CETO ILIMIN PHYSICS DAGA KAFIRCIN STEPEHEN HAWKING
[Abin da ya kamata Musulmi masu alhinin mutuwarsa su sani]
TAƘAITACCEN TARIHINSA
An haifi Mal. Hawking ranar 8 ga Janairu, 1942 a Oxford ta Birtaniya, ya kuma rasu ranar 14 ga Maris, 2018 a birnin Cambridge na dai Birtaniya. Ana lissafa STEPHEN HAWKING a sahun ragowar ƴan mazan jiya na duniyar kimiyya. Masana na ganin a wannan ƙarnin duniya ba ta ga malamin kimiyya irin STEPHEN HAWKING ba, ta fuskar zurfin ilimi da tunani da kuma kaifin ƙwaƙwalwa. Wasu ma na ganin, bayan ALBERT EINSTEIN [1879-1955] baban Relativity, ba a ga wani mayataccen Physicist kamarsa ba. Hawking ya yiwa tsarekunsa fintinkau, inda ya kutsa cikin duniyar kimiyyar Physics, a lokacin da ake ganin an gama ƙulle ƙofa, har ma ya kawo wani gagarumin sauyi da sabunta bincike, waɗanda suka sauya akalar abubuwa da yawa a duniyar Physics da Sama-Jannati [Astronomy].
GUDUNMAWARSA
Daga cikin irin abubuwan da STEPHEN HAWKING ya kawo waɗanda ba wanda ya gabace shi wajen gano su akwai:
1- Hawking Radiation: Hawking ya gano cewa, kimiyyar Physics game da zafi [Thermodynamics] na da MUHIMMIYAR rawar takawa wajen nazarin Baƙin Rami [Black Hole]. Ya tabbatar da cewa; duk abin da ke iya juya zafi ko tasarrufin zafi a kewaye da shi, to zai iya fitar da zafi. Don haka Black Hole, tunda yana da yanayi [Temperature], to kuwa akwai zafi kewaye da shi! Don haka shi ma yana fitar da zafi [Radiation].
A nan ne ma ya yiwa Albert Einstein gyara na kuskuren da ya yi game da RELATIVITY ɗinsa da ke cewa: "ba wani abu ko sinadari [particle] ko ma zafi da zai iya kuɓuta daga kamun Baƙin Rami [Black Hole]" Idan ka gwada wannan da abin da Hawking ya gano, za ka gane EINSTEIN ya gaza! Domin Black Hole yana fitar da zafi, don haka sunansa Black body [A material which emit radiation and give it out], kenan akwai abin da ke iya fita daga jikin baƙin ramin.
2- Theory of Everything: Zurfafa bincikensa ga wasu asalai tabbatattu a Physics [constants] da suka ƙunshi: Newton's constant, Planck's constant, Einstein's relativity da kuma Boltzman constant; bisa jagorancin Zurfafa tunani, su suka sa ya gano "Theory of Everything"
Wannan theory shi ne ya tattara kana ya dunƙule dukkanin wasu Equations da Relations da Formulae na Physics a guri guda! A nan ne Stepehen Hawking ya tabbatarwa da duniyar Physics cewa: zurfafa bincike game da BLACK HOLE, shi ne kaɗai zai sa a fahimci haƙiƙanin ƙa'idojin da ba a kai ga fahimtar ƙeƙe da ƙeƙensu ba a kimiyyar Physics.
