TSAKANIN KIMIYYA DA ADDINI 001
TSAKANIN KIMIYYA DA ADDININ MUSULUNCI
00|| GABATARWA
Musamman ma zallar ƴan bokon musulmi waɗanda galibinsu ba su samu leƙawa makarantar Islamiyya ba a rayuwarsu, galibinsu suna kallon ilimin addinin a matsayin wani ƙauyanci, sannan suna kallon ma'abota addini a matsayin ƙauyawa gidadawa. Idan an zo batun nazariyyar kimiyya, suna ganin kwata-kwata addinin musulunci ba shi da hurumin tsoma baki a cikin SCIENCES, saboda su a tunaninsu waɗannan laws, theories, theorem, formulae, equations, statements dss da manyan malaman Science suka samar addini bai isa ya iya samar da su ba.
Wannan ta sanya ko da a nan facebook sau tari idan na yi rubutu na nazarci wani abu na kimiyya (Physics) a sikelin addinin Musulunci, suna ganin kamar mun kauce hanya, ko muna haɗa kashi.
01|| MENENE KIMIYYA (SCIENCE)?
A dunƙule malamai suna ta'arifin kimiyya da:
"Science is the pursuit and application of
knowledge and understanding of the natural and social world following a systematic methodology based on evidence."
Ma'ana: Ita Kimiyya wasu ƙa'idoji ne na ilimi da malaman fannin suka tsara, waɗanda ake nazarin duniya da halittun cikinta masu rai da marasa rai, da ma rayuwarsu a cikinta.
Idan mun lura da kyau za mu ga; ita kimiyya ƙa'idoji ne da malamai suka kafa, su ma bisa dogaro da su hujjoji ta hanyar bincikensu da suka gudanar. Wannan ta sa bincike da nazari da tahƙiƙi (bin diddigi) suka zama manyan turakun da aka aza tukunyar da ake girka kimiyya akansu.
02|| SIFFAR ILIMIN KIMIYYA
Akwai abubuwa guda 2 waɗanda su ne ilimin kimiyya ke gudana akansu:
I- Scientific Theory: Shi ne abin da malaman kimiyya suka gano ta hanyar bin diddigi da ƙwaƙƙwafin wani abu. A nan malaman suna ɗaukar wani tunani da ya zo musu (idea), sai su samar da bayanai/kayan aiki (data) da za su fassara musu wancan tunanin (hypothesis), sai su bi diddigin wannan fassara ko bayani su ga abin da ya ƙunsa (test hypothesis), abin da suka samu na sakamako a wannan mataki na ƙarshe shi ake tabbatarwa a matsayin SCIENTIFIC THEORY.
Misalinsu su ne kamar: Special Relativity (1905) da General Relativity (1915) na Albert Einstein, Evolution of natural selection (1859) na Charles Darwin dss.
II- Scientific Laws: Shi ne abin da malaman kimiyya suka fahimci yana maimaita kansa a bisa ɗabi'a ta duniya da abin da ke cikinta.
Misalansu su ne: Newton's Law of Universal Gravitation, Law of Conservation of Energy, 3 Laws of Thermodynamic dss.
03|| MANYAN HANYOYIN BAYANIN ILIMIN KIMIYYA
Ilimin kimiyya yana tafiya ne ta wasu manyan hanyoyi guda 2 waɗanda babu wata gargada akansu:
I- Theoritical: Su ne bayanai na baka akan allo game da ƙa'idoji da abubuwan da nazari ya tabbatar bisa hujjoji na ilimi. Misali, ɓangarorin darussan kimiyya da ake koyarwa a cikin aji akan allo.
II- Practical: Su ne hanyoyin nazarin kimiyya ta hanyar bincike da aune-aune ko gwaje-gwaje ta hanyar amfani da kayayyakin aikin binciken kimiyya (aparatus and equipments)a cikin ɗakunan binciken kimiyya (laboratory).
04|| ƁANGARORIN ILIMIN KIMIYYA
Kusan babu saɓani a tsakanin malamai kan cewa kimiyya tana da manyan ɓangarori guda 2, waɗanda kowannensu kogi ne mai faɗi da zurfin da har abada ba za a iya kaiwa ƙarshensa ba.
I- Physical Science: Ita ce kimiyyar da ta ƙunshi nazarin sandararrun abubuwan da ke cikin duniya (non-livinthings). Sun ƙunshi manyan ɓangarori masu zaman kansu kamar Physics, Chemistry, Astronomy dss.
