"DARK ENERGY" DA GAZAWAR MALAMAN PHYSICS WAJEN GANE GIRMAN ALLAH (S.W.T)
(Tsaftatacce Kimiyyar Physics daga Maguzancin Girkawa)
0.0• MATASHIYA
A shekarar 1916 shahararren Bajamushen-Ba'amurken malamin Physics ɗin nan da ya rayu a ƙarni na 20 Sir Albert Einstein ya gano wata nazariyya game da dangantakar motsi wadda ya sanyawa suna "General Theory of Relativity" (قانون النصبية) wadda a cikin bayanin wannan nazariyya ne malamin ya bijirowa da duniyar kimiyyar Physics mas'alar; shin duniya (universe) tana motsi (dynamic) ne ko kuwa a tsaye take (static)?
Daga nan ne wani ƙwararren Ba'amurken malamin Physics Malam Edwin Hubble (1889-1953) ya tabbatar da duniya tana motsi a wani bincike da ya wallafa a shekarar 1929. Daga nan ne malaman Physics da dangoginsu (Cosmologists, Astronomers, Astrophysicists) suka fara binciken dalilin da yake sanyawa duniya ta motsa ko kuma ta tale (expanding).
Daga nan ne suka gina nazariyyar "Dark Energy", wanda ya kai su ga shan baƙar wahala saboda rashin rabauta da HASKEN TAUHIDI, suka kasa gano haƙiƙanin abin da yake faruwa! Suka koma karime-karime da make-make.
NOTE: In sha Allah akwai topic na musamman da za mu tattauna game da mas'alar "Talewar Duniya Tsakanin Kimiyyar Physics da Alƙur'ani", nan gaba.
0.1• MENENE ENERGY?
Yana da kyau mu ɗan yi gajeriyar shimfiɗa game da "Energy" don sauƙaƙa mana fahimtar "Dark Energy" da muke magana akai a wannan rubutu.
A fassarar (isɗilahin) kimiyyar Physics "energy" na nufin: ikon aikata wani abu. Wato dama ta ƙarfi da wani abu kowane iri ne (Solid, Liquid ko Gas) ke da ita wajen aikata wani aiki, wannan damar ita ake kira "energy".
A Ilimin Physics wannan iko/dama (energy) ta kasu zuwa ajujuwa mabanbanta, amma duka in an dunƙule su suna komawa zuwa ga turke guda 2 ne:
I- Potential Energy: Shi ne nau'in energy (ƙarfi/ikon) da yake ajiye a cikin jiki irin na kimiyya (Solid, Liquid da Gas).
Irin wannan energy ɗin shi ne kamar:
A- Mechanical Energy
B- Gravitational Energy
C- Chemical Energy
D- Nuclear Energy
II- Kinetic Energy: shi ne nau'in energy ɗin da yake motsa abubuwan da idanu ba su da ikon ganin yanayin motsinsu kamar tafiyar ruwa ta kimiyya (wave), motsin ƙananun sinadarai kamar atoms da molecules, motsin ƴaƴan ƙwayar zarra (electrons) da makamantansu.
Irin wannan energy ɗin shi ne kamar:
A- Thermal Energy
B- Motion Energy
C- Sound Energy
D- Electrical Energy
E- Radiant Energy
A nan gaɓar ma ya kamata mu tattauna game da "Law of Conservation of Energy" mu warware wata shubuha ta kafirci da ake ginawa akan halittar "Energy". Amma za mu jinkirta sai a wani karon in sha Allah, gudun faɗaɗawa.
0.2• MENENE DARK ENERGY?
A yaren kimiyyar Physics "Dark Energy" shi ne nau'in energy (ƙarfi) wanda yake sanyawa duniya ta motsa ko ta tale ta ƙara girma, daga girmanta na asali. Malaman namu na Physics suna cewa: shi wannan "Dark Energy" ɗin shi ne kusan kaso 70% na energy ɗin da yake sanyawa duniya ta motsa ta ƙara girma. Wato dai iya abin da suka sani a zahiri da ƙurewar bincikensu na adadin ƙarfin da yake aikin motsa duniya bai fi kaso 30% ba, ragowar kawai sun yarda akwai shi amma ba su san shi ba, kuma sun gagara gano shi har zuwa yau!
