SHIN ƘA'IDOJIN PHYSICS ZA SU IYA BAYANIN SAMUWAR DUNIYA BA TARE DA BUƘATUWA ZUWA GA ALLAH (S.W.T) BA?
(Tsaftace Kimiyyar Physics daga Kafircin Stephen Hawking)
00|| KASHI NA FARKO: SHIMFIƊA
Shi dama Hawking ya gama ginawa zuciyarsa cewa babu Allah! Shi ya sa ya ƙarar da rayuwarsa wajen kwashe-kwashen karikicen da yake ganin za su taimaka masa wajen tallata ILHADI (kore samuwar Allah).
01|| KASHI NA BIYU: MAGANAR STEPHEN HAWKING
A wata hira da wata jarida mai suna ABC NEWS ranar 07-09-2010 game da halittar duniya, Hawking ya ce:
"The laws of physics can explain the universe without the need for a creator,"
Ma'ana: Ƙa'idojin kimiyyar Physics za su iya bayanin samuwar duniya, ba tare da an buƙaci wani mahalicci (Allah) ba!
Wannan magana kamar yadda muka saba, za mu koma mu nazarce ta a ma'aunin ƙa'idojin kimiyyar Physics, kuma za mu fahimci ɓacin wannan magana, da rashin dacewarta da ilimin kimiyyar Physics ɗin in sha Allah.
02|| KASHI NA UKU: NAZARIN MAGANAR HAWKING A MAHANGAR KIMIYYAR PHYSICS
Idan muka koma ƙa'idojin da suka kafa kimiyyar Physics, za mu samu suna ƙaryata abin da Stephen Hawking yake da'awa. Za mu kawo misalai guda 3 gudun tsawaitawa:
(A)- Newtonian Mechanics: Wannan nazariyyar ta ginu akan amfani da ƙa'idojin motsi (Newton's Laws of Motion) da Malam Isaac Newton (1643-1727) ya binciko a shekarar 1686, waɗanda suke tabbatar da nagartar kimiyyar tazara (distance), lokaci (time) da kuma adadi (mass). A cikin waɗannan ƙa'idojin guda 3, ƙa'ida ta 2 tana cewa:
"A body remains at rest, or in motion at a constant speed in a straight line, unless acted upon by a force"
Ma'ana: Duk wani jiki da yake tsaye da duk wani jiki da yake motsi, ba sa sauyawa daga matsayinsu sai an samu wani ƙarfi na musamman da ya yi aiki akansu.
A Physics idan aka ce "body" ana nufin duk wani abu da yake da adadi (mass) wanda za a iya aunawa. An ciro wannan ma'anar daga ƙa'idar nan sananniya da take cewa: "ρ = m /V". Wannan jikin zai iya zama daskararre (solid), ko ruwa-ruwa (liquid) ko kuma iska (gas). To dukkanninsu malaman Physics da suka kai matakin ijtihadi a fagen sun ce ba sa sauyawa sai an samu wani dalili!
Da mu da muka yarda da samuwar Allah (S.W.T) da su Hawking da suke musanta samuwarSa mun yarda "motion (motsi)" ba haka kawai yake faruwa dole sai da dalili! To kuwa, kimiyyar Physics ba za ta karɓi a ce wannan duniyar (universe) ta faru haka kurum ba tare da dalili ba!
Don haka, ba ta yadda za a yi Laws of Physics su iya yin cikakken bayani game da wannan duniyar ba tare da buƙatar Allah (S.W.T) ba!
(B)- Big Bang (Babban Amo): Stephen Hawking ya yarda duniya (univer) ta samu daga faruwar babban amo (amma ni ban yarda ba, na yi rubutu mai tsayi kan haka!). Idan da za mu sallama faruwar wannan lamari na babban amo to shi ma yana ƙaryata su Stephen Hawking ne ta kowace nahiya.
