ALJANNA TA IYA MUSULMI CE! [ Warware shubuhohin Aliyu Samba game da shigar wanda ba Musulmi ba Aljanna ]
أعوذ بالله بسم الله والصلاة والسلام على رسول الله، وبعد
A ƙoƙarin ya ba ni amsa ta ilimi kan da'awar da muka ci karo yana yaɗawa ta shigar wanda ba Musulmi ba gidan Aljanna ranar alƙiyama, ya kawo ayoyi guda 2 a Alƙur'ani mai girma.
AYA TA FARKO: A cikin suratul Baƙarah aya ta 62:
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالنَّصَارَىٰ وَالصَّابِئِينَ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Wannan aya ko kaɗan ba ta inda a zahirinta da mafhuuminta, take ba da lasisin Aljanna ga wanda ya mutu a akasin MUSULUNCI!
Domin Yahudawa, Nasara da Sabi'awa da Allah [S.W.T] ya ambata, ai a daidai gurin ya saka musu sharaɗi:
مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا
"Waɗanda suka yi imani da Ranar Lahira, kuma suka yi aiki na-gari"
Wannan kuma shi ne MUSULUNCI, wanda Allah [S.W.T] ya aiko Annabawansa don su isarwa duniya! Tsakani da Allah, ta wace fuska ne wannan ayar za ta shigar da wanda ba Musulmi ba gidan Aljanna? Shin wanda ba Musulmi ba dama shi ne
مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا؟
Ai wannan ayar ma tana RUGUZA mummunar fikirar da Aliyu Samba yake ƙoƙarin ginawa ne, wadda ta saɓa da manhajin Annabawa da kuma saƙonsu na Annabta!
Ka koma dukkanin littattafan tafsirin Alƙur'ani da muke da su a duniyar Musulunci, babu wani Mufassiri da ya taɓa kasassabar yiwa Alƙur'ani irin wannan cushen! Sai Aliyu Samba yau ya zo da abin da duk duniyar Musulunci ba wanda ya rigaye shi, sama da shekara 1400, kuma yake da'awar shi ne gaskiya.
Ga misalan maganganun malaman Tafsiri karkashin wannan ayar:
1- Ibn Katheer Rahimahullah:
لما بين [ الله ] تعالى حال من خالف أوامره وارتكب زواجره ، وتعدى في فعل ما لا إذن فيه وانتهك المحارم ، وما أحل بهم من النكال ، نبه تعالى على أن من أحسن من الأمم السالفة وأطاع ، فإن له جزاء الحسنى ، وكذلك الأمر إلى قيام الساعة ؛ كل من اتبع الرسول النبي الأمي فله السعادة الأبدية ، ولا خوف عليهم فيما يستقبلونه ، ولا هم يحزنون على ما يتركونه ويخلفونه ، كما قال تعالى:
( ألا إن أولياء الله لا خوف عليهم ولا هم يحزنون ) [ يونس : 62 ]
وكما تقول الملائكة للمؤمنين عند الاحتضار في قوله:
( إن الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا تتنزل عليهم الملائكة ألا تخافوا ولا تحزنوا وأبشروا بالجنة التي كنتم توعدون ) [ فصلت : 30 ]
2- Ibn Jareer Aɗɗabariy Rahimahullah:
قال أبو جعفر: يعني بقوله: (من آمن بالله واليوم الآخر)، من صدق وأقر بالبعث بعد الممات يوم القيامة، وعمل صالحا فأطاع الله, فلهم أجرهم عند ربهم. يعني بقوله: (فلهم أجرهم عند ربهم)، فلهم ثواب عملهم الصالح عند ربهم
3- Al-Imamul Ƙurɗubiy Rahimahullah
Ya tattauna mas'aloli 8 a ƙarƙashin ayar, mas:'ala ta 6 a ciki ita ce:
السادسة : قوله تعالى : من آمن أي : صدق . و " من " في قوله : " من آمن " في موضع نصب بدل من " الذين " . والفاء في قوله : " فلهم " داخلة بسبب الإبهام الذي في " من " . و " لهم أجرهم " ابتداء وخبر في موضع خبر " إن " . ويحسن أن يكون " من " في موضع رفع بالابتداء ، ومعناها الشرط . و " آمن " في موضع جزم بالشرط ، والفاء الجواب . و " لهم أجرهم " خبر " من " ، والجملة كلها خبر " إن " ، والعائد على الذين محذوف ، تقديره من آمن منهم بالله . وفي الإيمان بالله واليوم الآخر اندراج الإيمان بالرسل والكتب والبعث
Waɗannan kowannensu hujja ne a fagen Tafsirin Alƙur'ani mai girma. Aliyu Samba yana buƙatar ya kawo mana irinsu, da suka yiwa ayar fahimtar da ya yi mata!
