DAGA TASKAR IBN TAIMIYYA RAHIMAHULLAH 006
Shaikhul Islam Ibn Taimiyya Rahimahullah yana cewa:
"Idan bawa ya sanya addu'arsa ta zama SALATI ga Annabi Muhammad ﷺ , ya ishe shi Allah (S.W.T) Ya magance masa abin da ya dame shi a duniyarsa da lahirarsa. Domin kuwa duk lokacin da ya yiwa Annabi ﷺ salati guda goma (10), da a ce zai yiwa wasu ɗaiɗaikun muminai addu'a to Mala'iku za su ce "Allah Ya amsa, kai ma ya ba ka kwatankwacin abin da ka roƙa musu!", to addu'arsa (salati) ga Annabi ﷺ ta fi wannan addu'ar ga (sauran mutane) falala da daraja!"
- Majmū'ul Fatāwā 1/193
DARASI
Wannan zance shaida ce game da yadda Shaikhul Islam Ibn Taimiyya Rahimahullah yake tsananin girmama Annabi Muhammad ﷺ, tare da ba shi maɗaukakin fifiko akan dukkan halittun Allah (S.W.T). Ta yadda yi masa SALATI ﷺ yake sama da yin kowace irin addu'a a gurinsa.
Saɓani yadda maƙiyansa ke yi masa mummunar tarjama musamman domin tunzura jahilai zuwa ga ƙinsa; saboda ko dai jahilci na rashin karanta littattafansa, ko kuma saboda zalunci na ƙiyayyar da suke masa sakamakon tsayuwarsa wajen kare Tauhidi da Sunnah, ko kuma a ƴan tsirarun lokuta saboda wata shubuha da aka sanyawa zukatansu game da shi.
Allah ya kyauta makwancin dattijon Sunnah Shaikhul Islam Ibn Taimiyya.
#TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
Comments
Post a Comment