Wannan ta sa malaman Physics suke wa wannan theory nasa take da "The unlock secret of nature"
3- History of Time: Asali malaman Physics sun yi ijma'i akan cewa: indai General Theory of Relativity daidai ne, to kuwa a can cikin Baƙin Rami [Black Hole] dole a samu wani guri wanda za a samu farraƙu tsakanin space [guri] da time [lokaci]. Ta yadda daga nan sai dai a riƙa hasashen adadinsu, ba tare da sanin taƙamaimai ɗinsu ba. Daga nan kuma maganar duniyoyi [Universe] ya zama babu kenan, tunda sun narke a cikin kaunu [ikon Allah]. Wannan hasashen shi ake cewa SINGULARITY. A nan Stephen Hawking ya gano cewa, indai aka juya akalar lokaci [reverse time's arrow], to kai tsaye za a iya hasaso lokaci da guri [Space and Time] daga Universe. Don haka SINGULARITY shi ne tushe mafi girma game da nazarin alaƙar UNIVERSE da Black Hole [Baƙin Rami]. A nan ne ma Hawking ya rubutuwa duniya littafinsa "Brief History of Time".
Waɗannan kaɗan ne cikin irin rawar da Stepehen Hawking ya taka a duniyar kimiyyar Physics, wadda ta sa sunansa ya zama rayayye abin tunawa da ambato.
KAFIRCI DA SAƁON STEPEHEN HAWKING
Mu Musulumi da ma mun kwana da sanin duk wanda bai yi imani da shika-shikan Musulunci 5 da rukunan Imani 6 ba, to wajibi ne ka same shi yana munana zato ga Allah, ta hanyar shirka da kafirci. Stepehen Hawking da yake baƙin arne ne, Kimiyyar Physics da abubuwan da ya gano na ƙudira da ikon Allah, ba su sa ya miƙa wuya ga Allah [S.W.T] ba, sai ma ya ƙara fanɗarewa, ya shiga zagin Allah da ma kore samuwarsa.
Misalin maganganunsa na kafirci suna haɗa da:
1- A cikin littafin "The Grand Design" wanda Hawking shi da Leonard Mlodinow suka yi haɗin gwiwa suka wallafa, Hawking yana cewa:
"Because there is a law such as gravity, the universe can and will create itself from nothing. Spontaneous creation is the reason there is something rather than nothing, why the universe exists, why we exist. It is not necessary to invoke God to light the blue touch paper and set the universe going."
Gaɓa ta 1:
Inda yake cewa: "Because there is a law such as gravity, the universe can and will create itself from nothing."
A nan gurin Hawking yana iƙirarin: duniyoyi sun halicci kansu ne da kansu. Wannan kuwa zunzurutun ƙarya ne da jahiltar tushen ilimin PHYSICS, wanda asalinsa shi ne jahiltar Allah [S.W.T]! Da a ce Stephen Hawking ya yi tunani mai kyau game da NEWTON'S FIRST LAW OF MOTION [da ba zai yi wannan kasassaɓar ba!] da ke cewa:
"if a body is at rest or moving at a constant speed in a straight line, it will remain at rest or keep moving in a straight line at constant speed unless it is acted upon by a force."
Wannan law yana nufin ba wani abu da yake motsi da kansa, dole sai an samu sababi da zai sanya abun ya motsa! Motsi ya fi sauƙi sama da samar da abin da zai yi motsin daga babu. Physics ya yarda komai ba ya faruwa sai da sababi. Don haka Allah [S.W.T] shi ne sababin samuwar komai, ba su suka samar da kansu ba!
A addinmu na Musulunci, wannan magana KAFIRCI ne, domin Alƙur'ani ya faɗa mana cewa:
اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ
Allah shi ne ya halicci komai, kuma Shi ne mai wakiltar komai.
[Zumar: 62]
Komai shi muke kira everything da turanci a kimiyyar Phsics, duk wani abu da hankali zai iya tunowa a guri da lokaci [Space and Time], to Allah [S.W.T] ne ya samar da shi, ba shi ya samar da kansa ba! Jahiltar Allah [S.W.T] da kangarewa saƙon Musulunci da rashin sanin Alƙur'ani, su suka sa kasasshe tauyayyen hankali irin na su Hawking ke raya cewa, komai shi ya samar da kansa.
Gaɓa ta 2:
Inda Hawking ke cewa: "It is not necessary to invoke God to light the blue touch paper and set the universe going"
A nan kai tsaye yana cewa bai ma yarda da samuwar Allah [S.W.T] ba!
