HADISIN GHADĪR KHUM DA SHUGABANCIN SAYYIDINA ALIYYU (R.A) A BAYAN ANNABI MUHAMMAD ﷺ(Fitowa ta Farko)
01| SHIMFIƊA
Asali babu wannan nassi ingantacce daga Allah (S.W.T) ko Annabi Muhammad ﷺ da suka ayyana sunan wani cikin Sahabban Manzon Allah ﷺ cewa; wane ne zai gaji Manzon Allah ﷺ a bayan wafatinsa, a matsayin jagoran al'ummar musulmi! Wannan ta sa bayan wafatin #ZaɓaɓɓenZaɓaɓɓu Annabi Muhammad ﷺ, sai Sahabbai suka haɗu suka zaɓi babban aboki kuma aminin Annabi ﷺ, Sayyidina Abubakar (R.A) a matsayin Khalifa, a wani gurin zaman mutanen Madinah mai suna سَقِيفَةِ بَنِي سَاعِدَةَ (Bukhariy, 2462).
Sahabbai sun yi wannan zaɓin ne bisa lura da wasu isharori da Manzon Allah ﷺ ya riƙa yi game da shugabancin sayyidina Abubakar (R.A) a bayansa. Misali:
I• Ƙissar umarnin da Annabi ﷺ ya a bayar a rashin lafiyarsa ta ajali cewa a sanya Abubakar (R.A) ya ba da sallah a madadinsa. Da yadda Annabi ﷺ ya fito cikin rashin lafiya Sayyidina Abbas ibn Abdul-Muɗɗalib (R.A) da sayyidina Aliyyu (R.A) suna riƙe da shi, aka yi wata irin sallah ta musamman.
(Bukhariy 687)
II• Ƙissar matar da ta zo gurin Annabi ﷺ kan wata buƙata, Annabi ﷺ ya ce mata idan ta dawo ba ta same shi ba, za ta samu Abubakar (R.A).
(Muslim 2386)
III• Hadisin Sahabi Huzaifah (R.A)z wanda yake ba da labarin wasiyyar da Annabi ﷺ ya yi musu cewa: "Ban san adadin (lokacin) zamana a tsakaninku ba (a raye)! Don haka ku yi riƙo da ABUBAKAR da UMAR. Ku yi riƙo da shiriyar AMMAR. Kuma duk abin da ya zo muku daga ABDULLAHI IBN MAS'UD to ku gasgata shi.
(Tirmiziy 3662, Ibn Mājah 92)
IV• Ƙissar mafarkin Annabi ﷺ, da ya sha ruwa a cikinta, har ya bawa sayyidina Abubakar (R.A) da Sayyidina Umar (R.A) su ma suka sha.
(Muslim 2392)
Ganin waɗannan dalilai ya sa ƴan Shi'a suka shiga suka fita suka banƙara wani hadisi na Manzon Allah ﷺ suka ce ai in sama da ƙasa za ta haɗe wai Manzon Allah ﷺ ya naɗa Sayyidina Aliyyu (R.A) ya zama Khalifa a bayansa. Akan haka suka kafirta kusan dukkan. Sahabbai in banda wasu ƴan tsiraru da ba su ɗara goma ba. Akan haka suka gina mafi yawan miyagun aƙidunsu na cin zarafin almajiran Manzon Allah ﷺ, ta hanyar tuhumarsu da kaucewa wasiyyar Manzon Allah ﷺ! Wanda Allah (S.W.T) Ya barrantar da almajiran AnnabinSa daga aikatawa.
02| SABABIN HADISIN GHADĪR KHUM
Malaman hadisi suna da wani fanni na kimiyyr Hadisi mai suna
أسباب ورود الحديث
Wanda yake bincike da dangane da dalilin (sababi) da ya sa aka samu wani HADISI na Manzon Allah ﷺ. Amfaninsa shi ne taimakawa mai bincike wajen gano haƙiƙanin ma'anar da hadisin ke ɗauke da ita. Daga cikin mafi shaharar littattafan fannin akwai
اللمع في أسباب الحديث
Na Jalaluddeen As-Siyuɗiy Rahimahullah.
Wannan Hadisi na GHADĪR shi ma yana da sababbin samuwarsa. Wadda ita za ta yi mana jagoranci wajen fahimtar haƙiƙanin ma'anar hadisin in sha Allah.
