AIKII DA HANKALI A KIMIYYAR PHYSICS
Isaac Newton (1642-1727) daga cikin tsohuwar al'ummar Girkawa, ya fara kafa turakun nazarin kimiyyar Physics ne ta hanyar tunani da amfani da hankali wajen kallon tsanaki da zurfafawa wajen tunani game da hikimar da ke tattare da wannan duniya, da dalilan da suke sanyawa a samu sauyin na motsi daga wani bigire zuwa wani daban (motion)
Newton ya kalli abubuwan da ke cikin duniya (matter) sai ya fahimci abubuwa guda 2 game da alaƙarsu da motsi (motion):
1- Abubuwan da suke a tsaye a gurin guda (at rest).
2- Abubuwan da ke tsaka da yin motsi (in motion).
Daga nan sai fahimci dukkaninsu suna da alaƙa da tasirin makamashin ƙarfi (force) wajen sarrafa su da gudanar da su. Daga nan ne ya samar da Law of Inertia da muka fi sani da 'Newton's First Law of Motion '.
Irin wannan tunanin yana da sauƙin fahimta ga masu lafiyayyen hankali, za su gamsu da nazariyyar ko da kuwa tunanin hakan bai taɓa zuwa a ƙwaƙwalensu ba. Irin wannan nazariyyar ko a addinin Musulunci ba laifi musulmi ya ci gajiyarta, saboda ba ta ɗamfaru da wani hukunci ko fa'ida da take kishiyantar abin da ya zo a cikin Alƙur'ani maigirma da Sunnar Manzon Allah ﷺ ba.
Amma idan aka yi rashin dace ma'aunin hankali wajen ijtihadi a tsakanin malaman Physics ya ci karo da abin da ya zo a a cikin Alkur'ani, ko wanda ya tabbata a cikin Sunnar Manzon Allah ﷺ, to ba makawa wannan tunanin na malaman Physics shi ne ya KUSKURE hanya, saboda dalilai guda 2:
1- Babu wani tunani a ma'aunin ɗan adam a cikin usul na addinin musulunci: Alkur'ani da Sunnah bisa fahimtar magabata nagari, da za a gabatar da shi, a yi watsi da Alkitab Wassunnah saboda girmama ma'abocinsu. Idan musulmi ya yi gangancin gabatar da karkataccen tunanin wani masanin kimiyya wanda kuma tunanin yana kishiyantar abin da ya zo a cikin Alƙur'ani da Sunnah, to kamar ya fifita su ne akan Allah da ManzonSa wanda shi kuma yana iya kai musulmi zuwa ga fita daga musulunci.
2- Hanyoyin nazariyyar kimiyyar Physics tunani na ɗan adam mai kaifin ƙwaƙwalwa, wannan tunanin zai iya dacewa ya zama daidai kuma zai iya zama kuskure a ma'aunin addinin musulunci. Addinin musulunci dole shi ne kotu da zai riƙa yin hukunci ga fikirorin kimiyya, saboda shi ba fikirar wani mahaluƙi ba ce tsarin gudanar da rayuwa ne daga Mahaliccin halittu Allah (S.W.T)!
#KimiyyaDaAddini #physics #AddiniDaRayuwa #AdamSharada
(C) Adam Sharada
December 18, 2023
Comments
Post a Comment