Wannan zindiƙanci ya ci karo da tubalin da aka gina shi kanshi ilimin PHYSICS akai! Domin asalin abin da ake cewa PHYSICS shi ne nazarin kimiyyar komai [matter] bisa la'akari da tasirin ƙarfi [energy] wajen gudanarsu a kaunu [Universe]. Mafi yawan Laws da Equations na Physics kai tsaye suna nufin ikon Allah wajen tasirin ƙarfi game da motsawar abubuwa.
Da a ce da gaske babu Allah, ai da ba wani abu da zai faru akan wani sharaɗi da Physics ke ta nanatawa! Da a ce babu Allah, da Stepehen Hawking ya wanzar da kansa a duniya, ta yadda zai ci-gaba da bincike a Theoritical Physics da Quantum Mechanics. Da a ce babu Allah, da ISAAC NEWTON bai gane tasirin ikon Allah game da motsi ba, da malaman Physics ba su gane haske ya fi komai gudu ba, da acceleration due to gravity [9.8 m/s] bai samu a cikin kaunu ba! Da gravitational force bai janyo abu mai nauyi ya faɗo ƙasa ba, yayin da ya tashi sama! Akwai misalai dubunnai, in sha Allah, za mu tattauna su a faɗaɗe daga duniyar Physics a wani lokacin daban.
2- A cikin littafin "Brief History of Time" Stephen Hawking ya kuntuka wata kasassaɓar kamar haka:
"If we discover a complete theory, it would be the ultimate triumph of human reason -- for then we should know the mind of God."
A nan Hawking yana nufin ɗan adam zai iya sanin abin da Allah ya barwa kansa sani (gaibu), da gwargwadon sanin da ya yiwa Physics! Wannan ƙarya ce wadda Physics tun daga tushe ya ƙaryata ka ya kai Stepehen Hawking! Alal misali: a Physics akwai abubuwa da yawa waɗanda ba a san haƙiƙaninsu ba, sai dai hasashe kawai ake da dabaru! Misali:
Duk yadda aka juya, ba wani Physicist har shi Stephen Hawking ɗin, da ya isa ya ce ga "gravity" ko ga "force of gravity" ko ga "energy" ko ga "mass" da makamantansu ba, sai dai zato da hasashe [expectations]. Akwai misalai da yawa a fannoni mabanbanta na Physics.
A Alƙur'anance kuwa mu Musulumi Allah [S.W.T] ya faɗa mana:
إِنَّ اللَّهَ عِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ الْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْأَرْحَامِ ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ مَّاذَا تَكْسِبُ غَدًا ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ بِأَيِّ أَرْضٍ تَمُوتُ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ
Lallai a gurin Allah ne ILIMIN [yaushe ne] ALƘIYAMA yake, kuma shi ya ke saukar da ruwan sama, kuma shi ne ya san abin da ke cikin mahaifa [na ɗa/ƴa], babu wata rai da ta san me zai faru gobe, kuma babu wata rai da ta san a ina ne za ta mutu......
(Luƙman: 34)
Wannan aya tana ƙaryata duk wani KAFIRI da ya ke zaton wai zai iya sanin GAIBU!
Stepehen Hawking yana da miyagun aƙidu a matsayinsa na KAFIRI zindiƙi! Waɗanda abin mamaki hatta Physics ɗin da ya ƙware a cikinsa in mun koma sai mu ga yana ƙaryata shi.
ƊAURAYA
Don muna karanta kimiyyar Physics ko wani fanni na boko, hakan ba ya nufin mu fifita wannan ilimin akan abin da yake shi ne Musuluncinmu, wanda muka gada daga Alƙir'ani da sunnar Annabi Muhammad [S.A.W]. Yana da kyau mu riƙa gina muƙamin soyayya da ƙiyayya akan abun awo na Shari'a.
Fatanmu Allah ya tsare mana imaninmu da Musuluncinmu.
© Adam Sharada
14/03/2021
Comments
Post a Comment