Ai ko a ka'idojin ƳANCIN TUNANI DA AUNA ABUBUWA DA HANKALI [Free Thinking]; aiko da Manzannin ga duniya AIKIN BANZA ne, indai wanda bai karɓi saƙonsu ba ma zai shiga aljanna! Don Allah ka auna a hankalinka, Annabi Nuhu [A.S] ya shafe shekaru 950 yana wa'azi, amma wanda bai yi imani da shi ba ma zai shiga aljanna! Annabi Musa [A.S] ya sha gwagwarmaya da FIR'AUNA, amma ƙarshe FIR'AUNA ma zai shiga aljanna! Wannan tunani yana da matukar hatsari ga asalin imani!
2- AYA TA BIYU: A cikin suratu Aali Imran aya ta 114, inda Allah [S.W.T] yake cewa:
يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَأُولَٰئِكَ مِنَ الصَّالِحِينَ
Wannan ayar itama babu ta inda za ta bawa kafiri lasisin shiga gidan Aljanna, gidan da Allah [S.W.T] ya tanada ga waɗanda suka yi imani da saƙon TAUHIDI da SUNNAH!
Da a ce Aliyu Samba da masu irin fahimtarsa sun nazari zahirin ayar nan a mustawan lafiyayyen hankali, da ya bayyana a gare su cewa: tana yiwa da'awarsu raddi ne! Domin ƙarara itama ta ambaci IMANI da AYYUKAN ƊA'A a matsayin SHARAƊIN da ya bawa waɗancan YAHUDAWA DA NASARAN lasisin rabauta da ALKHAIRI! Ai wanda ya cika sharaɗin IMANI da AYYUKAN ƊA'A ya tashi daga tsohon sunan KAFIRCI zuwa MUSULUNCI!
Mu koma maganganun MUFASSIRUN mu ɗan tsakuro misalan yadda suka fassara ayar:
1- Al-Imamul Ƙurɗubiy Rahimahullah:
يؤمنون بالله يعني يقرون بالله ويصدقون بمحمد - صلى الله عليه وسلم - .
ويأمرون بالمعروف قيل : هو عموم . وقيل : يراد به الأمر باتباع النبي - صلى الله عليه وسلم - . وينهون عن المنكر والنهي عن المنكر النهي عن مخالفته . ويسارعون في الخيرات التي يعملونها مبادرين غير متثاقلين لمعرفتهم بقدر ثوابهم . وقيل : يبادرون بالعمل قبل الفوت . وأولئك من الصالحين أي مع الصالحين ، وهم أصحاب محمد - - صلى الله عليه وسلم - في الجنة .
