DAGA TASKAR IBN TAIMIYYA RAHIMAHULLAH 007


Shaikhul Islam Ibn Taimiyya Rahimahullah yana cewa:

"Ita SHIRKA ita ce mafi girman ɓarna (a doron ƙasa). Kamar yadda TAUHIDI shi ne mafi girman alheri (a doron ƙasa)!"

- Majmū'ul Fatāwā 1/94

DARASI 
A nan dattijon Sunnah Ibnu Taimiyyah Rahimahullah yana ishara ne zuwa ga abin da zai samarwa da mutanen duniya ALKHAIRI da cigaba cikin rayuwarsu a duniya, kuma ya iske su daga faɗawa cikin masifu da ƙasƙanci. TAUHIDI shi ne kawai mafita ga ɗan ɗan adam ɗin da yake so ya yi rayuwa mai tsafta a duniya, kuma ya dace da aljanna ranar alƙiyama.

Kamar yadda SHIRKA ga Allah (S.W.T) a cikin dukkanin haƙƙoƙinsa take gadar da masifa da ɓarna a ban ƙasa!

Allah ya kyauta makwancin dattijon Sunnah Shaikhul Islam Ibn Taimiyya.

#TaskarIbnuTaimiyya #AddiniDaRayuwa #AdamSharada

Comments

Popular Posts