Sun kuma ce dark energy ya ƙunshi wasu muhimman ɓangarori guda 2:
I- Cosmological Constant
II- Scalar Field/Energy Density
Malaman Physics (Astronomers da Astrophysicists) dai har wa yau sun haɗu kan cewa; har yanzu ba wanda ya san haƙiƙanin yanayin dark energy, kawai dai sun san shi ne sababbin/dalilin da yake sanyawa wannan duniyar ta ƙara girma, ba wai haka kurum take talewa tana ƙara girman ba! Kasa gano taƙamaimai ɗin meye shi, ta sa kawai suka rufe idanu suka zaɓar masa suna "Dark Energy" wato "Baƙin Ƙarfi" ƙarfin da ba kawai idanun zahiri ba, har idanu irin na kimiyyar Physics (na baɗini) sun kasa gano meye shi, ballantana su iya ganinsa.
0.3• DARK ENERGY A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI
Kamar yadda muka sha ambata a baya, malaman Physics sukan yi tufka su warware ta da kansu musamman idan suka nufaci kutsawa mas'alolin da suka shafi gaibu. saboda asalin manyan malamansu da suka fara aza nazarin kimiyyar Physics ɗin daga maguzawan Girka (Ancient Greek Philosophers) sai miyagun ƴan falsafa masu raba ƙafa game da samuwar Allah tsakanin korewa da tabbarwa (Agnosticism), su ba su ƙaryata ba su ba su gasgata ba. Mu kuma musulmi da Allah (S.W.T) ya albarkace mu da shiriyar imani, Annabinmu shugabanmu Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya zo mana da Alƙur'ani da Sunnah waɗanda suka yi mana gamsasshen bayani kan duk wani abu da yake da alaƙa da imani, don togace mu daga faɗawa ramin shirka da kafirci.
Allah (S.W.T) ya gaya mana a cikin Alƙur'ani maigirma cewa:
قُلِ ٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثُواْ ۖ لَهُۥ غَيْبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ أَبْصِرْ بِهِۦ وَأَسْمِعْ ۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِىٍّۢ وَلَا يُشْرِكُ فِى حُكْمِهِۦٓ أَحَدًا
(Alkahfi: 26)
A cikin ayar Ya ce (S.W.T)
لَهُۥ غَيْبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ
Shi ne kaɗai ya san ɓoyayyen abin da ke cikin sammai da ƙasa
Kuma ya faɗa mana:
قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Ka ce musu ba wanda ya san GAIBUN (abin da yake ɓoye) na sammai da ƙasa sai Allah.....
(Annamli: 65)
A wata ayar kuma Allah (S.W.T) ya ce:
وَعِندَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لَا يَعْلَمُهَا إِلَّا هُوَ ۚ
Allah (S.W.T) ne kaɗai ya san abin da ke ɓoye (GAIBU) babu wanda ya san su sai Shi....
(Al-An'ām: 59)
Sanin wannan da ƙudirce wannan game da buwayar Allah (S.W.T) a cikin iliminsa da ƙarfin ikonsa shi ne abin da yake tsaftace zukata daga dattin shirka da mugun tunani irin na maguzawan Girkawa da dangoginsu ma'abota falsafa. Da a ce malaman Physics sun san ALLAH wanda Shi ne Mahaliccin komai da kowa, wanda yake da ikon gudanar da komai da kowa, wanda isarSa da iliminSa suka kewaye game da komai, da ba su riƙa wannan kwane-kwanen da zille-zillen ba.
Idan muka koma ƙa'idojin da suka kafa kimiyyar Physics:
•Akwai abubuwa da dama irin su dark energy da PHYSICS bai iya gano haƙiƙanin siffarsu (dimension) ko alamominsu ba, amma kuma ya yarda da samuwarsu. Wannan na nufin don mulhidai ba su iya gane alamomin samuwar Allah (S.W.T) ba, hakan ba ya nufin babu Allah!
