SHIN ANNABI MUHAMMAD ﷺ YA YI TARAYYA DA ALLAH (S.W.T) A WASU SIFFOFI?

GABATARWA
Daga cikin Aƙidar Ahlussunnah Salafiyyah a babin Tauhidi akwai; ƙudirce cewa lallai Allah (S.W.T) Yana da SUNAYE da SIFFOFI. Alƙur'ani maigirma ya tabbatar da cewa tabbas Allah (S.W.T) Yana da sunaye mafiya kyawu:

وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَىٰ فَادْعُوهُ بِهَا ۖ وَذَرُوا الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَائِهِ ۚ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
 (Al-A'arāf: 180)

Game da siffofi kuwa, wannan ya maimaitu sau ba adadi a cikin Alƙur'ani maigirma. Allah (S.W.T) da kanSa ya tabbatar mana yana da siffofi kamar Ji da Gani (Asshūra: 11), Magana (Annisā'i: 164), Ilimi (Al-An'ām: 59), Rayuwa (Albaƙarah: 255), Soyayya (Al-Mā'idah: 54), Fushi (Al-Mā'idah: 60),........ Jin Ƙai (Al-A'arāf: 156, Gāfir: 7) da sauransu.

SHIN ANNABI MUHAMMAD ﷺ SUNA KAMA DA ALLAH (S.W.T) A SIFFOFI?

Asali a wannan babin; Allah (S.W.T) bayan ya tabbatarwa da kanSa siffofi, sai ya ce:

فَاطِرُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا وَمِنَ الْأَنْعَامِ أَزْوَاجًا ۖ يَذْرَؤُكُمْ فِيهِ ۚ لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
(Asshūra: 11)

A cikin ayar Allah (S.W.T) Ya bayyana ƙarara cewa

لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ
"Babu wani abu da ke kama da Shi!"

Malaman Tafsiri Allah ya saka musu da alkhairi sun yi sharhin wannan gaɓa. Ha misalai guda 3 kacal:

I- Alƙurɗubiy Rahimahullah:

وقد قال بعض العلماء المحققين : التوحيد إثبات ذات غير مشبهة للذوات ولا معطلة من الصفات

II- Ibnu Katheer Rahimahullah:

ليس كخالق الأزواج كلها شيء ; لأنه الفرد الصمد الذي لا نظير له

III- Albaghawiy Rahimahullah ya hakaito atharin sahabi Ibnu Abbas (R.A) da yake fassara ayar da cewa:

ليس له نظير

Kenan, babu wani mahaluƙi ko da Mala'ika ne makusanci ko Annabi da aka aiko wanda yake kama da Allah (S.W.T) a cikin cikin wasu siffofi.

Wannan kuma shi ne maganar da Malam Musa Asadus Sunnah (Hafizahullah) ya bayyana! Tabbas ƙudirce cewa Annabi Muhammad ﷺ yana da wata siffa daga cikin siffofin Allah (S.W.T) kafirci ne. domin ya saɓa da wannan ayar da Allah (S.W.T) da kamSa ta bayyana a cikin Alƙur'ani maigirma.

A nan ne aka raba gari tsakanin Ahlussunnah Salafiyyah da ƙungiyoyin ɓata karkatattu:

1- Mu'utazilah da Jahamiyyah (Mu'utazilawa da Jahamawa): Su ne masu korewa Allah (S.W.T) siffofi baki ɗaya.

2- Ashā'irah (Ash'ariyyawa): Su kuma sun zaɓi wasu siffofi ne guda 7 (Ilimi, Iko, Rayuwa, Nufatar aikata wani aiki, Ji, Gani da Magana) kacal sun tabbatarwa Allah (S.W.T), sannan sai suka yi tawilin sauran siffofin Allah (S.W.T) suka murguɗa tare da banƙara ma'anoninsu zuwa ga son zuciyarsu.

3- Ahlussunnah: Su ne suka tabbatarwa da Allah (S.W.T) dukkanin siffofin da Ya siffanta kanSa da su, ko ManzonSa ﷺ ya siffanta shi da su, ba tare da kamantawa ko buga misali ko ma korewa Allah (S.W.T) wata siffa daga cikin siffofinSa ba!

SHIN SIFFOFIN ANNABI MUHAMMAD ﷺ IRIN NA ALLAH (S.W.T) A CIKIN رءوف رحيم???

Da yake shi mai maganar aya ya kawo da zaton tana marawa jahilcinsa baya. Iya ayar da muka kawo da ta ke kore kamanceceniya tsakanin Allah (S.W.T) da bayinSa a cikin siffofi, za ta wadatar da mu da duk wanda yake da zuciya mai tsafta wajen fahimtar zurfin jahilci da karkacewar mai maganar, wanda ya taƙarƙare yana ƙoƙarin fito da kuskuren Mal. Asadus Sunnah, sai ga jahilcinsq ga bayyana a fili.

AYA TA FARKO: SURATUL BAƘARAH AYA TA 143
وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَاكُمْ أُمَّةً وَسَطًا لِّتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ وَيَكُونَ الرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيدًا ۗ وَمَا جَعَلْنَا الْقِبْلَةَ الَّتِي كُنتَ عَلَيْهَا إِلَّا لِنَعْلَمَ مَن يَتَّبِعُ الرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ ۚ وَإِن كَانَتْ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى الَّذِينَ هَدَى اللَّهُ ۗ وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَانَكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِالنَّاسِ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ

AYA TA BIYU: SURATUT TAUBAH AYA TA 128
لَقَدْ جَآءَكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِٱلْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ

• Yadda siffofin Ji da Gani da Magana na Allah (S.W.T) suke da bambanci da na halittunSa, saboda ba wanda yake kama da Shi, haka nan siffofin رءوف رحيم ma ba iri ɗaya ba ne tsakanin na Allah (S.W.T) da na Annabi Muhammad ﷺ!

• Babu wani cikin malaman ƙwarai daga Sahabbai da limaman shiriya da ya taɓa yin wannan maganar ya ce waɗannan ayoyin guda 2 suna nuna tarayya (collinearity) a cikin siffofi tsakanin Allah (S.W.T) da ManzonSa ﷺ!

• Mafita ga musulmi shi ne fassara Alkur'ani da Sunnah da irin fassarar da magabata nagari: Sahabbai da mabiya tafarkinsu suka yi. Ta haka ne za mu rabauta a duniya da lahira.

RUFEWA
Ƙudirce cewa Annabi Muhammad ﷺ yana da wata siffa irin ta Allah (S.W.T) kafirci ne! Domin ya ci karo da abin da Allah (S.W.T) Ya tabbatar a cikin Alƙur'ani maigirma!


Comments