TSIRAICIN MACE: TSAKANIN MUSULUNCI DA TURAWAN YAMMA
[Saƙon ranar mata ta duniya na shekarar 2021]
Ƴanci mafi girma da ya cika sharuɗɗan majalisar wargaza duniya [UN] da Bankin Duniya [WB] da ma asusun PARIS CLUB da sauran ƙungiyoyi da hukumomin kare haƙƙoƙin mata da yara, shi ne kare mace daga cusgunawa da wulaƙantawa, ta hanyar tursasa musu zinace-zinace da cin zarafi a tsakanin al'umma! Addinin Musulunci wanda Allah [S.W.T] ya turo Annabi Muhammad [S.A.W] ya koyawa duniya, shi ne tilon addini da ya fita zakka sama da shekaru 1442 wajen wannan aiki, da yau Amurka da ƴan ma'abbanta suka ɗakko!
Mace wata kadara ce katafariya mai tsadar da kuɗi ko mulki ba su iya mallakawa ɗan adam kusantarta [na sha'awa], face an cika sharuɗɗa na SHARI'A! Saboda wannan tsadar da mata ke da shi ne ya sanya Allah [S.W.T] ya iyakance waɗanda za su iya ganin kwalliyarta ta al'ada ma, ba wai tsiraicinta ba:
وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ ۖ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ ۚ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
[Suratun Núr: 31]
A cikin mutum 12 da Allah [S.W.T] ya amince su ga kwalliyar mace babu friend, babu classmates, babu maƙocinsu, babu abokin kasuwanci, babu mai ɗaukar hoto, babu masu gyaran gashi, babu masu kwalliya [make up artists]! Ballantana ta je ta yi rawa a gaban maza, ballantana ta yi fim ta tafi location, ta cire mayafi a ɗauke ta a kyamara tana rawa da waƙa da murmushi da sunan koya tarbiyya! Saɓanin yadda mata ke yawo tsirara a titunan Pennsylvania da New York da Texas da Arizona da London da Geneva da Paris da Berlin da duk duniya, sanye da guntun sikel ba kallabi [ɗan kwali] ba rigar mama da sunan ƴanci da wayewa.
Saboda kiyaye Mace da Namiji daga cakuɗa nasaba, sai Allah [S.W.T] ya halasta AURE ya kuma haramta zina! Bayan ya halasta ma, ya ware wasu nau'ikan mutane ya haramta aure tsakaninsu da mace, don girmama nasaba da yin lissafi mai tsafta na dangi:
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُم مِّنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمْ تَكُونُوا دَخَلْتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَن تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
[Suratun Nisá'i: 23]
Idan ka koma ADDINAI karakatattu za ka same su tamkar wata matattarar bariki, wajen ƙazanta da rashin kunya da rashin tarbiyya da ma rashin hankali game da abin da ya shafi tsiraicin mace! Eh mana! Akwai ƙazanta irin uba ya kwanta da ƴar cikinsa ta haihu kuma ya nunawa duniya wannan abin bajinta ne? Har ma abokai da dangi su haɗu su sha bikin suna! Misali, shahararrun ƴan ƙwallon tamolar nan Christiano Ronaldo da Lionel Messi sun haifi ƴaƴansu ne ba ta hanyar aure ba [cikin shege] amma da su da iyayensu da danginsu, har da sakarkarun magoya bayansu musulmi suna alfahari da haihuwar!
Yayin da zina take da hukuncin HARAMCI a SHARI'AR MUSLUNCI, a gurin TURAWA kuwa ba komai ba ce face jin daɗi da nishaɗin rayuwa! Don haka ne ma a gurinsu idan mace ta amince namiji ya sadu da ita, wannan ba laifi ba ne a United Nations da World Bank! Laifi shi ne a tursasa ta a yi mata FYAƊE! Shi ya sa yau a duniya har ma a ƙauyuka irin Najeriya ƴan daɗi arna ba su da aiki sai maganar fyaɗe! Alhalin statistically kafin a samu case na fyaɗe guda 1 an yi ZINA guda dubu a garuruwan Musulmi. Ɗakunan hotels da aka samar don matafiya masu yada zango, yanzu sun zama cibiyar zinace-zinace da lalata ƴan mata a duniya, ciki har da Nijeriya ta Arewa. Amma ƴan daɗi arna marubuta, masu SHARHI, manazarta, ƴan jarida da masana Shari'a ba za ka taɓa jinsu suna yakar zina ba! Saboda a gurin iyayen gidansu zina nishaɗi ce da jin daɗi tsakanin friends da lovers.
Ƙazantar maɗigo [mace ta nemi mace] wadda ko a cikin ƙazaman kafiran ma, sai dafaffiyar ƴar iska ce take aikatawa; a gurin WOMAN RIGHT ORGANISATIONS [masu fafutukar kare haƙƙin mata da nemo musu ƴanci] wannan ba komai ba ne face nisaɗi! United Nations da WORLD BANK suna ta fafutukar yin dokar auren jinsi a ƙasashen musulmi, don raba mace Musulma da addininta mai tsada!
