TAFIYAR HASKE "SPEED OF LIGHT" TSAKANIN ALƘUR'ANI DA KIMIYYAR PHYSICS
MATASHIYA
Allah (S.W.T) ya faɗa mana a cikin Alƙur'ani cewa, zai nunawa mutane dalilai (ayoyi) da suke tabbatar da samuwarsa da kaɗaitakarsa a karan-kanmu, a cikin komai da muke iya gani ko tunani:
سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الْآفَاقِ وَفِي أَنفُسِهِمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ الْحَقُّ ۗ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ (فصلت: ٥٣)
A duk lokacin da ɗan adam ya nutsu ya kalli duniya da abin da ke cikinta, ta hanyar tunani kyakkyawa, zai ƙara samun yaƙin game da kaɗaitakar Allah (S.W.T), da cancantarsa da bauta, ba tare da haɗa shi da abokin tarayya ba!
MENENE HASKE A KIMIYYAR PHYSICS?
Ba wata tsayayyar amsa guda 1 da za ta iya gamsar da mu ma'anar abin da malaman Physics ke nufi da HASKE (LIGHT)! Kawai dai suna cewa a yaren Physics:
"light is an electromagnetic radiation that can be detected by the human eye."
Ma'ana: haske wani nau'in ƙarfi (energy) ne da yake tafiya (irin tafiyar ruwa) a sararin da ba ya ɗauke da komai na (matter), wanda yake iya bayyana akan idon mutum.
Wato gwari-gwari, shi haske wani nau'in abu ne na musamman da yake tafiya a cikin sarari, ta yadda har idanun mutum ke iya ganinsa. Idan ka duba haske da kyau, za ka ga shi haske wani abu ne da yake bayyana akan idanunmu, kuma bai ta'allaƙa da wani mazubi ko gurin ƙayyadajje ba, yana mamaye gurare masu yawan gaske. A rubutu na gaba in sha Allah za mu yi bayanin yadda ARNAN malaman Physics suka kasa gano daga ina ne haske ya samo asali. Kishiryar haske shi ne duhu, wato daukewar wancan ƙarfin (energy) da yake iya bayyana akan idanun ɗan adam.
TAFIYAR HASKE (SPEED OF LIGHT)
An kimiyyar Physics kacokan akan turaku guda 3 ne:
1- Space (sarari/guri)
2- Time (lokaci)
3- Energy (ƙarfi)
Duk wani juye-juye a Ilimin Physics ba ya fita daga da'irar waɗannan abubuwan guda 3.
Abin da ake cewa tafiya (SPEED) a Physics shi ne: motsawar jiki a cikin sarari daga wani guri zuwa wani daban. Kamar motsawar jirgin sama daga ƙasa zuwa tudun da yake hawa ya fara tashi sama. Kamar motsawar mota daga cikin gareji zuwa ƙofar gida. Kamar motsawar tafiyar ɗan adam daga gida zuwa masallaci.
Haske (light) yana tafiya shi ma daga wani waje zuwa wani. Wannan tafiyar dole ta ƙunshi gurin da ya yi tafiyar (space) da kuma lokacin da ya ɓata daga farkon inda ya taho zuwa inda ya isa (time). Wannan nau'in tafiyar a Physics ana kiranta 'VELOCITY". Ana kuma wakiltar tafiyar haske da harafin 'c'
MATSAYIN TAFIYAR HASKE (c) KIMIYYAR PHYSICS
Malaman Physics sun gano duk duniya ba wani abu ko wane iri ne da ya kai haske saurin tafiya. A binciken ƙwaƙwaf an gano haske yana gudun tazarar mita 300,000,000 a duk daƙiƙa ɗaya! Daga wannan bincike ne malaman Physics suka susuce suka ce 'BABU WANI ABU DA ZAI IYA KUSANTAR HASKE MA A TAFIYA' ballantana ma ya iya zama daidai da haske a saurin tafiya. Haske yana da matuƙar amfani a kimiyyar Physics, yau abubuwan da muke gani na ci-gaban kimiyya da fasaha galibi sun samu ne daga nanotechnology, wanda shi ne technology da ya shiga likitanci, sadarwa, ƙere-ƙere, kiwo, noma, magunguna, nazarin yanayi, labarin ƙasa da sauransu.
