GAME DA BATUN SUNAN "MUHAMMAD" A KAFET ƊIN SARKI SANUSI


• A fahimtata, bai dace ba kuma zuciyata ba za ta karɓi sanya sunan "MUHAMMADU" a ƙasa a taka ba! Ni gaskiya ba ni da wannan wayewar. Bokota ba ta kai wannan matakin ba.

• Ƙurewar ADALCI shi ne ka ce; lallai Sanusi Lamiɗo ba ya sanya wancan sunan domin ɓata sunan asalin mai sunan ba! Amma fa mafi yawan musulmi ba za su iya ba, saboda sunan ba na wasa ba ne a gurinmu.

• Al'ummar musulmi na masarautar Sanusi Lamiɗo sun nuna rashin jin daɗi da wannan al'amari, saboda a gurinsu "MUHAMMADU" wani suna ne da ba a wasa da shi! To, tunda Sanusi Lamiɗo ba zai cutu ba idan ya cire wannan sunan, sai ya duba maslahar al'umma ya cire don a zauna lafiya.

• A wayewar boko irin ta Sanusi Lamiɗo ga kuma rawanin sarauta akansa, ba girmansa ba ne a riƙa cece-ku ce da shi akan wannan batun. Zai zama zubewar ƙima da darajar kujerar sarautarsa, ya riƙa fitowa yana yiwa al'ummar gari martani! Ina ma dai bai yi magana ba, ya yi dattaku, da lamarin bai yamutsa hazo irin haka ba.

• Sarakunan gargajiya irin Sanusi Lamiɗo ya kamata su riƙa tuna, addinin Musulunci shi ne ya kafa su ya wanzar da kujerun da suke kai! Bai kamata su janyowa daular Ɗanfodiyo abin surutu ba!

• Don Allah idan zai yiwu gwamnatin Kano ta sa Sanusi Lamiɗo ya cire wannan sunan, ya bar sunansa da aka sani, wanda aka rubuta a jikin takardunsa na makaranta. Sunan da aka rubuta a jikin kuɗin Najeriya (Naira ₦) lokacin da yana gwamnan banki.

#AddiniDaRayuwa #AdamSharada

Comments

  1. Akidar mu itace kirmama Manzon Allah kawai ta hanyar da tadace Babu ruwan mu da wani fahimtar karatun mutum indai Abu ya shafi Manzon Allah girmama wace kawai shiya yasa duba da Hadith Manzon Allah shehi Ibrahim yake cemasa shine asalin komai Kuma daga komai azahiri da badini zan turama screen shoot din asin ta what's up duk Wanda yasaba da wannan ka'ida bama tare dashi har Sai yadawo kwanta shiyasa duk Mai Suna irin nasa sai muce masa Mai Babban suna saboda bana son Fadar sunan

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts