HOTON SARARIN SAMANIYA DA AKA ƊAKKO A AMURKA TSAKANIN ALƘUR'ANI DA KIMIYYAR PHYSICS
(Dalilan Kimiyyar Physics da ke Tabbatar da Samuwar Allah)
#KimiyyaDaAddini
00|| MATASHIYA
Allah (S.W.T) a cikin Alƙur'ani maigirma ya yi alƙawarin sai ya tabbatarwa da kowa da kowa ɗayantakar samuwarSa:
سَنُرِيهِمْ ءَايَٰتِنَا فِى ٱلْءَافَاقِ وَفِىٓ أَنفُسِهِمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ ۗ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ شَهِيدٌ
(Fussilat: 53)
Ya kuma yi alƙawarin hatta a karan kanmu mu mutane a cikin halittunSa sai ya tabbatar mana da buwayarSa da kaɗaitakarSa (S.W.T):
وَفِىٓ أَنفُسِكُمْ ۚ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
(Azzāriyāt: 21)
Wannan alƙawari ne ya sanya tun bayan aiko Annabi (S.A.W) da saƙon Alƙur'ani kullum duniya ke ganin dalilai na hankali da suke tabbatar da wancan alƙawari da Alƙur'ani ya zo da shi!
A wannan ɗan tsukun kwanakin hukumar binciken sararin samaniya ta ƙasar Amurka (NASA) ta gano wani sabon al'amari, wanda yake tabbatar da wancan alƙawari na Allah (S.W.T) da Alƙur'ani ya faɗa mana sama da shekaru 1400.
01|| SARARIN SAMANIYA A KIMIYYAR PHYSICS
A gurin malamanmu na Physics (Astronomers/Astrophysicists) sararin samaniya shi ne: wani guri na waje (outer space) da ke kishiyantar duniyar ƙasa (Earth). Wannan gurin (space) ya ƙunshi gurare (halittu da duniyoyi) da dama (outer space) da ke kishiyantar ƙasa, da kuma yanayin iska (atmosphere) wanda ya bambanta da na ƙasa.
02|| SARARIN SAMANIYA A CIKIN ALƘUR'ANI
Tun gabanin malaman Physics da shi kanshi ilimin kimiyyar Physics su samu, Alƙur'ani maigirma ya yi bayanai masu yawan gaske game da sama (sky) da irin abubuwan da Allah (S.W.T) ya sanya a cikinta. Duk wani bincike da malamanmu yau suke zaton sun yi bajintar ganowa game da sararin samaniya (outer space) in dai ingantacce ne, to Alƙur'ani maigirma ne ya fara tabbatar da shi sama da shekaru 1400. Kamar yadda duk wata siffa da malaman namu ke iya siffanta sararin samaniya da shi, to ba makawa Alƙur'ani ne ya fara kawo wannan siffar. Alal misali:
• Halittar sararin samaniya da kafa ta kamar rumfa ba tare da wani ginshiƙi (pillar) da yake iya riƙe ta daga faɗuwa ba. Allah (S.W.T) ya tabbatar mana da wannan a cikin Alƙur'ani maigirma
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيْرِ عَمَدٍۢ تَرَوْنَهَا ۖ وَأَلْقَىٰ فِى ٱلْأَرْضِ رَوَٰسِىَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٍۢ ۚ وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍۢ كَرِيمٍ
(Luƙmān: 10)
• Saukar da ruwan sama daga sararin samaniya
وَهُوَ ٱلَّذِىٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجْنَا بِهِۦ نَبَاتَ كُلِّ شَىْءٍۢ فَأَخْرَجْنَا مِنْهُ خَضِرًا نُّخْرِجُ مِنْهُ حَبًّا مُّتَرَاكِبًا وَمِنَ ٱلنَّخْلِ مِن طَلْعِهَا قِنْوَانٌ دَانِيَةٌ وَجَنَّٰتٍۢ مِّنْ أَعْنَابٍۢ وَٱلزَّيْتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُشْتَبِهًا وَغَيْرَ مُتَشَٰبِهٍ ۗ ٱنظُرُوٓاْ إِلَىٰ ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثْمَرَ وَيَنْعِهِۦٓ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكُمْ لَءَايَٰتٍۢ لِّقَوْمٍۢ يُؤْمِنُونَ
(Al-An'ām: 99)
In sha Allah za mu faɗaɗa idan mun zo rubutu game da duniyoyin da ke cikin sararin samaniya nan gaba kaɗan.
