DAGA TASKAR IBN TAIMIYYA RAHIMAHULLAH 002
"Duk abin da ya kasance BIDI'A a cikin addini, wadda ita a cikin Alƙur'ani maigirma, babu a cikin ingantacciyar Sunnar Annabi ﷺ; to wannan (aikin) ko wane ya faɗa, kuma kowane ya yi aikin, ba aikin shari'a ba ne! Domin Allah Subhanahu Wa Ta'ala ba ya son irin wannan aikin, kuma ManzonSa ﷺ ma ba ya son shi. Don haka (aikin) ba zai taɓa shiga cikin kyawawan ayyuka ba, ba kuma zai zama aiki nagari ba! Kamar yadda duk wanda ya aikata aikin da bai halatta (a aikata) ba, kamar yaɗa ɓarna a ban ƙasa da zalunci, su ma ba za su shiga cikin kyawawan ayyuka (da Allah zai karɓa) ba,ba kuma za su taɓa zama ayyuka nagari ba!"
- Al-Ubudiyyah shf 55
#TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
Comments
Post a Comment