II- Natural Science: Wannan ɓangaren kuma ya ƙunshi nazarin kimiyyar abubuwa masu rai a cikin wannan duniyar. Shi ne ilimin Biology da ƴaƴan da ya haifa kamar: Ecology, Physiology, Molecular Biology, Genetics, Microbiology dss.
05|| MENENE ADDINI?
• Addini wata hanya ce ta gudanar da rayuwar ɗan adam a ƙarƙashin wasu dokoki ko tsare-tsare. Da gwargwadon yadda ɗan adam ya gudana a bisa tsarin koyarwar wani addini, da gwargwadon yadda ake jingina shi zuwa ga wannan addinin.
• Addinin Musulunci wani tsararren tafarki ne da Allah (S.W.T) ya tsarawa ɗan adam don ya gudana akansa a nan duniya, wanda ya ginu kacokan akan kaɗaita Allah (S.W.T) da bauta da nesantar jingina duk wani nau'i na wannan bautar ga waninSa.
Saboda wannan tsarin bauta ne Allah (S.W.T) ya aiko Annabawa da Manzanni zuwa ga dukkan duniya da saƙon
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ ۖ
Kuma haƙiƙa mun aika da Manzo (musamman) ga kowacce al'umma da saƙon; a bautawa Allah sannan a nisanci (bautar) ɗagutu...
(Annahli: 36)
Wanda kuma shi ne addinin da dukkanin Annabawa tun daga Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) har zuwa kan Annabi Muhammad (S.A.W), suka kira al'ummominsu zuwa gare shi, domin ginawa ɗan adam danganta tsakaninsa da Allah, da kuma zamantakewar rayuwa a tsakanin bayi a ban ƙasa.
Allah ya jiƙan Al-Imamul Ƙahɗāniy, Muhammad ibn Sālih Abu Muhammad, yana da baitukan masu kyawun gaske a cikin nūniyyarsa:
وشريعة الإسلام أفضل شرعة ... دين النبي الصادق العدنان
هو دين رب العالمين وشرعه ... وهو القديم وسيد الأديان
هو دين آدم والملائك قبله ... هو دين نوح صاحب الطوفان
وله دعا هود النبي وصالح ... وهما لدين الله معتقدان
وبه أتى لوط وصاحب مدين ... فكلاهما في الدين مجتهدان
هو دين إبراهيم وابنيه معا ... وبه نجا من نفحة النيران
وبه حمى الله الذبيح من البلا ... لما فداه بأعظم القربان
هو دين يعقوب النبي ويونس ... وكلاهما في الله مبتليان
هو دين داود الخليفة وابنه ... وبه أذل له ملوك الجان
هو دين يحيى مع أبيه وأمه ... نعم الصبي وحبذا الشيخان
وله دعا عيسى بن مريم قومه ... لم يدعهم لعبادة الصلبان
والله أنطقه صبيا بالهدى ... في المهد ثم سما على الصبيان
وكمال دين الله شرع محمد ... صلى عليه منزل القرآن
• Addinin musulunci shi ne mafi tsafta kuma mafi dacewa da cancanta ga bayi a matsayin hanyar bauta;
Allah (S.W.T) ya faɗa mana a cikin Alƙur'ani maigirma:
إِنَّ الدِّينَ عِندَ اللّهِ الإِسْلاَمُ
Kaɗai addini a gurin Allah shi ne MUSULUNCI
(Āli Imrān: 19)
Ya kuma faɗa mana bai yarjewa bayinsa su je gurinsa ranar alƙiyama ba, sai suna musulmi, waɗanda suka bi addinin Musulunci:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسْلِمُونَ
(Āli Imrān: 102)
Ya kuma faɗa mana bai yarda mu yi wani addinin ba idan ba musulunci ba:
ٱلْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِى وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلْإِسْلَٰمَ دِينًا ۚ
(Al-Mā'idah: 3)
Da waɗannan ƙa'idojin da muka samu a cikin Alƙur'ani maigirma ne ake gane musulmi da kafiri! Da su ne muka ja muka tsaya kai da fata wajen tunkuɗe yiwuwar shiga aljanna ga arniyar nan ta Birtaniya (Elizabeth II) da ta kwanta dama kwanakin baya.
06|| ME YA SA MUKE AUNA KIMIYYA DA SIKELIN ADDININ MUSULUNCI?
Zan ci gaba in sha Allah a karo na gaba, gudun tsawaitawa in sha Allah.
#KimiyyaDaAddini #Falsafa
#AddiniDaRayuwa
(C) Adam Sharada
October 20, 2022
Comments
Post a Comment