03|| NAZARIN HOTON SARARIN SAMANIYA DA AKA ƊAKKO A AMURKA
Ranar Litinin (11 July, 2022) wata na'urar ɗaukar hoto mai nisan zango (Telescope🔭) mai suna James Webb Space Telescope, wadda hukumar binciken sararin samaniya (outer space) na ƙasar Amurka da ake kira National Aeronautics and Space Administration (NASA), tare da haɗin gwiwar hukumar kula da sararin samaniya ta yankin Turai European Space Agency (ESA) da takwararta ta ƙasar Kanada Canadian Space Agency (CSA); ya samu nasarar ɗakko hoto mafi ban ƙaye na sararin samaniya, wadda ta sha ado (beza) da wasu irin nau'ikan kalolin taurari masu jan hankali da sanya nishaɗi a zukatan malaman Physics da ma sauran gama-garin mutane.
Ita kanta hukumar NASA da take jagorantar binciken sararin samaniya lamarin ya yi matuƙar ɗaukar hankalinta! A sakin layi na farko na bayanin da hukumar ta rabawa manema labarai a duniya, kuma ta wallafa a shafinta, suna cewa:
“Today, we present humanity with a groundbreaking new view of the cosmos from the James Webb Space Telescope – a view the world has never seen before,” said NASA Administrator Bill Nelson. “These images, including the deepest infrared view of our universe that has ever been taken, show us how Webb will help to uncover the answers to questions we don’t even yet know to ask; questions that will help us better understand our universe and humanity’s place within it."
Ma'ana: A yau muke gabatarwa da duniya wani sabon labari game da duniyar kaunu, wanda na'urar ɗaukar hoton sararin samaniya ta James Webb ta ɗakko. Wannan hoton duniya ba ta taɓa ganin irinsa ba gabanin wannan lokaci!........
A ɗan tsukun nan masana kimiyyar sararin samaniya da ɗaukacin malaman Physics da ma sauran ƴan boko ba abin da suke zance sai wannan lamari, wannan bincike da suke kallo a matsayin wani abu da ba a taɓa ganinsa ko jin labarinsa ba a tarihin duniya.
Shugaban Amurka Joe Biden tsabagen zumuɗin daɗi cewa yake: "These images are going to remind the world that America can do big things. And remind American people especially children that nothing is beyond our capacity. We can see possibilities no one has ever seen before! We can go places no one has ever gone before...."
Mu kuma Alhamdulillah, da yake Allah ya azurta mu da Alƙur'ani maigirma wanda malamin duniya Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da shi, ba irin wannan kallon na siyasa, ko bajintar malaman kimiyyar hukumar NASA muke yiwa lamarin ba.
04|| YADDA ALƘUR'ANI MAIGIRMA YA TABBATAR DA WANNAN BINCIKE NA HUKUMAR NASA
ALLAH (S.W.T) wanda shi ne ya halicci sama da ƙasa da koma da komai a cikin kwanaki 6 (Al-A'arāf: 54), ya tabbatar mana da cewa shi ne ya ƙawata halittar sama a cikin ayoyin Alkur'ani da dama. Daga cikinsu:
وَلَقَدْ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِمَصَٰبِيحَ وَجَعَلْنَٰهَا رُجُومًا لِّلشَّيَٰطِينِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ
Lallai mun ƙawata halittar sama da wasu fitilu (taurari), kuma muka sanya ta mai jifan shaiɗanu...(Almulk: 5)
Zumuɗi da ruɗewar da malaman Physics suka yi shi ne yadda taurara suka yiwa sararin samaniya wani irin ƙayataccen ado na fitilun taurari, masu ƙyalƙyali da walwali. Ashe tun sama da shekaru 1400 an faɗawa Annabi Muhammad (S.A.W) wannan siffar a cikin Alƙur'ani maigirma! A cikin sahara mai faƙo, ba wutar lantarki ballantana a samar da wata na'urar Telescope, babu fasahar ƙere-ƙeren zamani ballantana a samar da jiragen tafiya sararin samaniya, ba wani mahaluƙi da ya wanzu da ya san wani abu Physics da kowace irin ma'ana!
Wannan dalili ne da ya kamata duk wani mulhidi mai inkarin samuwar Allah, ya zauna ya nazarce shi a nutse, ya auna da hankalinsa da ilimin Falsafar (Metaphysics) tasa, ya gani shin lafiyayyen hankali zai karɓa ko kuwa!
