DAGA TASKAR IBN TAIMIYYA RAHMATULLAH 005
Da yawa-yawan masu zagi da baƙar ƙiyayya ga Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya Rahimahullah, musamman ta hanyar ƙaga masa ƙin Manzon Allah ﷺ, za ka samu; ko dai kwata-kwata ba su da alaƙa da harkar ilimi, ballanta su iya karanta littattafansa! Ko kuma sun gina zukatansu akan ƙinsa da yi masa ƙage ta kowace hanya!
Dubi yadda bawan Allah yake sanarwa duniya da alƙalaminsa muhimmancin sanya SALATI ga Manzon Allah ﷺ a cikin kowane lungu da saƙo na addu'a, domin neman karɓuwarta a gurin Allah (S.W.T)!
Allah ya jiƙan ƴan mazan!
#TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
Comments
Post a Comment