2- Ibn Katheer Rahimahullah:
وهؤلاء هم المذكورون في آخر السورة : ( وإن من أهل الكتاب لمن يؤمن بالله وما أنزل إليكم وما أنزل إليهم خاشعين لله [ لا يشترون بآيات الله ثمنا قليلا أولئك لهم أجرهم عند ربهم إن الله سريع الحساب ] ) [ الآية : 199 ]
Mu Ahlussunnah Salafiyyah da muke cewa: dole sai an koma Alƙur'ani da Hadisi ingantacce a bisa fahimtar magabata na-gari an cirato addini: muna ƙudirce cewa Aljanna Allah ya tanade ta ne KAWAI ga Musulmi waɗanda suka cika sharuɗɗan Musulunci 5 da na Imani 6
Addinin Musulunci shi ne addinin da Allah [S.W.T] ya aiko dukkanin Annabawansa da Manzanninsa su isarwa duniya. Kamar yadda ya bayyana ƙarara a cikin Alƙur'ani mai girma:
إِنَّ الدِّينَ عِندَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ ۗ وَمَا اخْتَلَفَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۗ وَمَن يَكْفُرْ بِآيَاتِ اللَّهِ فَإِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
[Aali Imran: 19]
Kuma ya gaya mana har wa yau, duk wanda ya mutu ba yana Musulmi ba, to ya taɓe ba kuma zai shiga ALJANNA ba:
وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَن يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Mu Ahlussunnah Salafiyyah muna da yaƙini a zukatanmu; tunda Allah [S.W.T] ya ce duk wanda ya kuskura ya mutu ba Musulmi ba ya yi asara a lahira, ASARRRE ba zai shiga aljanna ba iya wuya! Domin waɗannan ayoyin ba ma Hadisi ba ne, ballantana a tuhumi SAHABBAI da MALAMAN HADISI, da yin cushe.
A cikin Suratu Ibrahim aya ta 23 Allah [S.W.T] ya ayyana samfurin mutanen da zai shigar gidan Aljanna:
وَأُدْخِلَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِمْ ۖ تَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَامٌ
Ƙarara Allah [S.W.T] ya ayyana mana; MASU IMANI su zai shigar gidan Aljanna! Ashe ba Ibn Taimiyah da Ibn Abdulwahhab da Wahhabiyawa ne suka kore da waɗanda ba MUSULMI ba daga samun Aljanna! Mai tuhumar ba iya MUSULMI ne kaɗai 'yan Aljanna ba, ya za ka yi da wannan ayar?
Har wa yau a cikin Suratul Hijr aya ta 45-46 Allah [S.W.T] yana cewa:
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ (45) ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ آمِنِينَ (46)
Don girman Allah mai karatu su waye masu TAƘAWA [kiyaye dokokin Allah] idan ba Musulmi ba? To Allah [S.W.T] ga shi a cikin Alƙur'ani ba a منهاج السنة ba, yana ayyana waɗanda ya zai sanya a gidan Aljanna! Kai da ka ce ba iya MUSULMI ba ne kaɗai, don Allah ya za ka yi da wannan ayar?
A cikin Suratul Baƙarah aya ta 25, Allah [S.W.T] ya sa Annabi Muhammad [S.A.W] ya yi bayanin BUSHARA game da waɗanda za su rabauta da shiga gidan Aljanna:
وَبَشِّرِ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۖ كُلَّمَا رُزِقُوا مِنْهَا مِن ثَمَرَةٍ رِّزْقًا ۙ قَالُوا هَٰذَا الَّذِي رُزِقْنَا مِن قَبْلُ ۖ وَأُتُوا بِهِ مُتَشَابِهًا ۖ وَلَهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَهُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Wanda ya ce ba iya MUSULMI ne kaɗai za su shiga aljanna ba, don Allah ina zai ajiye wannan ayar? Shi dai Allah [S.W.T] ya ce zai ba da ALJANNA ga MUMINAI [su ne dai Musulmi], kai kuma ka ce ba su kaɗai ba ne?
ƊAURAYA
Mu ji tsoron Allah, mu tuna da mutuwa da hisabin ayyuka! Ƙoƙarin rigima da Ahlussunnah Salafiyyah kada ya zama dalilin kore أصول الدين a duniyar Musulunci! Malaman Musulunci Ahlussunnah a tsawon igiyar tarihi aikinsu shi ne; ƙoƙarin mayar da musulmi zuwa ga Musulunci irin wanda Annabi Muhammad [S.A.W] ya gadarwa SAHABBANSA! Wannan kuma shi ne manufar wahayi Alƙur'ani da aiko Manzo a gare mu. Muna roƙon Allah ya raya mu akan Musulunci, ya ɗauki rayukanmu muna Musulmi, ya tashe mu muna Musulmi ranar alƙiyama.
© Adam Sharada
Comments
Post a Comment