Wannan nazariyya ce ma ta sanya Sir. Albert Einstein ya alaƙanta dangantakar karfi da nauyin ƴan ƙananun abubuwa, da kuma tafiyar haske (c) a cikin shahararriyar nazariyyar nan mai suna Einstein Energy:
E = mc²
TAFIYAR HASKE A CIKIN ALƘUR'ANI
Allah (S.W.T) mahaliccin kowa da komai a cikin Alƙur'anin da ya saukarwa Annabi Muhammad (S.A.W) sama da shekaru 1400, a tsakiyar saharar Larabawa, ya ambaci tafiyar haske:
يُدَبِّرُ الْأَمْرَ مِنَ السَّمَاءِ إِلَى الْأَرْضِ ثُمَّ يَعْرُجُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ أَلْفَ سَنَةٍ مِّمَّا تَعُدُّونَ
(Sajdah: 5)
"Yana jujjuya al'amura daga sama zuwa ƙasa, sannan su tafi (Mala'iku) zuwa wajensa a cikin yini, a (tafiyar) abin da ya kai shekaru dubu da ku ke lissafawa!"
A nan Allah (S.W.T) yana faɗa mana, Mala'iku suna tafiyar shekara dubu (a lisssafinmu na mutane) wajen zirga-zirgar kai saƙo daga ƙasa zuwa sama. A ƙarƙashin wannan ayar za mu fitar da wasu muhimman mas'aloli guda 3 kamar haka:
1- Asali su dama Mala'iku Allah (S.W.T) ya halicce su ne daga haske. Al-Imam Muslim ya fitar da Hadisi a cikin Sahihinsa a lamba ta 2966:
حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ رَافِعٍ ، وَعَبْدُ بْنُ حُمَيْدٍ ، قَالَ عَبْدٌ : أَخْبَرَنَا، وَقَالَ ابْنُ رَافِعٍ : حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّزَّاقِ ، أَخْبَرَنَا مَعْمَرٌ ، عَنِ الزُّهْرِيِّ ، عَنْ عُرْوَةَ ، عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " خُلِقَتِ الْمَلَائِكَةُ مِنْ نُورٍ، وَخُلِقَ الْجَانُّ مِنْ مَارِجٍ مِنْ نَارٍ، وَخُلِقَ آدَمُ مِمَّا وُصِفَ لَكُمْ ".
Annabi (S.A.W) ya ce: "An halicci Mala'iku daga haske....."
Don haka a kimiyyar Physics za mu iya cewa: su Mala'iku ba su kai ɗan adam nauyi ba, saboda asalin halittarsu ba ta da nauyi.
2- A lokacin da aka saukar da Alkur'ani, Larabawa da Allah (S.W.T) ya ke magana da su, suna lissafin tazarar nisa (distance) ne da tazarar kwanakin da za su yi tafiya daga wani gari zuwa wani, ba wai da meter ko kilometer da Physics ke awon tazara da su ba. Don haka dole tazararsu ta fi tsayi sama da tazarar da abin awo (measurement of distance) yake iya aunawa a Physics.
3- Larabawa a lokacin Annabi Muhammad (S.A.W) suna lissafa shekara ne da kalandar Ƙamariyya (Lunar Calendar) ne, saɓanin mu da malaman Physics da muke lissafi da kalandar Shamsiyya (Solar Calendar). Tafiyarsu da Mala'iku ke yi a kwana ɗaya a irin wannan lokacin nasu, ita ce daidai da tafiyar shekaru 1000 a dai irin nasu zamanin da ake lissafi da Ƙamariyya (wato tafiyar wata) da ita.
A Lissafance (Mathematically),
1 day = 1000 lunar years
1 lunar year = 12 months
12 x 1000= 12,000
Kenan, a kullum Mala'iku suna tafiyar shekaru 12,000 ne a lissafin Kalandar Ƙamariyya.
Dama kuma a ilimin Physics da ya shafi sama (Astrophysics) mun sani cewa:
12000 lunar orbits/day = speed of light
Ma'ana: adadin kewayar da wata ke yi guda 12000 a kwana 1, shi ne adadin tafiyar haske guda 1.
Ƙarara ta bayyana a nan, abin da malaman Physics suka gano game da adadin tafiyar da haske yake, tun shekaru sama da 1400 Allah (S.W.T) ya labartawa Annabi Muhammad (S.A.W) shi a cikin Alƙur'ani.
ƊAURAYA
Ya isa mu'ujiza ga Annabi Muhammad (S.A.W) kuma ya isa dalili mai ƙarfi ga duk mai hankali ya gane samuwar Allah (S.W.T), ta yadda ya yi wahayin abubuwan da yau ake ganin kamar wani sabon ci-gaba aka kawowa duniya, a cikin littafin da aka saukar a tsandaurin sahara, a cikin al'ummar da ba sa karatu da rubutu.
© Adam Sharada
11, Muharram 1443
20, August 2021
Comments
Post a Comment