USTAZAI NA BUƘATAR SANIN KIMIYYAR DA’AWA!



Take: Tsokaci Akan Wasiƙar As-Shaikh Abdul Azīz Bn Bāz Rahimahullah ga Hasanayn Makhlūf Rahimahullah 

Wannan wata wasiƙa ce Fadhilatus Shaikh Bn Bāz Rahimahullah (مفتي الجزيرة) ga Shaikh Hasanayn Muḥammad Makhlūf, ɗaya daga cikin fitattun manyan malaman Azhar game da fatawarsa akan 'rashin halascin yin sallar nafila (تحية المسجد) a lokacin da liman yake tsaka da huɗubar Juma'a'. Salon da Shaikh Bn Bāz Rahimahullah ya yi amfani da shi, yana da matuƙar ban ƙaye da burgewa ga waɗanda suka san kimiyya da fasahar da'awa!

Abin da ya fara zuwa raina bayan na gama karantawa; da a ce irinmu ne ƴan karambani suka ci karo da wannan gaɓar, da yanzu ka ji yadda ake auno nassoshi ake lugudensu akan malamin 😥

Mu ɗan duba wasu gaɓoɓi guda 5 a cikin wannan gajeriyar wasiƙar:

1- Gaɓa ta 1
Abin da Shaikh Bn Bāz Rahimahullah ya buɗe da shi:
من عبدالعزيز بن عبدالله بن باز إلى حضرة الأخ المكرم فضيلة الشيخ حسنين مخلوف وفقه الله لكل خير آمين، سلام عليكم ورحمة الله وبركاته.

Daga Abdul-Azīz bin Abdullahi bin Bāz, zuwa ga ɗan uwa maigirma As-Shaikh Hasanayn Makhlūf, Allah ya datar da shi ga dukkan alkhairi.

2- Gaɓa ta 2

 يا محب 
Ya wanda nake ƙauna!

3- Gaɓa ta 3

 لكونه لا يخفى مثلكم ما صح عن النبي ﷺ من أمره للذي دخل وهو يخطب يوم الجمعة أن يصلي ركعتين؛ فلعل فضيلتكم قد نسيتم ذلك
Domin ba zai ɓuya ga (malamai) irinku ba; abin da ya tabbata daga Annabi ﷺ na umarninsa ga wanda ya shiga masallaci liman yana huɗubar Juma'a, zai yi sallar nafila raka'a 2 (تحية المسجد). Wataƙila su malam sun manta da wannan umarnin!

4- Gaɓa ta 4

ولذا رأيت أن أذكركم بهذا الأمر من باب التعاون على البر والتقوي، ويحسن من فضيلتكم تصحيح الجواب على هذه المسألة، والإعلان عن ذلك كما أعلنتم الأول.
Saboda haka ne na ga dacewar tunatar da ku wannan al'amarin a babin taimakekeniya wajen yiwa Allah (S.W.T) ɗa'a da kiyaye dokokin shari'a. Lallai yana da kyau su Malam su dake yin bayani game da wannan mas'alar, da yaɗa saƙon kamar yadda aka yaɗa na farko ga al'umma.

5- Gaɓa ta 5
Kalmomin da Shaikh Bn Bāz Rahimahullah ya rufe da su

 شكر الله سعيكم، وبارك في جهودكم، ونفع بعلومكم، وجعلنا وإياكم وسائر إخواننا من دعاة الهدى، ووفقنا جميعا لإصابة الحق في القول والعمل؛ إنه خير مسؤول.
 والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته.
 
Da yawan masu da'awar ilimi da karatu, sun rasa irin wannan kyakkyawan usulibin na malamai na Allah, shi ya sa suke ƙara rikita al'umma da tunzura su zuwa ga halaka da ɓata. Da yawanmu (in banda ƴan ƙalilan) kamar jira muke wani mai harkar ilimi ya yi kuskure, mu dirar masa da ruwan ayoyi da hadisai. Yanzu za ka ga an zubo ayoyi 80 hadisai 65, ana jahiltar da shi. Mal. Musa Muhammad Dankwano ya taɓa faɗa min wata magana da ta zauna min a raina, ya ce "ba daidai ba ne a riƙa faɗin kuskuren malami a gaban gama-garin mutane!"

Akwai wata magana da yayana Mal. Isma'il Ibrahim Abdulkadir ya faɗa min watarana na kai masa ziyara, game da irin salo da dabarun da ake amfani da su wajen raba matasa da ɗabi'ar shaye-shaye a cikin al'umma. Tun daga lokacin na koyi janyo masu laifi a jika da nuna musu ƙauna da biya musu bukatunsu.

Ƴan uwana ɗalibai mu gyara usulibin wa'azi! Mu guji ƙyama da tsangwama da kyarar masu laifi. Mu guji zumuɗin jiran kuskuren wani don mu yi masa raddi, don a ce mun iya. Mu riƙa yawan tuna faɗin Allah (S.W.T)

ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ ۖ وَجَٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
(Suratun Nahli: 125)

Da faɗin Manzon Allah ﷺ:

"يسروا ولا تعسروا ، وبشروا ولا تنفروا"
(Bukhari: 69, Muslim: 1734)

#AddiniDaRayuwa #AdamSharada

(C) Adam Sharada 
 January 7, 2024

Comments