DAGA TASKAR IBN TAIMIYYA RAHIMAHULLAH 007
Shaikhul Islam Ibn Taimiyya Rahimahullah yana cewa: "Ita SHIRKA ita ce mafi girman ɓarna (a doron ƙasa). Kamar yadda TAUHIDI shi ne mafi girman alheri (a doron ƙasa)!" - Majmū'ul Fatāwā 1/94 DARASI A nan dattijon Sunnah Ibnu Taimiyyah Rahimahullah yana ishara ne zuwa ga abin da zai samarwa da mutanen duniya ALKHAIRI da cigaba cikin rayuwarsu a duniya, kuma ya iske su daga faɗawa cikin masifu da ƙasƙanci. TAUHIDI shi ne kawai mafita ga ɗan ɗan adam ɗin da yake so ya yi rayuwa mai tsafta a duniya, kuma ya dace da aljanna ranar alƙiyama. Kamar yadda SHIRKA ga Allah (S.W.T) a cikin dukkanin haƙƙoƙinsa take gadar da masifa da ɓarna a ban ƙasa! Allah ya kyauta makwancin dattijon Sunnah Shaikhul Islam Ibn Taimiyya. #TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada