SHAIDAR MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR GA MARIGAYI SARKIN DUTSE DR. NUHU MUHAMMAD SUNUSI RAHIMAHULLAH
A bakin marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah nake jin wannan suna, da irin kyawawan halayensa na son addini da shigewa gaba a cikin al'amurran addini! Da wuya munasaba ta biyo malam Ja'afar Rahimahullah ya ambaci wannan Basarake bai tsaya ya yanke shi, ya faɗi alkhairansa ba. Wannan kam sanannen al'amari musamman tsakanin makusantan Shaikh Ja'afar Rahimahullah cikin ɗalibansa, da kuma sauran ɗalibai masu bibiyar karatuttukan Malam.
Ko a ranar da marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah ya yi tafsirinsa na ƙarshe a Maiduguri a shekarar 2006, sai da ya yabawa namijin ƙoƙarin da mai martaba Sarkin Dutse ya yi na kafa ɗakin karatu na addinin Musulunci (Islamic Library). Shaikh Ja'afar Rahimahullah ya ambaci yadda wannan Basarake ya sa aka tara ƙwararrun masana gogaggun malaman addini, suka fitar da jadawalin duk wani littafi da malamai da ɗaliban ilimi ke buƙata, aka tafi ƙasashen aka sayo, aka gina katafaren ɗakin karatu, aka shaƙe shi da littattafan. Domin sauƙaƙawa malamai da ɗaliban ilimi hanyoyin karatu da nazari a cikin addinin Musulunci. Har yanzu haka wannan library tana nan, kuma ɗalibai da malamai suna ci gaba da amfana da ita. Wanda in sha Allah sadaƙa ce mai gudana ga mai martaba!
A cikin bakandamiyar khuɗubar Malam Ja'afar Rahimahullah mai taken "Wasiƙar Sarakuna" ya yi ishara game da irin kyawawan halaye da salon adalcin wannan adalin basarake, mai martaba marigayi sarkin Dutse Rahimahullah.
Haka nan a cikin khuɗubar Shaikh Ja'afar Rahimahullah game da kisan ramuwar gayya da aka yiwa ar*na sakamakon ki*san kiy*ashi bisa zal*unci da aka yiwa ƴan uwa*nmu musu*lmi a wasu sasannin jihar Plateau, a ƙarƙashin shugab*ancin gwa*mna Joshua Dariye, da haɗin gwiwar ƙungiyar C *A* N; a tsakiyar wannan huɗuba Malam Ja'afar Rahimahullah ya kakkasa sarakunanmu zuwa gida 3 kamar haka:
1- Kaso na farko: Su ne sarakunan da ake zukatan talakawa ke nutsuwa da matsayarsu, kuma ake musu fatan alkhairi akan abubuwa da dama da suka faru a Najeriya na siyasa ko na addini.
Sarakunan da ya kawo a wannan kason su ne:
• Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari
• Sarkin Dutse (shi ne marigayi Dr. Nuhu Muhammad Sunusi)
• Sarkin Kazaure
• Sarkin Bargu
• Sarkin Suleja
• Sarkin Fika
• Sarkin Askira a cikin jihar Borno
• Shehun Bama
• Sarkin Biu
• Sarkin Katsina
da sauran waɗansu ɗaiɗaiku makamantansu.
Sai Shaikh Ja'afar Rahimahullah ya ce "Amma waɗannan su ne matsayarsu, da taimakonsu, da kulawarsu da haƙƙin talakawansu, ya ɗara na sauran waɗanda ake buga misali da su fitowa fili."
2- Kashi na 2: Malam Ja'afar Rahimahullah ya ce "waɗanda jama'a suke kuka da su, musamman a daidai wannan lokaci, musamman a daidai wannan jamhuriya ta uku, musamman a cikin wannan baƙin mulki na Obasanjo wanda kowa ke shan wahala a ciki. Tsakanin musulmi da Kirista, tsakanin mai kuɗi da mara shi, tsakanin ɗan birni da ɗan ƙauye, tsakanin makiyayi da ɗan kasuwa da manomi."
