"DARK MATTER" DA GAZAWAR MALAMAN PHYSICS WAJEN GANE GIRMAN ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI

00• GABATARWA
A ɗabi'ar malaman kimiyya musamman a fannonin da suka shafi duniyar da ake gani (Natural Science) irin su Physics, Geography, Biology da Chemistry: duk abin da bincikensu ya kasa gano haƙiƙaninsa ko tushensa, sai su ce masa "nature", wato sauran halittu da abubuwa masu rai da marasa rai waɗanda ba ɗan adam ne ya same su ba, kawai sun samu ne gaba-gaɗi. Saboda tsabar sanyin da ke damun ƙwaƙwalensu na rashin tauhidi.

Mu kuma musulmi da muka rabauta da shiriyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da mun ga irin wannan bankaurar, sai wallensu da ɓacin tunanin nasu ya bayyana gare mu, saboda muna da Alƙur'ani maigirma, wanda a cikinsa Allah Subhanahu Wata'ala ya sanar da mu cewa ya halicci kowa da komai, wanda aka sani da wanda ma da babu wanda ya sani ko ya isa ya sani.

ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَىْءٍۢ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ وَكِيلٌ
ALLAH shi ne ya halicci dukkan komai, kuma shi ne mai kula da dukkan komai.
(Azzumar: 62)

01• MENENE MATTER?
Yana da kyau mu fara sanin "MATTER" tukun, domin sauƙaƙa fahimtar "Dark Matter": A yaren kimiyyar Physics ana nufin

"substance made up of various types of particles that occupies physical space and has inertia"
Ma'ana: abin da ya samu daga haɗuwar wasu ƙananun abubuwa, wanda zai ci gurin da ake iya gani (in an aza shi a wani bigire, zai rufe bigiren), kuma yake iya hawa ƙa'idar motsi ta 1 ta Newton (Newton's 1st Law of Motion).

Wato duk wani abu da ya ke da adadi (weight) da adadi sananne a cikin ma'aunin kimiyya (mass), wanda kuma in ya aka aza shi a wani bigire zai rufe guri, sannan Law of Inertia wadda take magana akan sauya hanyar motsin mata da motsin nata, za ta iya aiki akansa, shi ne matter. Da wannan ta'arifin ƴan Physics ke cewa komai a duniya Physics ne.

Matter nau'i 3 ce a asali; Solid (Sandararru), Liquid (Ruwa-ruwa) da Gas (Iska). Idan an ɗan nutsa kuma za a ci karo da wasu kamar 
Solids, Liquids, Gases, 

I- Ionized Plasma
II- Quark-Gluon Plasma
III- Bose-Einstein Condensate
IV- Fermionic Condensate

NOTE: In sha su ma akwai abin da na tanada akansu nan gaba, zamu tattauna su don warware wasu shubuhohin mulhidai da ƴan daɗi arna a ƙarƙashinsu.

DAJIYA: Wannan definition ɗin na "matter" kaɗai ya isa ya tabbatar mana kimiyyar CHEMISTRY kacokan reshe ce daga bishiyar Physics🤸🤣 Ba wai da ƙafarta take tsaye ba. Ta'arifin da Chemistry ya bawa matter "anything that has weight, mass and can occupy space" kaɗai hujja ne akansu🤣🤣

02• MENENE DARK MATTER?
Dark Matter na nufin wani yanki na duniya (matter) wanda ba su da haske nasu na kansu kuma haske ba ya iya haska su a gansu, waɗanda malaman Physics na sama-jannati (Astrophysics/Astronomy) suka kaso gano haƙiƙaninsu. 

Dark Matter suna da matakai guda 2:

I- Baryonic Dark Matter: sun samo asali daga wani sinadari mai suna Baryon (Particle Physics), wanda shi ya samar da ƙwayar zarra (subatomic particles). Ita wannan Dark Matter ɗin ba ta fi kaso 5% a cikin duniya.

II- Nonbaryonic Dark Matter: ita kuma kishiyar Baryonic ce, ita ce kusan kimanin 85% na matter ɗin da ke duniya (universe).

