HADISIN GHADĪR KHUM DA SHUGABANCIN SAYYIDINA ALIYYU (R.A) A BAYAN ANNABI MUHAMMAD ﷺ(Fitowa ta Biyu)



02| HADISIN GHADĪR 
Hadisin Ghadīr ya zo ta hanyoyi da dama, wasu sun inganta, wasu kuma suna da rauni, yayin da wasu masu tarin yawa kuma ba su inganta ba kwata-kwata. 

In sha Allah zan taƙaitu da ruwayoyi guda 2, a cikin Sunanut Tirmiziy da Sunan Ibn Mājah. Saboda su كتب السنن kamar yadda As-Shaikh Abdul-Mājid Algauriy yake cewa:

ولا يذكر في الكتب السنن شيء من الموقوفات والمراسيل، فإنها لا تسمى (سنة) عند المحدثين، وإن ذكر شيء منها ، فهو للاسشتهاد به لا غير. 

Ba a kawo wani abu (hadisi) Mauƙufi ko Misali, saboda Malaman Hadisi ba sa kiran wannan da sunan 'Sunnah'. Idan kuwa (marubuta Sunan) suka kawo, sun yi ne don kafa hujja ba wani abu daban ba.

Ya ci gaba da cewa:

لكنها لا تذكر شيء إلا الحديث المبوي بسنده، لذالك كانت مرتبتها بصورة إجمالية أعلى من "المسانيد" و "المصنفات".

Sai dai su (ma'abota Sunan) ba su kawo wani abu sai hadisin Annabi da isnadinsa. Saboda haka ne darajar littattafan a dunƙule ta ɗararwa ta "Masānīd" da "Musannafāt".

(الوجيز في تعريف كتب الحديث، ص٢١)

NB: Wataƙila wani ya ji kamar ana zaurance ko ya rasa gane ina aka dosa. Wannan ya shafi musamman wanda yake da ido a harkar Hadisi ne, komai ƙanƙantarsa.

1• Al-Imamut Tirmiziy ya fitar da hadisin a ƙarƙashin 
كتاب المناقب عن رسول الله صلى الله عليه وسلم

Hadisi mai lamba 3713 kamar haka:

حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ، قَالَ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ جَعْفَرٍ، قَالَ حَدَّثَنَا شُعْبَةُ، عَنْ سَلَمَةَ بْنِ كُهَيْلٍ، قَالَ سَمِعْتُ أَبَا الطُّفَيْلِ، يُحَدِّثُ عَنْ أَبِي سَرِيْحَةَ، أَوْ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ شَكَّ شُعْبَةُ - عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ ‏ "‏ مَنْ كُنْتُ مَوْلاَهُ فَعَلِيٌّ مَوْلاَهُ ‏"‏ ‏.‏

 قَالَ أَبُو عِيسَى هَذَا حَدِيثٌ حَسَنٌ غَرِيبٌ ‏.‏ وَقَدْ رَوَى شُعْبَةُ هَذَا الْحَدِيثَ عَنْ مَيْمُونٍ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَنْ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم ‏.‏ وَأَبُو سَرِيحَةَ هُوَ حُذَيْفَةُ بْنُ أَسِيدٍ صَاحِبُ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم ‏.‏

2• Shi kuma Ibn Mājah ya fitar da hadisin a كتاب المقدمة a ƙarƙashin

باب: في فضائل أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم - فضل علي بن أبي طالب رضي الله عنه

Hadisi na 116

  حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ مُحَمَّدٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا أَبُو الْحُسَيْنِ ، قَالَ : أَخْبَرَنِي حَمَّادُ بْنُ سَلَمَةَ ، عَنْ عَلِيِّ بْنِ زَيْدِ بْنِ جُدْعَانَ ، عَنْ عَدِيِّ بْنِ ثَابِتٍ ، عَنِ الْبَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ قَالَ : أَقْبَلْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجَّتِهِ الَّتِي حَجَّ فَنَزَلَ فِي بَعْضِ الطَّرِيقِ فَأَمَرَ الصَّلَاةَ جَامِعَةً، فَأَخَذَ بِيَدِ عَلِيٍّ، فَقَالَ : " أَلَسْتُ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ ؟ ". قَالُوا : بَلَى. قَالَ : " أَلَسْتُ أَوْلَى بِكُلِّ مُؤْمِنٍ مِنْ نَفْسِهِ ؟ ". قَالُوا: بَلَى. قَالَ : " فَهَذَا وَلِيُّ مَنْ أَنَا مَوْلَاهُ، اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالَاهُ، اللَّهُمَّ عَادِ مَنْ عَادَاهُ ".  

FASSARAR HADISAN GUDA 2

• A riwayar farko Manzon Allah ﷺ yana cewa: "Duk na kasance MAULANSA, to ALIYYU ma MAULANSA ne!"

• A riwaya ta biyu kuma bayan an yi kiran sallah jama'a sun tattaru, sai Annabi ﷺ ya kama hannun sayyidina Aliyyu (R.A) ya ce: "Ba ni na fiyewa dukkan muminai soyuwa sama da kawunansu ba?" Sai Sahabbai suka ce, haka ne ya Manzon Allah ﷺ. Sai Annabi ﷺ ya ce: "Wannan (Aliyyu) shi ne WALIYYIN duk wanda ni ne MAULANSA! Ya Allah ka yi WALA'I ga wanda ya yi masa (Aliyyu) WALA'I! Ya Allah ka ƙi wanda yake ƙinsa!".

NB: Na yi ƙoƙarin ƙin fassara kalmar ولاية ɗin cikin hadisan ne saboda ita ce kusan gaɓar saɓaninmu da ƴan Shi'a. Kuma in sha Allah za mu tattauna akanta a kashi na uku.

MAGANGANUN MALAMAI GAME DA MA'ANAR HADISIN
In sha Allah za mu koma littattafai bisa amana ta ILIMI mu ji ya malaman hadisi suka fassara hadisin. Zan taƙaita sosai gudun tsawaitawa.

Ga maganganun malamai guda 3 game da hadisin:

I- Al-Imam Abiy Bakr, Ahmad ibnul Husain Alkhurāsāniy Al-Baihaƙiy (458 BH) Rahimahullah a cikin كتاب الاعتقاد , bayan ya kawo Zaid ibn ALIYYU ibnul Husain ibn Aliyyu, da yake cewa:

أَمَّا أَنَا فَلَوْ كُنْتُ مكَانَ أَبِي بَكْرٍ لِحَكَمْتُ بِمِثْلِ مَا حَكَمَ بِهِ أَبُو بَكْرٍ فِي فَدَكَ
Da ni ne a kujerar Sayyidina Abubakar (R.A), da zan yanke irin hukuncin da Sayyidina Abubakar (R.A) ya yanke game da gonar Fadak!

Sai Al-Baihaƙiy ya ce:

