SUN ƘARA YUNƘUROWA WAJEN CUSA WANDA BA MUSULMI BA GIDAN ALJANNA!
SHIMFIƊA
Musulmi nagari shi ne wanda yake cirato addininsa daga Alƙur'ani maigirma da Sunnar Manzon Allah ﷺ. Babbar matsalar da ƴan boko waɗanda suka tasirantu da barbarar falsafa da logic suke fama da ita; auna addinin Musulunci da zantukan malamansu na Falsafa waɗanda yanyawa ne na maguzawan Girkawa. Shi ya sa ba ka taɓa samunsu suna maƙalewa ayoyi da hadisai wajen tattauna wata mas'ala, sai dai hankali da ma'aunin ra'ayoyin malamansu na falsafa.
Da a ce suna karanta Alƙur'ani maigirma tare da tadabburin ayoyinsa, kuma sun rabauta da sanin usul na ilimi tun daga tushe, da kuma kyautata musu zaton ba za su riƙa sunanta addini da muguwar falsafa da ƙazamin logic ba.
A cikin Suratu Āli Imrān aya ta 85, Allah (S.W.T) Yana cewa:
وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَن يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Don Allah mai karatu, ka yi amfani da ɗan ilimin da Allah (S.W.T) Ya ba ka ka duba ayar, ko ka samu wani ɗalibin ilimi mu zauna ku nazarci ayar nan ta fuskoki 5:
1- Sababin saukarta
2- Yadda ta zo a tsakanin ayoyi (siyāƙi)
3- Zantukan malaman Tafsiri game da ma'anarta
4- Ƙa'idojin harshen Larabci a cikin ayar (Nahwu, Balagha)
5- Natijar ma'anar ayar
Za ku ƙara tabbatar da abin da Al-Imamul Ghazāliy ya yiwa littafinsa take da "تهافة الفلاسفة", wato shirme da shashancin ma'abota Falsafa.
Zan yi dogon sharhi akan wannan shubuhar in sha Allah.
#AddiniDaRayuwa #AdamSharada
(C) Adam Sharada
January 22, 2024
Comments
Post a Comment