SHIN DA GASKE SAHABI ANAS IBN MALIK [R.A] YA TUHIMI ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] DA YIWA NANA SAFIYYAH BINT HUYAY [R.A] FYADE???
بسم الله الرحمان الرحيم
Daga cikin sharri da qazafin da ABDULJABBAR NASIRU KABARA ke yiwa SAHABBAN MANZON ALLAH [S.A.W], akwai tuhumar da ya yiwa sahabi ANAS IBN MALIK [R.A], game da hadisin da ya rawaito na auren ANNABI [S.A.W] da Nana Safiyyah [R.A]. Malamai da dama sun rawaito hadisin kamar; Bukhari, Muslim, Ibn Katheer, Ibn Abdulbarrin Namiriy, Ibnul Atheer, Ibnul Jauziy, Zahabiy a cikin da wasu cikin malaman Hadisi da na Tarihi, cewa wai SAHABI ANAS IBN MALIK [R.A] YANA TUHUMAR ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] DA YIN FYADE [wal iyazu billahi]!
Ga ruwayar IMAMUL BUKHARIY a cikin صحيح البخاري, wadda ABDULJABBAR yake nanatawa, saboda baqar tsanarsa ga Bukhari da littafinsa: Bukhari ya kawo ta a cikin كتاب النكاح babin da ya sanyawa suna: باب من جعل عتق الأمة صداقها hadisi mai lamba *5086* , ga lafazin:
حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا حَمَّادٌ عَنْ ثَابِتٍ وَشُعَيْبِ بْنِ الْحَبْحَابِ عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَعْتَقَ صَفِيَّةَ، وَجَعَلَ عِتْقَهَا صَدَاقَهَا.
Daga Anas bn Malik: "Hakika Annabi [S.A.W] YA 'YANTA SAFIYYAH. Sai ya sanya 'yanta ta ya zama SADAKINTA"
Kalmar ' 'yanta SAFIYYAH' ita ABDULJABBAR ya lanqwasa ya banqarata, sannan ya fassara ta da cewa; wai Sahabi Anas bn Malik [R.A] yana tuhumar Annabi [S.A.W] da yiwa Nana SAFIYYAH [R.A] fyade!
AMSA:
SADAKI yana cikin manyan sharudda guda 3 da AURE ba ya zama aure cikakke sai da su! Malaman Fiqhu sun san mas'alar 'yanta baiwa mace da sanya wannan 'yantawar ya zama SAADAKINTA! Da damansu sun tafi akan halaccin wannan fuskar aure kamar; Al-Imamus Shaafi'iy, Al-Imamu Ahmad da manyan malaman Fiqhun Masar da suka rayu a karni 2-3! Wasu kuma cikin malamai suna ganin rashin halaccin haka ga wanin Annabi [S.A.W]! Suna cewa: mas'alar 'yanta Nana Safiyyah [R.A] yana cikin abubuwnan da Allah [S.W.T] ya ke6e Annabi Muhammad [S.A.W] da su [الخصوصيات] ne. Don haka 'yanta mace ba ya lazimta aurenta, domin in har an 'yanta ta, to tana da haqqin mallakar kanta da za6in ra'ayinta!
Magana mafi inganci shi ne; dukkanin ayyukan Annabi [S.A.W] suna daukar hukuncin halascin kwaikwayo ne, sai dai inda Allah ko Annabi suka ce wannan ya taqaita ne kawai ga Annabi Muhammad [S.A.W] kamar AUREN MATA SAMA da 4 da makamantansu!
Wannan shi ne FIQHUN da ake fitarwa qarqashin hadisin! Amma saboda baqar qiyayya, qullaci da tsanar da ABDULJABBAR ya yiwa mutanen kirki, ALMAJIRAN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] sai ya fassara hadisin da cewa wai ANAS BN MALIK yana tuhumar ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] da yiwa NANA SAFIYYAH [R.A] FYADE! Don girman Allah mai karatu a ina wani abu mai kama da haka ya fito a lafazin hadisin?
SHIN ANNABI [S.A.W] TURSASA NANA SAFIYYAH [R.A] YA YI YA AURE TA?
Bayan an dawo daga yakin Khaibar [shekara ta 7 B.H], an samo ganimar bayi maza da mata, cikinsu har da UWAR MUMINAI NANA SAFIYYAH bint HUYAY [R.A]. Nana Safiyyah ta zama rabon sahabi mai daraja DIHYAH IBN KHALIFAH ALKALBIY [R.A]. Daga baya wasu cikin SAHABBAI DATTAWA suka ce da Annabi; ya Manzon Allah! Ita [Nana Safiyyah] fa shugaba ce ta kabilar بنو قريظة da بنو النضير, muna ga da kai ta fi dacewa!
Sai Annabi [S.A.W] ya saye ta a hannun Dihyah [R.A]. Sannan Annabi [S.A.W] ya ce da Nana Safiyyah: "Kina da za6i: Idan ki ka za6i MUSULUNCI, to zan za6arwa kaina ke. Idan kuma ki ka za6i YHAUDANCI, to zan 'yanta ki, ki je ki hadu da mutanenki [Yahudawa]"
Sai Nana Safiyyah [R.A] ta ce: "Na za6i ALLAH da MANZONSA? Haqiqa na yi sha'awar MUSULUNCI, kuma na gasgata ka tun gabanin ka kira ni zuwa Musulunci, lokacin da muka taho cikin ayarinka! Ba ni da wani gado a cikin YAHUDANCI, ba ni da DA ko DAN'UWA a cikin sa [Yahudanci]! Ka ba ni za6i tsakanin KAFIRCI da MUSULUNCI, lallai ALLAH da MANZON su na fi qauna, sama da 'yanci da komawa cikin al'ummata"
Nana Safiyyah [R.A] ta musulunta kuma ta kyautata musuluncinta! Annabi [S.A.W] ya 'yanta ta sannan ya aure ta, ya sanya 'yanta ta da ya yi ta zama SADAKINTA!
Wannan shi ne abin da malaman tarihi suka rawaito a qarqashin kissar auren ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] da UWAR MUMINAI, NANA SAFIYYAH BINT HUYAY daya daga cikin zuriyar LAAWIY dan Annabi YA'AQUB [A.S] ibn Ishaq [A.S] ibn Ibrahim [A.S], kuma daya daga cikin jikokin Annabi Hárún [A.S] kanin Annabi Musa [A.S]. Amma haka kawai Abduljabbar ya qirqiro abin da babu shi ya cusa don cimma wata manufa mummuna; ita ce samun damar cin mutuncin SAHABBAN MANZON ALLAH [S.A.W]! Tsakaninmu da Allah a nan gurin, da SAHABI ANAS IBN MALIK [R.A] hadimin Manzon Allah da Annabi ya bar duniya yana mai yarda da shi, da kuma DAN-ISKAN GARI ABDULJABBAR NASIRU KABARA waye ya yiwa ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] mafi Tsarki da Daraja a dukkanin halittun Allah qazafi da jafaa'in FYADE? Kamar haka ne ya fake da hadisin shiga bandaki ya ce; Sahabi ANAS IBN MALIK ya tuhumi Annabi [S.A.W] da LUWADI! Wannan shi ne tantagaryar maqiyin Manzon Allah mai jinginawa Annabi [S.A.W] abin da Abu Jahal da Waleed Ibnul Mugheerah da sauran MUSHIRIKAN MAKKAH ma ba su ta6a karmabanin yi masa karya da su ba [S.A.W]! Wannan kuma shi ne jigon rigimarmu ta ilimi da wannan mutumin banzar ABDULJABBAR NASIRU KABARA!
DAURAYA:
A yunqurin Abduljabbar na rigima da AHLUSSUNNAH SALAFIYYAH, tun yana kare KARAMOMIN WALIYAI na bogi, ya koma batutuwan TAUHIDI, yanzu ya dawo kan ALQUR'ANI DA SUNNAH yana rugurguje su da son zuciya, saboda qiyayyar da yake yiwa AHLUSSUNNAH! Duk wanda ya karanta littattafansa na farko-farko kamar سيف الجبار, إحياء العقيدة da عصى موسى zai gamsu lallai ABDULJABBAR yana girmama SAHABBAN MANZON ALLAH [S.A.W]. Amma tun daga مقدمة أزقة zuwa الأبابيل ya warware hatta رضي الله عنه da yake girmama SAHABBAN da ita! SAHABBAN da a baya yake yabo yanzu tsine musu albarka yake!
Ya daina dogara da ka'idojin ilimin Hadisi علم الحديث الدراية والرواية, saboda ya ga buqatarsa ba za ta biya ba! Yanzu yana ruguje INGANTATTUN HADISAI ne da ra'ayi da abin da zuciyarsa ta tsara masa! Babu ruwansa da kowane malami ne ko sahabi ko tabi'i, tunaninsa da ma'auninsa shi ne ILIMI! Da Wannan ya zama halakakke mai halakar da al'umma. Muna fatan Allah ya tsare musulmi daga sharrinsa, shi kuma Allah ya shirye shi!
Wadanda ba sa karatun addini, yana da kyau su koma makaranta! Sannan su riqa tuntu6ar daliban ilimi da malamai kan duk wata magana da ABDULJABBAR ya yi! Daliban ilimi da malamai kuma a ci gaba da aikin
تبيين كذب المفتري المتعالم الكبري
Allah ya tsare mana Musuluncinmu da imaninmu. Allah ya qara yarda da SAHABBAN ANNABINMU.
MANAZARTA
-صحيح البخاري
Na Abu Abdullah Albukhari [Hadisi na 5086]
- صحيح فقه السنة وأدلته وتوضيح مذاهب لأئمة
Na Abu Malik ibn Abdussalam [Juz'i na 3, shafi 161-162]
-السيرة النبوية
Na Ibn Hisham [Juz'i na 4, shafi 166]
الفصول في سيرة الرسول
Na Ibn Katheer Addimashqiy [shafi na 117]
مختصر سيرة الرسول وأصحابه العشرة
Na Abdulganiy Aalmaqdisiy [shafi na62]
- نبي الرحمة
Na Dr. Muhammad Sani Umar Musa [shafi na 260, 341]
-أسد الغابة
Na Ibnu Atheer Namiriy [tarjama ta 7063]
- الاستيعاب في معرفة الأصحاب
Na Ibnu Abdulbarrin Namiriy [Juz'i na 4, shafi 1854-1855, tarjama ta 4005]
Rubutawa:
Adam Sharada
Physics department, Bayero University Kano
physicsp33@gmail.com

Allah ya saka da alkhairi
ReplyDeleteSunana sunusi mansur yusuf almajirinka

ReplyDelete