وَأَمَّا حَدِيثُ الْمُوَالِاةِ فَلَيْسَ فِيهِ - إِنْ صَحَّ إِسنَادُهُ - نَصٌّ عَلَى وَلَايَةِ عَلِيٍّ بَعْدَهُ، فَقَدْ ذَكَرْنَا مِنْ طُرُقِهِ فِي كِتَابِ الْفَضَائِلِ مَا دَلَّ عَلَى مَقْصودِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ ذَلِكَ وَهُوَ أَنَّهُ لَمَّا بَعَثَهُ إِلَى الْيمَنِ كَثُرَتِ الشَّكَاةُ عَنْهُ وَأَظْهَرُوا بُغْضَهُ فَأَرَادَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ يَذْكُرَ اخْتِصَاصَهُ بِهِ وَمَحبَّتَهُ إِيَّاهُ وَيَحُثُّهُمْ بِذَلِكَ عَلَى مَحَبَّتِهِ وَمُوَالِاتِهِ وَتَرْكِ مُعَادَاتِهِ فَقَالَ: «مِنْ كُنْتُ وَلِيَّهُ فَعَلِيٌّ وَلِيَّهُ» وَفِي بَعْضِ الرُّوَايَاتِ: مِنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ اللَّهُمْ وَالِ مِنْ وَالِاهُ وَعَادِ مِنْ عَادَاهُ. وَالْمُرَادُ بِهِ وَلَاءُ الْإِسْلَامِ وَمَودَّتُهُ، وَعَلَى الْمُسْلِمِينَ أَنْ يوَالِيَ بَعْضُهُمْ بَعْضًا وَلَا يُعَادِي بَعْضُهُمْ بَعْضًا وَهُوَ فِي مَعْنَى مَا ثَبَتَ عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّهُ قَالَ: وَالَّذِي فَلَقَ الْحَبَّةَ وَبَرَأَ النَّسَمَةَ إِنَّهُ لَعَهْدُ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَيَّ «أَنَّهُ لَا يُحِبُّنِي إِلَا ⦗٣٥٥⦘ مُؤْمِنٌ وَلَا يُبْغِضُنِي إِلَّا مُنَافِقٌ» . وَفِي حَدِيثِ بُرَيْدَةَ شَكَا عَلِيًّا فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَتَبْغِضُ عَلِيًّا؟ فَقُلْتُ: نَعَمْ، فَقَالَ: لَا تُبْغِضْهُ وَأَحْبِبْهُ وَازْدَدْ لَهُ حُبًّا، قَالَ بُرَيْدَةُ: فَمَا كَانَ مِنَ النَّاسِ أَحَدٌ أَحَبُّ أَليَّ مِنْ عَلِيٍّ بَعْدَ قَوْلِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
(كتاب اعتقاد ص٣٥٤)

Al-Imamul Baihaƙiy ya ci gaba da bayani, ya kawo wani athari da isnadinsa zuwa ga Al-Imamus Shāfi'iy (BH) Rahimahullah:

أَخْبَرَنَا أَبُو عَبْدِ اللَّهِ السُّلَمِيُّ، ثنا مُحَمَّدُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ يَعْقُوبَ الْحَجَّاجِيُّ، ثنا الْعَبَّاسُ بْنُ يُوسُفَ الشِّكْلِيُّ قَالَ: سَمِعْتُ الرَّبِيعَ بْنَ سُلَيْمَانَ يَقُولُ: سَمِعْتُ الشَّافِعِيَّ رَحِمَهُ اللَّهُ يَقُولُ فِي مَعْنَى قَوْلِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِعَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: مِنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ، يَعْنِي بِذَلِكَ وَلَاءَ الْإِسْلَامِ وَذَلِكَ قَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ ذَلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ مَوْلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَأَنَّ الْكَافِرِينَ لَا مَوْلَى لَهُمْ وَأَمَا قَوْلُ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ لِعَلِيٍّ: أَصْبَحْتَ مَوْلَى كُلِّ مُؤْمِنٍ، يَقُولُ: وَلِيُّ كُلِّ مُسْلِمٍ
(كتاب اعتقاد ص٣٥٥)

II- A cikin Sharhin As-Shaikh Abdurrahman ibn Abdurrahīm Al-Mubarakfūriy (1353 BH) Rahimahullah ga littafin Sunanut Tirmiziy, mai suna:

تحفة الأحوذي شرح جامع الترمذي

A ƙarƙashin wannan hadisin yana cewa 

قوله : " من كنت مولاه فعلي مولاه "
قيل معناه من كنت أتولاه فعلي يتولاه من الولي ضد العدو . أي من كنت أحبه فعلي يحبه وقيل معناه من يتولاني فعلي يتولاه

Ma'ana: Malamai sun ce ma'anar
 " من كنت مولاه فعلي مولاه "
Shi ne; Duk wanda yake ƙaunata to ALIYYU ma abin ƙaunarsa ne. Daga kalmar "MASOYI" kishiyar "MAƘIYI". Wato; duk wanda nake SO, to ALIYYU ma yana sonsa. Wasu kuma sun ce: Duk wanda ni ne majiɓincin al'amarinsa, to ALIYYU ma majiɓincin al'amarinsa ne.