Dukkanninsu dai malaman Physics har zuwa yau ba su san menene su ba, saboda wannan "Dark" ɗin ya sa ba sa iya ganinsu ko da ido ko da na'urorin kimiyya. Kuma sun ce su ne kusan kimanin kaso 85-90% na matter da ke cikin universe. Suna ta bincike da aune-aune amma sun kasa kaiwa ga gano haƙiƙar Dark Matter.

Marubuciyar nan Amerikiya Maria Dahvana Headley tana da wata shaharriyar magana a cikin littafinta "Magonia" game da Dark Matter:

"I'm dark matter. The universe inside of me is full of something, and science can't even shine a light on it. I feel like I'm mostly made of mysteries."

A nan za mu fahimci sakarcin mulhidai (masu inkarin samuwar Allah) da suke musanta samuwarSa saboda wai tunani irin nasu su bai iya kirdadon siffar zati (Imagination), kuma dalilansu na Falsafar Diddigi (Metaphysics) wai ba su iya tabbatar musu da samuwarSa ba. Amma kuma suke iya gasgata irin wannan kimiyyar wadda har zuwa yau an kasa gano haƙiƙaninta meye a cikinta.

03• DARK MATTER A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI
Mu musulmi Allah (S.W.T) ya faɗa mana a cikin Alƙur'ani maigirma cewa ya halicci abubuwan da babu wani mutum da ya sani ko ya isa ya sani:

وَيَخْلُقُ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Kuma ya halicci abubuwan da ba ku sani ba.
(Annahli: 8)

Sannan ya faɗa mana ilimin da ɗan adam zai yi wani abu ne ɗan ƙalilan da bai taka kara ya karya ba:

 وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ إِلَّا قَلِيلًا
.......Kuma ba komai aka ba ku na ILIMI sai ɗan kaɗan
(Al-Isrā'i: 85)

Babbar matsalar da suka samu shi ne jahiltar ADDININ MUSULUNCI, addinin da Allah (S.W.T) ya aiko dukkanin Annabawa da Manzanni don su karantar da duniya. Shi ya sa sai su musanta abin da yake bayyane a gabansu, amma kafirci ya makantar da su, sannan kuma su tabbatar da abin da ba sa iya gani hankali lafiyayye ma ba zai karɓe shi ba.

04• KAMMALAWA
Dark Matter tana gwada gazawar ɗan adam wajen gane haƙiƙanin abin da Allah (S.W.T) ya bari a ɓoye, ya ƙi ya bayyana shi ga halittunsa. Kuma duk wani yunƙuri da ɗan adam zai yi na gano gaibu to ba zai iya ba, saboda buwaya da ƙarfin ƙudirar Allah mahaliccin kowa da komai, mai sarrafa faruwar komai da komai ta shallake tunani da ilimi ko binciken ɗan adam mai nakasa da tawaya.

Duk wani abu na kimiyya da ya shafi gaibu to ba zai fita daga da'irar ƙa'idojin da Alƙur'ani maigirma ya shimfiɗa ba. Ɗaliban kimiyya da suke karantawa bisa ma'aunin Alƙur'ani da Sunnah su kaɗai ne suke saurin game hikimomin Allah Subhanahu wata'ala game da nazariyyar da malaman kimiyya suka kasa gane tushenta ko haƙiƙanin abin da ta ƙunsa.

Allah (S.W.T) yana faɗa mana a cikin Alƙur'ani maigirma:

قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Ka ce musu babu wanda ya san abin da ke cikin sammai da ƙasa na GAIBU sai ALLAH......
(Annamli: 65)

Kuma ya ce mana

عَٰلِمُ ٱلْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَىٰ غَيْبِهِۦٓ أَحَدًا
Shi ne masanin GAIBU, wanda ba ya bayyana gaibunsa ga kowa!
(Aljinn: 26)

#KimiyyaDaAddini #DarkMatter 
#AdamSharada #Physics

© Adam Sharada
     13 Muharram, 1444
     11 August, 2022

Comments