Domin abin da malaman Physics suka ambata game da faruwar babban amo shi ne; wani abu ne a dunƙule a tsaye a guri guda, sai aka samu wani ƙarfi (force) ya zo ya buge shi sai ya tarwatse ya fashe har da yin ƙara (a ƙaryarsu), sai duniya da abin da ke cikinta suka samu. Kenan akwai abin da ya sa Big Bang ya samu, ba haka kawai ya farar da kansa da kansa ba! Kenan daga nan za mu ƙara fahimtar cewa: "nothing is happening from nothing", ba abin da yake faruwa haka kurum, wadda kuma ita ce tukunyar da ilimin Physics yake kai-kawo a cikinta. Su malaman Physics da yake galibinsu maguzawan Girka ne ba su iya gano wannan abun ba har zuwa yau! Shi ya sa suke kiransa "unknwon force", amma dai a ittifaƙinsu ba haka kawai duniya ta samu ba!
Wannan ya isa ya ƙaryata mai cewa, wai Physics zai iya bayanin duniya ba tare da buƙatar Allah (S.W.T) ba!
(C)- Matter: Shi ne duk abin da yake da nauyi (weight), adadi (mass) kuma zai iya cin guri (occupy space). Wannan abin zai iya zama solid, liquid ko gas. Nazarin tushen inda "matter" ta samo asali wani abu ne da ya gajiyar da kafatanin malamanmu na Physics. Iyakar abin da aka gano shi ne; matter (ta komai) ta ƙunshi atom (za mu tattauna akansa nan gaba). Shi kuma atom ya ƙunshi abubuwa guda 3: electron, proton da neutron. Su kuma proton da neutron sun samu daga wani abu da ake kira "quark", shi kuma quark ya samu daga wani da ake kira "hadron"! Iya nan ne binciken malaman Physics ya tiƙe, ba su san haƙiƙar inda "hadron" ɗin ya samo asali ba🤣🤣
Wajen bayanin asalin tushen matter dole ana buƙatar dalili, domin ba haka kurum matter ta samu ba! A nan ma Physics yana buƙatar Allah (S.W.T) domin sanin tushen komai da komai na cikin kaunu. Idan Physics ya gudana a haka, ba tare da sanin ainihin tushen "matter" ba, to allon rantsuwarsa ya karye. Duk manyan ɓangarorin Physics irin su Quantum Mechanics, Nuclear Physics, Medical Physics, Environmental Physics, Astrophysics, Geophysics, Biophysics, Acoustic da sauransu sai zama tamkar miyar da ba gishiri ba magi a cikinta! Wannan kuwa ba zai yiwu ba!
Wannan ma dalili ne game da yadda Physics yake zama nakasasshe idan ba a mayar da lamarinsa zuwa ga Allah (S.W.T) ba!
A mahangar addinin musulunci kuwa mun sha ambaton dalilai daga cikin Alƙur'ani maigirma wanda Allah (S.W.T) ya saukarwa Annabi Muhammad (S.A.W) gane da tabbatar da samuwar Allah (S.W.T). Ba buƙatar mu maimaita kawo su.
04|| KASHI NA HUƊU: KAMMALAWA
Allah (S.W.T) ya samu da dalillai na kimiyya, Physics ta kowace nahiya yana tabbatar da samuwar Allah, haka sauran fannonin kimiyya musamman Mathematics, Geography, Astronomy, Biology da sauransu.
Ya ishi duk musulmi dalili a hannunsa faɗin Allah (S.W.T) cewa:
إِنَّ فِى خَلْقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱخْتِلَٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ لَءَايَٰتٍۢ لِّأُوْلِى ٱلْأَلْبَٰبِ
Lallai a cikin halittar sammai da ƙasa da sassaɓawar dare da yini, akwai ayoyi ga ma'abota zuzzurfan hankali (malamai da ma'abota ilimi tsaftatacce).
(Āli Imrān: 190)
#KimiyyaDaAddini
#AdamSharada
#StephenHawking
© Adam Sharada
9 Almuharram, 1444
7 August, 2022
Comments
Post a Comment