III- Ibn Hajar Al-Haitamiy (973 BH) a cikin littafinsa

الصواعق المحرقة في الرد على أهل البدع والزندقة

ya yi maganganu a gurare da dama dangane da hadisin. Za mu kawo guri 1:

Bayan ya kawo shubuha ta 11 da ƴan Shi'a ke kawowa, wato hadisin من كنت مولاه game da shugabantar da sayyidina Aliyyu (R.A) akan dukkan Sahabbai bayan Annabi Muhammad ﷺ. Sai ya ce:

وَجَوَاب هَذِه الشُّبْهَة الَّتِي هِيَ أقوى شبههم يحْتَاج إِلَى مُقَدّمَة وَهِي بَيَان الحَدِيث ومخرجيه وَبَيَانه أَنه // حَدِيث صَحِيح // لَا مرية فِيهِ وَقد // أخرجه جمَاعَة كالترمذي وَالنَّسَائِيّ وَأحمد // وطرقه كَثِيرَة جدا وَمن ثمَّ رَوَاهُ سِتَّة عشر صحابيا وَفِي رِوَايَة لِأَحْمَد أَنه سَمعه من النَّبِي صلى الله عَلَيْهِ وَسلم ثَلَاثُونَ صحابيا وشهدوا بِهِ لعَلي لما نوزع أَيَّام خِلَافَته كَمَا مر وَسَيَأْتِي وَكثير من أسانيدها صِحَاح وَحسان وَلَا الْتِفَات لمن قدح فِي صِحَّته وَلَا لمن رده بِأَن عليا كَانَ بِالْيمن لثُبُوت رُجُوعه مِنْهَا وإدراكه الْحَج مَعَ النَّبِي صلى الله عَلَيْهِ وَسلم وَقَول بَعضهم إِن زِيَادَة اللَّهُمَّ وَال من وَالَاهُ الخ مَوْضُوعَة مَرْدُود فقد ورد ذَلِك من طرق صحّح الذَّهَبِيّ كثيرا مِنْهَا

(الصواعق المحرقة في الرد على أهل البدع والزندقة ص١٠٦-١٠٧)

MA'ANAR ZANTUKAN MALAMAN
Idan muka tattara waɗannan zantuka guda 3 za mu fitar da fa'idoji da dama. Ha guda 3 daga ciki:

• Hadisin yana fito da matsayin Sayyidina Aliyyu ibn Abi Ɗālib (R.A), da tabbatarwa masu zarginsa cewa yana da kaso a cikin KHUMUSI.

• Annabi ﷺ yana nufin duk wanda yake ƙaunarsa a matsayinsa na Manzon Allah ﷺ, to dole ya ƙaunaci Sayyidina Aliyyu ibn Abi Ɗālib (R.A)! Don haka duk wanda ba ya ƙaunar Sayyidina Aliyyu (R.A) to yana da matsala game da asalin IMANINSA.

• A aƙidar Ahlussunnah Salafiyyah suna ƙudirce cewa; duk wanda yake ƙin Sayyidina Aliyyu (R.A) to munafiki ne! (Muslim 78)

Don haka wanda zai fassara hadisin da cewa wai MANZON ALLAH ﷺ yana nufin Sayyidina Aliyyu (R.A) shi ne SHUGABA a bayansa, yana buƙatar ya kawo magabaci cikin SAHABBAI, AHLIL BAITI, Magabata na gari da Malaman Hadisi waɗanda suka fassara hadisin da ma'anar da suke ba shi.

In sha Allah a kashi na 3 za mu tattauna game da ma'anar kalmar مولى a harshen Larabci, da yadda ƴan Shi'a suka banƙara ta zuwa ga ma'anar da kwata-kwata ba ita Manzon Allah ﷺ yake nufi ba. Daga nan sai mu tattauna game da shi kan shi gurin da ake kira غدير خم ɗin, tare da warware shubuhohinsu game da gurin.

#AddiniDaRayuwa
#Ghadeer #salafiyyah 
#adamsharada 

(C) Adam Sharada

Comments