Ƴan drama na Kannywood sun zama dillalan lalata ƴan mata Musulmi! Suna ɗebo ƴan mata daga ko ina masu kyauwn jiki da za su iya motsa sha'awar ɗa Namiji, su saka su a fim! Inda suke motsa jikinsu da salon jan hankalin namijin da ke kallonsu, ana biyansu ƴan silallan da ba su taka kara sun karya ba! Duka wannan sunansa ƴanci da wayewa da kuma gogayya da ake so mata su koya! A gurin Musulmi wannan shi ne keta alfarmar mace da ƙasƙantata da zubar da ajin da Allah ya ba ta akan titi.
A cikin igiyar tarihin Musulunci, Annabinmu Muhammad [S.A.W] ya kare mace daga dukkanin wani yanayi ko aiki da zai wahalar da ruhuinta da gangar jikinta! Saboda halittar mace halitta ce ta kwalliya da ado da jan hankali da samun nutsuwa [ta aure] da nishaɗantuwa tare da ita. Saɓanin yadda yau aka hana su Malala Zai aure, ake yawo da su duniya ba kallabi ba gyale suna fafutukar kare haƙƙin Mata da nemo musu ƴanci!
Mu Musulumi muna ƙara godewa Allah da ya ba mu addinin Musulunci da Annabinmu Muhammad [S.A.W] a matsayin jagoranmu. A Musuluncimu dama can mace mai tsada ce. Ba wani fanni na rayuwa wanda Manzon Allah [S.A.W] bai sanya mata ba. A cikin Alƙur'aninmu akwai SURATUN NISA'I da ta keɓanci mata kai tsaye. Suratu Maryam [sunan Nana Maryam ya maimaitu sau 34 Alƙur'ani] kuwa sunan Mace ta ci, amma a cikin Bible [New Testament] babu GOSPEL OF SAINT MERRY! A cikin Sahabbai 5 mafiya ruwaito Hadisan Manzon Allah [S.A.W] akwai Nana A'ishah [Hadisanta 2210]. Annabi Muhammad [S.A.W] ya bawa mata muƙamai, ya koya musu karatu, ya ƴanto su daga kisa da tsangwama, ya halasta musu sadakinsu ya yi umarni a kyautata musu, ya ma fi kowa kyautata musu.
Babbar manufar da ke ƙarƙashin SHARI'AR MUSLUNCI shi ne a samu rayuwa ta jin daɗi a duniya, sannan a samu irinta a lahira. Malaman Usulul Fiƙh suna da wata ƙa'ida da ke cewa:
وكل أمر نافع قد شرع
وكل ما يضرنا قد منع
Duk abin da zai amfane mu a duniya da lahira da gangar jikinmu da ruhinmu, to Shari'ar Muslunci ta umarce mu da aikata shi [ko umarnin WAJIBI, ko MUSTAHABBI ko MUBAHI]. Kuma duk abin da zai cutar da mu duniya da lahira da gangar jikinmu da ruhinmu, to Shari'ar Muslunci za ka samu ta hana mu aikata shi.
Don haka duk wani ƙulle-ƙullen makirci na ƙoƙarin raba mace Musulma da hijjabinta da niƙabinta, da sunan GWAGWARMAYA ko wayewa, ba komai ba ne face halasta zina da maɗigo da sauran dangogin ɓarna. Ku kalli ƴan daɗi arna da ke ta ihun ana danne mata, ba sa magana akan zina da maɗigo da rashin aure da karuwanci, domin a gurin Amurka da Isra'ila halal ne kuma wayewa ne!
Ya ke ƴar uwa Musulma, ki riƙe addininki da hijjabinki da mutuncinki! Kada ki yarda a raba ki da Annabi Muhammad [S.A.W]! Kada ki yarda a ce ki cire hijjabinki da niƙabinki, ki fito a fafata da ke, ki zama mai izza da addininki da Musuluncinki da hijjabinki. Ki roƙi Allah ya ba ki miji nagari, ki yi aurenki ki ci gaba da rayuwar ibada, kina yiwa mijinki kwalliya da fara'a da kwarkwasa da girki da kissa da rausaya ana rubuta miki lada! Ki nisanci ƴan fim yaran Yahudawa ne da ake amfani da su, don a raba ki da iyayenki da mutuncinki, a raba ki da aure da karatun Alqur'ani da zaman lafiya! Darajarki da tsadarki ta fi ƙarfin a ga kwalliyarki idon duniya kina rausaya da rangwaɗa. Allah [S.A.W] ya yi miki alƙawarin lada mai girma idan ki ka kiyaye shari'arsa:
إِنَّ الْمُسْلِمِينَ وَالْمُسْلِمَاتِ وَالْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَالْقَانِتِينَ وَالْقَانِتَاتِ وَالصَّادِقِينَ وَالصَّادِقَاتِ وَالصَّابِرِينَ وَالصَّابِرَاتِ وَالْخَاشِعِينَ وَالْخَاشِعَاتِ وَالْمُتَصَدِّقِينَ وَالْمُتَصَدِّقَاتِ وَالصَّائِمِينَ وَالصَّائِمَاتِ وَالْحَافِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَالْحَافِظَاتِ وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
[Suratul Ahzáb: 35]
Alherin Allah ya kai gare ku zaɓaɓɓun Mata ma'abota kamun kai da kamala, masu rufe tsiricinsu. Ma'abota hijabi da niƙabi.
© Adam Sharada
08/03/2021
Comments
Post a Comment