ABOKIN TAFIYAR ƊALIBAN ILIMI MASU TASOWA

Mai karatu da kai/ke nake; daga fara neman ilimin addininku zuwa yau wace nasara ku ka samu? A cikin ilimummukan kayan aiki (علوم الآلة) da ke mayar da mutum ɗalibin ilimi wanne ne ka/ki ke da ido a cikinsa? Wanne fanni ne cikinsu idan aka yi kuskure ko daga bacci ka tashi za ka iya ganewa? Da za a ce ku bawa kanku maki game da matakinku na neman ilimi daga 1 zuwa 100, nawa za ka bawa kanka? Ke ma nawa za ki bawa kanki?

Littafin طلب العلم بين الوهم والحقيقة na malaminmu As-Shaikh Abdurrahman Umar Bagarawa Hafizahullah shi ne maganin mafi yawan cututtukan da ke damunmu a ɗalibta. Littafi ne da zai taimakawa ɗalibi wanda ya shiryawa neman ilimi da gaske, wajen gina masa tushe (أصول) na ilimi, waɗanda su ne suke mayar da mai neman ilimi ya zama ɗalibi na gaske. Ko da a ce ɗalibi ya taɓa karanta تعليم المتعلم na Zarnūjiy da كتاب العلم na Ibn Uthaimeen, ba zai taɓa wadatuwa daga wannan littafin ba, saboda dalilai guda 4 da na fahimta kamar haka:

1- Malam ya tattauna matsalolin ɗalibta na zamani, waɗanda malaman da suka gabace shi ba su tattauna akansu ba. Kamar tsarin majalisan neman ilimi na zamani, makarantun Islamiyya irin wanda muke da su a nan Najeriya, da kuma shafukan sada zumunta da yanar gizo.

2- Dabarun HADDACE ƙa'idojin ilimi (متون العلم), waɗanda su ne kayan aikin da ke riƙe ɗalibai kuma su tabbatar da shi a matsayin ɗalibin ilimi wanda ya san makamar aiki a harkar ɗalibta.

3- Uwa-uba manhajin neman ilimi, wanda shi ne kaso na biyu na littafin wanda Malam ya yiwa take da المنهج المقترح المتكامل. A ciki ne malam ya tattauna marhaloli guda 10 na ilimi, tare da kawo littattafan da ya kamata ɗalibin ilimi ya koya a kowane fanni a gaban malamai, littattafai masu zurfi da ya kamata ɗalibin ilimi ya ajiye a kusa da shi yana leƙawa a kowane fanni, da kuma littattafan da idan ɗalibin ILIMI yana son ya samu ƙwarewa a wani fanni cikin fannonin ilimi, zai karanta su ya samu ƙwarewa a wani fanni cikin fannonin ilimi.

4- Littafi ne da kullum ɗalibin ilimi yana buƙatar ya zama yana kusa da shi, yana leƙawa domin auna jininsa na ilimi, ta yadda zai fita daga duniyar WAHAMI zuwa dausayin TABBAS cikin wahalhalun neman ilimi. Don haka ba na zaton za mu wadatu daga wannan littafi da abin da ya ƙunsa.

NB: Ana iya samun PDF copy a shafin Malam na Telegram. Kuma ana samun hard copy. Na sanya duka bayanan a comment section.

#AddiniDaRayuwa #LittattafanMusulunci #AdamSharada 

 December 9, 2023

Comments