YADDA IBNU TAIMIYYA RAHIMAHULLAH YAKE GIRMAMA SAYYIDINA ALIYYU (R.A)
Ina karatu cikin مجموع الفتاوى ta Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya Rahimahullah, a juz'i na 24 babin SALLAR JUMA'A, a shafi na 113, inda aka tambayi Ibnu Taimiyya Rahimahullah game da halascin yin sallar Juma'a a gidan kurkuku (ga fursunoni) alhali akwai masallaci a cikin gari da ake yin Juma'a.
A cikin amsar Ibnu Taimiyya Rahimahullah ya bayar, sai yake cewa:
"Lokacin da Sayyidina Aliyyu (R.A) ya zama Halifa birnin ya koma birnin Kufa, garin ya tara mutane da yawa (da suka kwararo) a cikinsa. Sai (jama'a) suka ce masa: Ya sarkin muminai! Haƙiƙa a Madinah akwai dattawa da mutane masu rauni, waɗanda suna shan wahalar fita (sallar idi) zuwa bayan garin Madina (sahara)! Sai Sayyidina Aliyyu (R.A) ya naɗa musu limamin da zai musu sallar idi a masallaci. Limamin sai ya cigaba da yi musu sallah a inda ba bayan garin Madina ba. Gabanin lokacin (halifancin Sayyidina Aliyyu) ba haka ake yi ba!"
Ibnu Taimiyya Rahimahullah ya cigaba da cewa:
"Shi Sayyidina Aliyyu (R.A) yana cikin halifofin Manzon Allah ﷺ masu shiryarwa. Kuma dama Annabi ﷺ ya ce (game da su): "Ku yi riƙo da sunnata, da sunnar halifofin nan masu shiryarwa a bayana!" Duk wanda ya yi riƙo da karantarwa halifofin nan masu shiryarwa, haƙiƙa ya yi ɗa'a ga Allah da ManzonSa........"
TSOKACI
A gurin Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya Rahimahullah, Sayyidina Aliyyu ibn Abi Ɗalib (R.A) halifan Manzon Allah ﷺ ne, ɗaya daga cikin waɗanda Annabi ﷺ ya yi wasiyyar a yi riƙo da shiriyarsu. Kamar sauran ƴan uwan uwansa Sayyidina Abubakar (R.A), Sayyidina Umar (R.A), Sayyidina Usman (R.A) har ma da Sayyidina Alhasan (R.A) a zance mafi inganci!
#TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
Comments
Post a Comment