الدين.


Ta ce: Ya Manzon Allah ﷺ! Haƙiƙa Ibn Jud'ān ya kasance a lokacin jahiliyya mutum ne mai zumunci da ciyarwa ga mabuƙata. Shin wannan zai amfane shi? Sai Manzon Allah ﷺ ya ce "A'a, ba zai amfane shi ba! Domin bai taɓa cewa ya Ubangiji ka gafarta min zunubaina a ranar sakamako ba!"

Wato, Ibn Jud'ān bai tuba daga kafirci zuwa musulunci ba! Don haka aikinsa na banza da hofi ne.

Shi ya sa, wallahi tallahi billahi da a ce mutanen nan suna karatu muna kyautata musu zaton ba za su faɗa wannan mummunan ramin halakar na sukar Allah da ManzonSa a fakaice ba!

Malama Zainab Ahmad Muhammad ta ba mu saƙo mu ba su, ta ce "Waje ɗaya za su burge ni. Tunda sun yarda har wanda ba musulmi ba zai shiga aljanna, to su bar musuluncin mana!"

Allah ya jiƙinnAdibin ƙasar Hausa Malam Sa'adu Zungur, da ya ce:
Mu dai aikinmu faɗa muku
Ku yi kuka ko ku yi dariya
Dariyarku ta zam kuka gaba
Da nadamar mai ƙin gaskiya.

Za mu cigaba in sha Allah!

#AddiniDaRayuwa #AdamSharada 

(C) Adam Sharada 
Madinatu Kano, Nigeria 
16/07/1445 / 26/01/2024

Comments

Popular Posts