RANAR MASOYA TA SAINT VALENTINE


GABATARWA

Saint Valentine ɗaya ne daga cikin manyan malaman addinin Kirista da suka kai matsayin jakadu masu rawaito Bible, wanda ya rayu a ƙarni na 3 a daular Rumawa ta Kiristoci (Roman Empire). Ya rasu ranar 14 ga watan Fabrairu a shekara ta 269 AD a birnin Rum na ƙasar Italiya.

Saboda maɗaukakin matsayinsa a gurin mabiya addinin Kirista, suke gina majami'u (churches) sanya sunansa, musamman a ƙasar Italiya (Italy) inda nan ne babbar fadar Fafaroma (jagoransu na duniya)!

RANAR 14 GA WATAN FABRAIRU

Bayan rasuwar Saint Valentine babban malami mai fatawa a addinin Kirista a wannan rana, Kiristoci saboda ƙaunarsa da suke a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa don yaɗa addinin Kirista (wanda ya yi mutuwar shahada a cewarsu), sai suka ware ranar a matsayin ranar girmamawa gare shi. A cikin shekarun 1500s Kiristoci mabiya Saint Valentine suka fara tura saƙonnin SOYAYYA (Love Messages) zuwa ga masoyansu, domin tunawa da masoyinsu Valentine da ya rasu. Suna kiran ranar da Valentine's Day, ko Saint Valentine's Day, ko kuma Feast of Saint Valentine. Shi "Feast Day" shi ne sunan bikin da mabiya addinin Kirista ɗin ke yi, domin tunawa da waliyyinsu Saint Valentine da ya rasu a irin wannan rana (14th February).

Abubuwa sun ci gaba da haɓɓaka har zuwa shekarun 1700s, lokacin da aka sabunta wannan biki, ta hanyar buga katinan saƙonnin SOYAYYA ana aikewa masoya da shi. A tsakiyar shekarun 1800s wannan biki ya sake sauya salo a ƙasashen Amurkawa (Americas) inda aka fara sayar da katinan ranar masoya (Commercial Valentine's Card). Daga nan kuma likkafa ta ɗaga zuwa abin da muke gani yau yana faruwa a duniya, masoya suna miƙa kyaututtukan furanni musamman jajaye (red roses 🌹) da alawoyi, da sumbata (kisses) tsakanin samari da ƴan mata da makamantansu.

MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI GAME DA WANNAN BIKI NA RANAR MASOYA

Akwai muhimman batutuwa guda 3 da ya kamata mu kalla game da wannan biki na ranar masoya: 

1- Shi dai Saint Valentine Kirista ne mai da'awar Alloli guda 3 (Trinity). Matsayin addininsa a Alƙur'ani da Hadisan Manzon Allah (S.A.W) ga misalai kamar haka:

Kiristoci suna kiran Annabi Isah (A.S) a matsayin Allah abin bauta, sai Allah (S.W.T) ya ce mana wannan aikin ya mayar da su KAFIRAI

لَقَدْ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ ۖ وَقَالَ ٱلْمَسِيحُ يَٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱعْبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبَّكُمْ ۖ إِنَّهُۥ مَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِ ٱلْجَنَّةَ وَمَأْوَىٰهُ ٱلنَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍۢ
(Al-Mā'idah: 72)

Kiristoci suna da'awar wai Allah 3 ne (Trinity), Allah (S.W.T) ya ce mana wannan da'awar ta sa sun zama KAFIRAI

لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ ثَالِثُ ثَلَاثَةٍ ۘ وَمَا مِنْ إِلَٰهٍ إِلَّا إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۚ وَإِن لَّمْ يَنتَهُوا عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
(Al-Mā'idah: 73)

Kiristoci sun yiwa Allah (S.W.T) mafi girman zalunci na jingina masa ɗa

وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ عُزَيْرٌ ٱبْنُ ٱللَّهِ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَى ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ ٱللَّهِ ۖ ذَٰلِكَ قَوْلُهُم بِأَفْوَٰهِهِمْ ۖ يُضَٰهِـُٔونَ قَوْلَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبْلُ ۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُ ۚ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
(Attaubah: 30)

Allah (S.W.T) ya gaya mana addininsu ɓataccen addini ne

وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ الْيَهُودُ وَلَا النَّصَارَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى اللَّهِ هُوَ الْهُدَىٰ ۗ وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَاءَهُم بَعْدَ الَّذِي جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ ۙ مَا لَكَ مِنَ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
(Al-Baƙarah: 120)

Za mu taƙaita da ambaton hadisai gudun tsawaitawa.

2- Wannan biki kamar yadda muka ji biki ne na Kiristoci, waɗanda muka kawo misalai daga Alƙur'ani maigirma game da matsayin addininsu da ɓacin tafarkinsu na aƙida a gurin Allah (S.W.T). Abin tambaya, shin ya halatta musulmi ya riƙa kwaikwayon Kiristoci a cikin bukukuwansu?

Al-Imam Abiy Dawud Assijistāniy (ya rasu 275 BH) a cikin Sunan nasa hadisi na 4031, ya rawaito da isnadi (حسن صحيح) zuwa ga Sahabi Abdullahi Ibn Umar (R.A) shi kuma zuwa ga Annabi Muhammad (S.A.W) kamar haka:

عَنِ ابْنِ عُمَرَ قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : "مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ".

Annabi (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya kwaikwayi wasu mutane, to ya zama su!"

