NAZARIYYAR TELEPORTATION A KIMIYYAR PHYSICS


0.1| GABATARWA
Bari mu tambayi kanmu wata haƙiƙa da muka sani a yau da kullum, don mu gane haƙiƙanin saƙon da kimiyyar "Teleportation" ke ɗauke da shi: Kun yi cinikin hula da Mal. Anas Darazo kai kana unguwar Kmashi a Kaduna, shi kuma (Mal. Anas) yana Darazo ta Bauchi mai kamar Kano daga nesa. Madadin Anas Darazo ya je tasha ya bawa direba (way bill) zuwa tashar Kawo Kaduna, sai ya buɗe laptop ɗinsa ya jona mata scanner, ya ɗora hular akan inji, kawai sai ta bi iska ta tafi. Kai kuma a Kaduna da ka shiga ɗaki ka buɗe laptop ɗinka, sai ka yi downloading hularka tangaran/kindei ka fito da ita fili (physically) ka yi mata kari biyu ɗora ta akan goshinka!

Kana ganin akwai wata fasahar cigaba da za a kai a duniya, wadda za ta iya wannan aikin? Za mu shiga mu ji me masana suka ce, sai mu aza dalilan nasu akan ma'aunan kimiyyar Physics don ganin yiwuwa ko rashin yiwuwar hakan, in sha Allah.

0.2| MENENE TELEPORTATION?
Malamar Physics Anne van Weerden (2010) ta ce:

"the transportation of the unknown state |ψ〉 of a spin 1/2 particle, onto another one"
(Teleportation, p10)
Ma'ana: Shi ne aika wani jiki ya yi tafiya daga wani gurin zuwa wani daban.

Malaman Physics sun ɗauki tsawon lokaci suna bajekolin ilimi ta hanyar bincike mai zurfi game da yiwuwar faruwar 'Teleportation' matter, da hanyoyin da za a iya bi wajen aika jikin (rigid body/matter) daga wani gurin zuwa wani daban, ba tare da an yi tafiyar takanas ba!

03| DALILAN ƁACIN NAZARIYYAR TELEPORTATION A KIMIYYAR PHYSICS
Za mu yi amfani da ƙa'idojin da suka kafa kimiyyar Physics mu kalli wannan nazariyyar:

1- MATTER : A kimiyyar Physics 'matter' shi ne duk wani jiki da yake da adadi, ake iya gane nauyinsa a ma'anunin kimiyya (scale) kuma yake da alaƙa da makamashin ƙarfi (force) wajen sarrafa shi.

Akwai wata ƙa'ida sananniya game da matter da ake kira 'Conservation of Matter' kamar haka:

"Matter can neither be created nor destroyed."
Ba za a iya ƙirƙirar matter ko a sauya mata zubinta na asali ba!

Gini akan wannan ƙa'idar, kenan ba zai yiwu a sauyawa hula zubinta na asali (disintegration) ba, idan za a tura ta daga Darazo ta Bauchi mai kamar Kano daga nesa, zuwa Kadunar su Shehu Liman! Ballantana kuma a yi maganar disintegrating jikin ɗan adam a tura shi daga wani garin zuwa wani, wanda hankali ma ba zai karɓa ba sam!

2- LIGHT: Idan ta tabbata za a iya Teleportation na matter daga wani gurin zuwa wani daban, to ba makawa sai an yi maganar Quantum Mechanics, sai an yi amfani da nazariyyar haske, wadda ita ce kusan kashi 95% na hanyar da za a iya wannan aiki. Shi kuma haske a kimiyyar Physics yana da wata ɗabi'a ta musamman da ta musamman da ta bambanta shi da sauran nau'ikan matter. Malaman Physics sun yi ijma'i akan:

• "Nothing can approach speed of light!"
Ba abin da ya kai haske saurin tafiya!

Kenan, duk wani jiki da bai dace da zubin haske ba, ba zai iya yin ko da ɗaya bisa adadin saurin tafiyar haske a cikin daƙiƙa (1/1.0x10⁸ m/s) ba. Jikin ɗan adam (Classical Mechanics) ba zai taɓa iya cika wannan ƙa'idar ba a kimiyyance.

• "Light has no mass"
Haske ba shi da ma'aunin adadi!

Duk wani jiki (matter) da malamam Physics da suke ganin yiwuwar Teleportation ke nazari akansu, idan ka kalle su a nutse za ka samu suna da mass (ma'auni na adadinsu) a sikelin kimiyya. Jikin ɗan adam ko ƙone shi aka yi ya zama toka, sai an same shi da mass! Sarrafa shi da za a yi ya zama mara mass kamar haske abu ne da hankali ma ba zai taɓa karɓa ba, kamar yadda Law of Conservation of Matter ta tabbatar!

3- Wave: A Physics wave shi ne "disturbance that travels/propagates from the place where it was created"
Shi ne tafiyar ruwa (kaɗawar ruwa) da wani abu yake yi akan titi (na kimiyya wanda ba a gani) daga inda ya taso zuwa inda ya nufa.

Misalan wave mafiya bayyana su ne kamar tafiyar sauti (sound wave) da tafiyar haske (light wave). Waɗannan suna tafiya akan titin kimiyya wanda idanun ɗan adam ba sa gani.

Duk wani jiki da za a iya yin amfani da Teleportation wajen aika shi wani guri, dole jikin ya dace da wave wajen tafiya akan titin kimiyya (medium). Canjawa jikin abubuwa kamar mutum (Classical) kama zuwa wata sura da za ta iya yin tafiyar ruwa kamar dai sound da light wani abu ne da ba zai yiwu ba, sai dai a cikin fina-finan tatsuniyoyin kimiyya (Science Fiction).

4| ƊAURAYA
Idan muka kalli ƙa'idojin Physics da muka za teleportation akansu za mu fahimci cewa; yiwuwar samuwar fasahar teleportation wani abu ne mai matuƙar wahalar gaske a nan gidan duniya. Shi ya sa Malam Michio Kaku ya kawo mas'alar a cikin littafinsa da ya yi naƙadin abubuwan da ba za su yiwu ba a kimiyyar Physics mai suna 'Physics of the Impossible: A Scientific Exploration into the World of Phasers, Force Fields, Teleportation, and Time Travel'

#kimiyyadaaddini #physics #AddiniDaRayuwa #AdamSharada 

(C) Adam Sharada 
 December 19, 2023

Comments