A wata ayar kuma Allah (S.W.T) yana cewa
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِزِينَةٍ ٱلْكَوَاكِبِ
Lallai mun ƙawata halittar saman duniya da ado na taurari (Assāfāt: 6)
Mu ɗan koma Physics kaɗan a wannan gaɓar:
• Mun sha nanatawa a baya cewa: "everything happens for a reason and that reason is usually Physics" Su dai waɗannan taurarin da suka yiwa samaniya ƙawa ta haske mai burgewa ba haka kurum suka faru ba, dolen-dole a samu wanda ya samar da su! Malaman kimiyya duk ba su sani ba, Alƙur'ani ya ce wanda ya samar da su shi ne ALLAH (S.W.T)! Kuma dai yau ga shi ƴar manuniya ta nunawa duniya tabbacin wannan magana, idan ba a gamsu da na Alƙur'ani ba.
Duk abin da ba a san dalilin faruwarsa ba, sunansa "undefine" abin da hankula masu lafiya ma ba za su karɓa ba!
• Shi haske "light" wanda yake fita daga jikin taurarin nan (electromagnetic radiation) yana haska sararin samaniya (outer space) dole shi ma yana da tushe (source)! Allah (S.W.T) wanda ya halicci waɗannan halittu shi ne yake samar musu da hasken daga abin da ya barwa kansa sani! Idan ya ce ya daina ba su hasken DUK DUNIYA ba ɗan da ya isa ya ba su, kamar yadda yanzu da suke hasken ba ɗan da ya isa ya dakatar da hasken daga samuwa!
Mulhidai suna cewa haka kurum ya samu, wannan tunanin nasu zallar sanyin ƙwaƙwalwa ne irin na tuburarrun maguzawa🤣
Ku ce musu ƙwan lantarki (Electric Bulb) da suke kunnawa a ɗakunansu idan za su karanta turancin banzar da yake burge su a ilimin falsafa, me yake sanyawa ya kawo haske? Me ya sa ba za su iya kwance ƙwan daga gindinsa su ajiye shi kusa da su ya kawo musu hasken haka kurum ba?
• A yaren kimiyyar Lissafi (Mathematics) suna cewa: "function is undefined when the denominator is equal to zero" wato duk abin da idan aka koma tushensa zai zama babu (zero), to wannan abun babu shi kawai!
Anan na fahimci wani abu a Physics game da wannan sabon binciken da NASA take ganin ta yi; tunda dai su kafirai (mulhidai da mushirikan) da ƴan daɗi arna sun yarda an gano yadda taurari suka haska sararin samaniya da wata kwalliya ta ado, to kenan dole waɗannan taurarin akwai abin da ya samar da su! Kenan dole ma a ce akwai daga inda ake samar musu da wannan hasken nasu! Wannan tushen shi ne zai zama turken da nazariyyar lamarin za ta koma kansa, a gwari-gwari za mu ce:
Let, "a" ta zama kwalliyar haske da taurari suke yiwa sararin samaniya, and "b" ta zama inda taurarin suka samo haskensu. Wajen gano wani abu da ke danganta "a" da "b", sai dai a ce
f(x) = a/b,
idan "b" ta zama sifili/babu (if b= 0), to fa shikenan wannan lamarin ya lalace a yaren lissafi. Saboda lambar ƙasa (denominator) idan ta zama 0 a lisssfi, to wannan lissafin sunansa hauka in ji malaman lissafi na duk duniya.
Kamar haka ne, idan wani ɗan gaba-gaɗi ya musanta jingina halittar taurari da inda suke samo haskensu zuwa ga Allah (S.W.T), to sunan tunaninsa hauka da naɗi!
05|| ƊAURAYA
Alƙur'ani maigirma littafi ne na shiriya a cikin dukkan komai, a cikinsa akwai cikakken fayyataccen bayani game da komai da komai:
وَيَوْمَ نَبْعَثُ فِى كُلِّ أُمَّةٍۢ شَهِيدًا عَلَيْهِم مِّنْ أَنفُسِهِمْ ۖ وَجِئْنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ ۚ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَٰبَ تِبْيَٰنًا لِّكُلِّ شَىْءٍۢ وَهُدًى وَرَحْمَةً وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
(Annahli: 89)
Duk wata nazariyya da ta ci karo da Alƙur'ani, idan aka bi diddiginta a kimiyyance ma za a same ta ba ta da inganci!
Allah ya ɗaukaka musulunci. Allah ya shiryar da waɗanda suka ɓata daga tafarkin Annabi Muhammad (S.A.W)
A LURA: Na sanya taƙaitaccen bayanin kowane hoto a ƙarƙashinsa, don taimakawa musamman ɗaliban kimiyya gane zaurancen da ake yi!
𝔸𝕕𝕒𝕞 𝕊𝕙𝕒𝕣𝕒𝕕𝕒
14 Zulhijjah, 1443/ 13 July, 2022
Comments
Post a Comment