• Physics kacokan ya gudana akan cewa "everything happens for a reason", dark energy ma ya tabbatar ba haka kawai wannan duniyar ke motsawa ba, akwai mai motsa ta da ba su iya sani ba. A gurinmu Allahu Subhanahu Wata'ala Shi ne yake wannan aikin a cikin gaibunsa.
Ƙarfin mulki da buwayar Allah (S.W.T) wanda ya halicci komai da komai, shi ne dai mai ikon tasarrufin komai da komai, a cikin komai ɗin har da motsawar duniya da malamanmu na Physics suka kasa gane daga ina ne, suka maƙala wata cuwa-cuwa wai "dark energy".
Allah maɗaukakin sarki ya faɗa mana:
ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَىْءٍۢ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ وَكِيلٌ
Allah Shi ne Ya halicci dukkan komai, kuma Shi ne Wakili (mai kulawa) da dukkan komai.
(Azzumar: 62)
Haka dai a wata ayar Ya faɗa mana ƘARARA cewa Shi ne ya halicci dukkan komai kuma Shi ne ya ke hukunta faruwar dukkan komai, a cikin dukkan komai ɗin nan har da motsawar/talewar da duniya take yi sakamakon aikin "dark energy"
ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَلَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٌ فِى ٱلْمُلْكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَىْءٍۢ فَقَدَّرَهُۥ تَقْدِيرًا
Shi ne wanda yake da mulkin sammai da ƙasa, ba Shi kuma da ɗa ko abokin tarayya a cikin mulkinSa, kuma (Shi ne) Ya halicci dukkan komai......
(Alfurƙān: 2)
Da a ce sun yi imani da irin waɗannan gwala-gwalan ayoyin da Alƙur'ani maigirma ya riƙa bamu labarinsu da ba su faɗa wannan kwazazzabon ramin halakar ba. Shi ya sa duk wani abu da suka yi shakkarsa a kimiyyance ko dai ya zama akwai shi a cikin Alƙur'ani, ko kuma Alƙur'anin ya riga ya sanar da mu ba wani mahaluƙi da ya isa ya gane abin.
0.4• ƊAURAYA
Dark Energy wani abu ne da Allah (S.W.T) ya ɓoye saninsa a cikin gaibu, wanda kuma wani mahaluƙi ba zai taɓa ganowa ba! Kuma dalili ne daga cikin kimiyyar Physics a hannunmu mu musulmi da yake ƙaryata wani sashi na malaman Physics da sauran mulhidai da suke kore samuwar Allah (S.W.T), bisa dogaro da wasu gurɓatattun ƙa'idoji na ilimin falsafa wadda maguzanci da kafirci ke yiwa dabaibayi.
Idan mulhidai da ma'abota falsafa masu inkarin samuwar Allah (S.W.T) suka ce babu Allah, saboda babu wata shaida da za ta kama hankalinsu su yarda da abin da ido ba ya iya gani, sai mu ce musu: dukkanin malaman kimiyya na kowane (ba Physics kaɗai ba) sun yarda kuma sun yi imani da samuwar baƙin ƙarfi (dark energy) kuma sun gamsu da irin aikin da yake, wanda ya ke kaso 70% da energy ke yi wajen taimakawa duniya ta yi motsi ta tale ta ƙara girma. Idan suka bugi ƙirji suka ƙaryata Physics, to su sani sun ruguza kimiyya kacokan ɗin ta, domin duk wani dalili da suke riƙewa (irin gurɓatatttun dalilansu) ka kimiyya turken da suke komawa su ne Big Bang, Very Beginning da Kimiyyar Physics.
#KimiyyaDaAddini #DarkEnergy
#AdamSharada #Physics
(C) Adam Sharada
17 Muharram, 1444
15 August, 2022
Comments
Post a Comment