A cikin littafin عون المعبود شرح سنن أبي داود Asshaikh Al-Azeem Abādiy (ya rasu 1326 BH) Rahimahullah ya hakaito maganganun malamai kamar Abdurra'uf Almunāwiy, Mulla Aliy Alƙāriy da Shaikhul Islam Ibn Taimiyah Allah ya gafarta musu baki ɗaya, waɗanda duka fassara hadisin da haramcin kwaikwayon mushirikai a cikin addininsu da al'adunsu.

Ga maganar Ibn Taimiyah (ya rasu 728 BH) Rahimahullah da ya hakaito:
    
قال شيخ الاسلام بن تَيْمِيَةَ فِي الصِّرَاطِ الْمُسْتَقِيمِ وَقَدِ احْتَجَّ الْإِمَامُ أَحْمَدُ وَغَيْرُهُ بِهَذَا الْحَدِيثِ وَهَذَا الْحَدِيثُ أَقَلُّ أَحْوَالِهِ أَنْ يَقْتَضِيَ تَحْرِيمَ التَّشَبُّهِ بِهِمْ كَمَا فِي قَوْلِهِ مَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ وَهُوَ نَظِيرُ قَوْلِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو أَنَّهُ قَالَ مَنْ بَنَى بِأَرْضِ الْمُشْرِكِينَ وَصَنَعَ نَيْرُوزَهُمْ وَمِهْرَجَانَهُمْ وَتَشَبَّهَ بِهِمْ حَتَّى يَمُوتَ حُشِرَ مَعَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَقَدْ يُحْمَلُ هَذَا عَلَى التَّشَبُّهِ الْمُطْلَقِ فَإِنَّهُ يُوجِبُ الْكُفْرَ وَيَقْتَضِي تَحْرِيمَ أَبْعَاضِ ذَلِكَ وَقَدْ يُحْمَلُ عَلَى أَنَّهُ مِنْهُمْ فِي الْقَدْرِ الْمُشْتَرَكِ الَّذِي يُشَابِهُهُمْ فِيهِ فَإِنْ كَانَ كُفْرًا أَوْ مَعْصِيَةً أَوْ شِعَارًا لَهَا كان حكمه كذلك

وقد روي عن بْنِ عُمَرَ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنِ التَّشَبُّهِ بِالْأَعَاجِمِ وَقَالَ مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ وَذَكَرَهُ الْقَاضِي أَبُو يَعْلَى

وَبِهَذَا احْتَجَّ غَيْرُ وَاحِدٍ مِنَ الْعُلَمَاءِ عَلَى كَرَاهَةِ أَشْيَاءَ مِنْ زِيِّ غَيْرِ الْمُسْلِمِينَ وَأَخْرَجَ التِّرْمِذِيُّ مِنْ حَدِيثِ عَمْرِو بْنِ شُعَيْبٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِغَيْرِنَا انْتَهَى كَلَامُهُ مُخْتَصَرً!
(J 11, shafi na 52)

A dunƙule, Shaikhul Islam Ibn Taimiyah Rahimahullah yana cewa: Wannan hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) dalili ne akan haramcin kwaikwayon mushirikai a cikin addininsu da al'adunsu. Bikin da ake yau a duniya na ranar Saint Valentine yana ƙarƙashin wannan hadisin.

Wannan shi ne matsayin kwaikwayon Kiristoci a bikinsu na tunawa da malaminsu Valentine!

3- Dalilin da muka ambata daga Annabi Muhammad (S.A.W) ya ƙarrara cewa: HARAMUN ne kwaikwayon mushirikai. Menene HARAMUN a shari'ar Musulunci?

HARAMUN wani nau'i ne na hukunce-hukuncen shari'ar Musulunci. Ga abin da malaman Usul suka fassara mana ma'anar HARAMUN a cikin Alƙur'ani da SUNNAH:

هو ما طلب الشرع تركه والكف عنه على وجه الحتم والإلزام، أو هو ما يثاب تاركه ويعاقب فاعله
Shi ne duk abin da shari'ar Musulunci ta nemi musulmi ya ƙaurace masa, ya kamewa daga faɗawa cikinsa, ta fuskar ikon bari  (ɗan adam zai iya) da kuma tilastawa. Shi ne abin da idan aka bari (aka bar Haramun) za a samu lada, idan kuma aka aikata (Haramun) za a samu zunubi.

Wannan shi ne ta'arifin HARAMUN a gurin malaman Musulunci. Kuma shi ne sikelin da za mu iya auna bikin ranar tunawa da Saint Valentine da KIRISTOCI suka ƙirƙira, wanda ƴan birni cikin wayayyyun matasan musulmi yau muke kwafowa da sunan wayewa da burgewa! 

ƊAURAYA

Mafi tsaftar rayuwa abar kwaikwayo ita ce rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W), wanda ya zo mana da alkhairin duniya da lahira. Indai da gaske muke yin musuluncin nan, to mu riƙa kallon Annabinmu a matsayin fitilar rayuwarmu. Allah (S.W.T) ya haska mana wannan fitila mai haske a cikin Alƙur'ani maigirma:

لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِيهِمْ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِّمَن كَانَ يَرْجُواْ ٱللَّهَ وَٱلْيَوْمَ ٱلْءَاخِرَ ۚ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْغَنِىُّ ٱلْحَمِيدُ
(Al-Mumtahanah: 6)

Shaikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah a cikin muhadharar ALAMOMIN SON MANZON ALLAH (S.A.W) yana cewa: "Koyi da shi (Annabi) shi ne tsira, yin imani da shi da ƙanƙamewa karantarwarsa shi ne lasisin shiga aljanna ranar alƙiyama!"

© Adam Sharada
 14- February 2023

Comments