Al-Imamul Bukhariy ya kawo asalin ƙissar a hadisi mai lamba 4349 kamar haka:
حَدَّثَنِي أَحْمَدُ بْنُ عُثْمَانُ، حَدَّثَنَا شُرَيْحُ بْنُ مَسْلَمَةَ، حَدَّثَنَا إِبْرَاهِيمُ بْنُ يُوسُفَ بْنِ إِسْحَاقَ بْنِ أَبِي إِسْحَاقَ، حَدَّثَنِي أَبِي، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ، سَمِعْتُ الْبَرَاءَ ـ رضى الله عنه ـ. بَعَثَنَا رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم مَعَ خَالِدِ بْنِ الْوَلِيدِ إِلَى الْيَمَنِ، قَالَ ثُمَّ بَعَثَ عَلِيًّا بَعْدَ ذَلِكَ مَكَانَهُ فَقَالَ مُرْ أَصْحَابَ خَالِدٍ، مَنْ شَاءَ مِنْهُمْ أَنْ يُعَقِّبَ مَعَكَ فَلْيُعَقِّبْ، وَمَنْ شَاءَ فَلْيُقْبِلْ. فَكُنْتُ فِيمَنْ عَقَّبَ مَعَهُ، قَالَ فَغَنِمْتُ أَوَاقٍ ذَوَاتِ عَدَدٍ.
Asali wata runduna ce Annabi ﷺ ya tura zuwa Yemen a ƙarƙashin jagorancin sahabi Khalid Ibnul Walīd (R.A). Daga baya sai Annabi ﷺ ya tura sayyidina Aliyyu (R.A) ya jagoranci rundunar. Har ma aka samu ganima mai yawa!
A hadisi na 4350 da Al-Imamul Bukhariy ya kawo, Sahabi Buraidah Al-Aslamiy (R.A) ya faɗi abin da ya faru bayan an samu ganimar can:
حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ ، حَدَّثَنَا رَوْحُ بْنُ عُبَادَةَ ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ سُوَيْدِ بْنِ مَنْجُوفٍ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ بُرَيْدَةَ ، عَنْ أَبِيهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ : بَعَثَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلِيًّا إِلَى خَالِدٍ لِيَقْبِضَ الْخُمُسَ وَكُنْتُ أُبْغِضُ عَلِيًّا وَقَدِ اغْتَسَلَ، فَقُلْتُ لِخَالِدٍ : أَلَا تَرَى إِلَى هَذَا ؟ فَلَمَّا قَدِمْنَا عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَكَرْتُ ذَلِكَ لَهُ، فَقَالَ : " يَا بُرَيْدَةُ، أَتُبْغِضُ عَلِيًّا ". فَقُلْتُ : نَعَمْ. قَالَ : " لَا تُبْغِضْهُ ؛ فَإِنَّ لَهُ فِي الْخُمُسِ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ "
Sahabi Buraidah (R.A) ya ji haushin sayyidina Aliyyu (R.A) saboda ya ɗauki wata kuyanga daga cikin KHUMUSIN da aka karɓa, har ma ya yi saɗaka da ita. Da suka je gurin Annabi ﷺ sai shi sahabin yake kai ƙarar sayyidina Aliyyu (R.A) yana nuna rashin jin daɗinsa. Daga nan ne sai Annabi ﷺ ya yi masa nasiha game da jin haushin Sayyidina Aliyyu ta hanyar bayyana masa matsayinsa, da girman kason da yake da shi na KHUMUSIN a matsayinsa na ɗaya daga cikin AHLIL BAITI.
Daga wannan gaɓar ne fa, Annabi Muhammad ﷺ ya yi wancan bayani a Ghadir Khum wanda za mu tafi a hankali zuwa gurin in sha Allah.
In sha Allah a kashi na 2 za mu tattauna akan shi kanshi hadisin Ghadīr ɗin da maganganun malaman hadisi akansa. Sai kuma kalmar مولى da ta zo a cikin hadisin. Sannan mu tattauna akan shi kansa filin Ghadīr ɗin (Geographically). Daga nan sai mu warware manyan shubuhohi 3 da ƴan Shi'a ke yaɗawa ƙarƙashin hadisin. Sai mu cike da karya gadar Ƙum (cikin manyan biranen ƙasar Iran) da ƙalubale ga ƴan Shi'a.
#ghadir2023
#ghadir1444
#addinidarayuwa
#adamsharada
(C) Adam Sharada
14 Zul-Hijjah 1444 (July 2nd, 2023)
Comments
Post a Comment