MALAMAN GASKIYA DA MALAMAN FADA 001



Al-Hāfiz Ibnu AbdulBarrin Rahimahullah a cikin كتاب جامع بيان العلم وفضله (juz'i na 1, shf 640) athar mai lamba 1107, ya kawo maganar Sufyan At-Thauri (161 BH) Rahimahullah da yake cewa:

"كان خيار الناس وأشرافهم والمنظور إليهم في الدين الذين يقومون إلى هؤلاء الأمراء فيأمرونهم وينهونهم، وكان آخرون يلزمون بيوتهم ليسوا عندهم بشيء."

Ma'ana:

"Mafiya alkhairin mutane, mafiya falala waɗanda ake girmamawa a cikin addini (malamai na Allah), suna zuwa takanas gaban waɗannan SHUGABANNIN su yi musu umarni da kyakkyawa kuma su hana su mummuna! Su kuma wasu malaman (malaman faɗa), suna tarewa ne a gindin masu mulki, ba sa tsinana komai (na umarni ko hani) gare su!"

#Malamai #AddiniDaRayuwa #AdamSharada

Comments