Malam Ja'afar Rahimahullah ya buga misali da wasu sarakuna guda 2.
• Sarkin Gwandu Jakolo
• Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris
3- Kaso na uku: Malam Ja'afar Rahimahullah ya ce "waɗanda jama'a ke kallonsu kallo na mutunci, suna da babba matsayi a cikin zukatan da dama daga cikin talakawa. Suna da kwarjini ko wajen taro suka zo. Ko cewa aka yi ga sarki, sai ka ɗauka su kaɗai ne sarakuna, sauran ba sarakuna ba ne! Suna da kalma abar saurare in an ce za su yi bayani! Matsayinsu ya shahara ba a cikin Najeriya ba, har wajen Najeriya. Masarautunsu da suke mulki suna da tsawon lokaci a tarihi. Suna da zamani mai tsawon gaske. Suna da fararen takardu na tarihi kyawawa a baya, a waɗansu zamunna da suka wuce tun shekaru aru-aru."
Sai Shaikh Ja'afar Rahimahullah ya ba da misalin irin waɗannan sarakuna guda 3 kamar haka:
• Sarkin Musulmi na Sakkwato
• Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero
• Shehun Borno Alhaji Mustafa Umar
Daga nan sai malam Ja'afar Rahimahullah ya ce "waɗannan mutane har yanzu jama'a suna ganinsu da ragowar mutunci, da ragowar ƙima. Har yanzu kuma suna da ƙima ba wai a cikin Najeriya kaɗai ba, har a wajen Najeriya! Har yanzu da dama daga cikin sarakuna sukan ɗauki kansu su sarakuna ne kaɗai a fadarsu. Amma in sun zo Fadar Sultan Amirul Mu'uminīna a Sakkwato, ko fadar mai martaba sarkin Kano, ko Shehun Borno: gani suke ba su da bambanci da sauran talakawa! Ko in ce bambancinsu da sauran talakawan kaɗan ne......"
Babu shakka duk wani musulmi da ya san ina aka kwana aka tashi a ƙasar nan, duk wani Ahlussunnah da ya san faɗi-tashi da wahalhalun da da'awar Sunnah ta keto a Najeriya, ya san cewa lallai an rasa wannan babban giɓi mai wuyar cikewa! A lokacin da malamanmu suke tallata da'awar ana binsu da duka da zagi da jifa, ana yiwa rayuwarsu barazana, wannan dattijon arziƙi, wannan adalin basarake shi ne ya janyo su a jika, ya ba su dukkan wata gudunmawa da kujerarsa, da fadarsa, da lokacinsa, da aljihunsa, da ƙarfin faɗa a jinsa, har da'awar Sunnah ta kai matakin da yau ta gama mamaye Najeriya!
Babanmu Shaikh Dr. Abubakar Birnin Kudu Hafizahullah su za su ba mu labari. Yadda ya kasance tare da wasu da ƙarfafarsu wajen yaɗa Sunnah a masarautarsa, da yadda ya lazimci majalisansa. Tabbas Ahlussunnah sun shiga maraici!
Tabbas har Allah (S.W.T) ya naɗe ƙasa ba za mu manta da fararen takardun tarihi da wannan adalin basarake ma'abocin addini da hidimtawa da'awar Sunnah ya bari ba! Fatanmu Allah ya gafarta masa zunubansa. Allah ya lulluɓe shi da rahamarSa. Allah ya sa aljanna makomarsa. Allah ya kuka masa da iyalinsa, kamar yadda ya kula da addini a kwanakin rayuwarsa. Allah ya yi masa rahama. Allah ya tashe shi a tawagar salihan bayi ranar alƙiyama.
إنَّ لِلَّه ما أَخَذ ولَهُ ما أَعطَى، وكلُّ شَيءٍ عِنده بِأجَل مُسمَّى فَلتَصبِر ولتَحتَسِب
Adam Sharada
MD, At-Tasfiyah24
31st January, 2023
Comments
Post a Comment