'LITTAFIN KARATU'
Ina yawan bibiyar darasin النحو التطبيقي da shi mawallafin littafin As-Shaikh Khālid Abdul-Azīz yake gabatarwa a shafinsa. Darasin yana da natuƙar ban ƙaye da ratsa zukata, ɗalibai daga ko ina suna bibiya. Kwatsam makon da ya wuce sai na ga sanarwa a shafin cewa an aika littafin ƙasashen duniya, masu buƙata su faɗi ƙasarsu, a faɗa musu inda za su nema.
Ga shi nan ya zo NAJERIYA akan farashin ₦16,000 lakadan ba ajalan ba! Mujalladi (volume) ɗaya ba uku ko huɗu ba. Wannan fa kafin ya shiga hannun ƴan kasuwa ma ke nan.
Ɗaliban ilimi masu son sayen littafi suna cikin halin ƙunci! Littafi yanzu sai ka yi da gaske. Ga karatu ga ilimi, ga ɗaliban ilimi a gefe, amma abun ba a magana! Masu hali, don Allah ku riƙa sayawa abokanku da makusantanku ɗaliban ilimi littafi!
Allah ya kyauta!
#LittattafanMusulunci #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
(C) Adam Sharada
January 9, 2024
3:05pm Kano, Nigeria
Comments
Post a Comment