NAZARIYYAR TELEPORTATION A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI


GABATARWA
Daga cikin tambayoyin da aka yi min a ƙarƙashin rubutuna game da nazariyyar Teleportation, shin akwai alaƙa tsakanin teleportation da wasu abubuwa da suka faru na addini kamar Isra'i da Mi'irajin Annabi ﷺ?

In sha Allah za mu tattauna a taƙaice game da waɗannan gaɓoɓin guda 2.

ISRA'IN ANNABI MUHAMMAD ﷺ 

Isra'i shi ne tafiyar dare mai nisa wadda mala'ika Jibril (A.S) ya yi tare da Annabi Muhammad ﷺ akan wani abun hawa mai suna 'Burāq' daga masallaci mai alfarma na Makkah, zuwa masallaci mai alfarma na Ƙudus. 

Allah (S.W.T) Ya labarta mana wannan tafiya a farkon Suratul Isra'i

سُبْحَانَ الَّذِي أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِ لَيْلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَى الْمَسْجِدِ الْأَقْصَى الَّذِي بَارَكْنَا حَوْلَهُ لِنُرِيَهُ مِنْ آيَاتِنَا ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
(Suratul Isra'i: 1)

Wannan tafiya ta faru ne a daren ranar 27 ga watan Rajab, a shekara ta 12 da aiko Annabi Muhammad ﷺ a Makkah. Wato gabanin hijira zuwa Madinah da shekara 1!

A lissafin Google Map, adadin nisan tafiya a mota daga masallaci mai alfarma na Makkah (Ka'aba) zuwa masallacin Qudus (Masjidul Aqsa) ya kai tazarar 1466 km. A ma'aunin lokaci a lissafin agogo (time) kuma ya kai awanni guda 17. A zubi da ɗabi'ar da Allah (S.W.T) Ya halicci ɗan adam ba zai iya tafiya mai irin wannan saurin ba. Amma da yake shi mala'ika an halicce shi daga ne daga HASKE (Muslim, 2996) don haka jikinsa zai iya gudun 3x10⁸ m/s; wato yana gudun mita miliyan 300 a cikin daƙiƙa (sakan) 1!

Saurin tafiyar da wannan abin hawa ya yi da Annabi Muhammad ﷺ tare da mala'ika Jibril (A.S) a cikin tazarar lokaci (velocity), ya ninnika lokacin da mai tafiya akan abin hawa akan titi (mota) ko a jirgin sama zai iya shafewa daga Ka'aba zuwa Qudus. Wannan ya faru ne saboda abin hawa da aka yi amfani da shi, yana tafiya irin ta haske (velocity of light, c), inda yake cinye zango mai nisa a daƙiƙu ƴan kaɗan! Amma saboda ƙudira da buwaya ta Allah (S.W.T) Ya sa aka yi wannnan tafiya da babban masoyinSa Annabi Muhammad ﷺ #ZaɓaɓɓenZaɓaɓɓu a cikin ƴan daƙiƙu!

DARASI

- Iya tafiyar dare (ISRA'I) da Annabi ﷺ ya yi, tana tabbatar da samuwar Allah (S.W.T) da ikonSa wajen sarrafa gudanar al'amurra a akasin yadda ɗan adam ya san su. Kuma dai tana tabbatar da cancantar kaɗaita Allah (S.W.T) da bauta a dunƙule da rarrabe.

- Za mu iya kiran wannan tafiya da 'Teleportation' Domin ta ƙunshi aika saƙon wani jiki daga wani guri zuwa wani gurin na dabba mai nisa cikin ƙanƙanin lokaci, ta hanyar (medium) kimiyya!

Annabi Muhammad ﷺ shi ne jiki mai daraja da aka ɗauka aka tura Masjidul Aqsa. Hanyar da aka yi amfani da ita (medium for the propagation) shi ne 'burāƙ' da suka hau tare da mala'ika Jibril (A.S). Guraren guda 2 kuma (x1, x2) su ne Ka'aba da Masallacin Qudus.

Amma mu sauran mutane ba mu da wani iko ko dabara ko ƙwarewar fasahar ƙirƙira ko ma zurfi a kimiyyar Physics da zai sa jikinmu ya ɗauki 'teleportation'. Wannan shi ne tsaftataccen ilimin Physics da zai dace da lafiyayyen hankali.

Za mu ci gaba in sha Allah!

#kimiyyadaaddini #AddiniDaRayuwa #physics 

(C) Adam Sharada
 31st December, 2023

Comments