ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] SHI NE JAGORANMU
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله على النبي الكريم، وعلى ءاله وصحبه أجمعين وبعد:
Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo Hafizahullah a muqaddimar نبي الرحمة [bugu na 3, 1434H] yana cewa:
"فتوجيهاته وأقواله صلى الله عليه وسلم، وأفعاله مصدر وتطبيق لهذا الدين، كما كان صلى الله عليه وسلم أسوة حسنة لهذه أمة..." (ص ٦)
"Umarninsa da maganganunsa [S.A.W], da ayyukansa da abubuwan da ya yi a aikace [dukkaninsu] tushe ne na wannan addinin [Musulunci]! Kamar yadda [Annabi S.A.W ya zama] ya zama KYAKKYAWAN ABIN KWAIKWAYO ga wannan al'ummar....."
Wannan haka yake! Domin kuwa Allah [S.W.T] ya tsarkake shi tun daga danginsa da ya fito! Al-Imamu Muslim Rahimahullah a cikin صحيح مسلم ya rawaito Hadisi:
«6077» حدثنا محمد بن مهران الرازي ومحمد بن عبد الرحمن بن سهم جميعا عن الوليد- قال ابن مهران حدثنا الوليد بن مسلم- حدثنا الأوزاعي عن أبي عمار شداد أنه سمع واثلة بن الأسقع يقول سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((إن الله اصطفى كنانة من ولد إسماعيل واصطفى قريشا من كنانة واصطفى من قريش بني هاشم واصطفاني من بني هاشم)).
Daga Waathilah Ibn Al-Asqa'u [R.A] yana cewa cewa: Na ji Manzon Allah [S.A.W] yana cewa: "Lallai Allah ya za6i Kinaanah daga 'ya'yan Annabi Isma'il [A.S], sai ya za6i Quraishawa daga cikin Kinaanah, sai kuma ya Banu Hashim daga Quraishawa, sai ya za6o ni daga BANU HASHIM!"
Shaikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah a qarqashin wannan hadisin yana cewa: "Saboda haka, za6a66en za6a66u ne. wato sai da aka tace , aka rairaye, aka tankade, aka bakace, sannan aka ciro shi. Sallallahu Alaihi Wa Aalihi Wasallam!" [ALAMOMIN SON MANZON ALLAH (S.A.W) shafi 15]
Ba wai a iya za6en NASABARSA da danginsa fifikonsa wajen za6e ya tsaya ba! Allah [S.W.T] ya tsarkake shi a dukkan komai, ta yadda ba shi da wata tawaya ko aibu daidai da qwayar komayya, da za ta iya tauye masa daraja da cikar kamala!
Allah [S.W.T] ya tsarkake masa HANKALINSA:
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَى
"Ma'abocinku [Annabi Muhammad] ba 6atacce [halakakke] ba ne, kuma bai kuskure ba [cikin abin da aka aiko shi na Manzanci]" [Najm:2]
Allah ya tsarkake masa GANINSA:
مَا زَاغَ الْبَصَرُ وَمَا طَغَى
"Idon [na Annabi Muhammad S.A.W] bai karkace ba, kuma bai yi kuskure ba!" [Najm:53]
Allah ya tsarkake masa HARSHENSA:
وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلْهَوَىٰٓ
"Kuma ba ya furta son-zuciya!" [Najm:3]
Allah ya tsarkake shi a za6ar masa MALAMINSA:
عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَى
"Madaukaki mai tsananin karfi shi ne ya sanar da shi [Jibril A.S]" [Najm:5]
Allah ya tsarkake masa ZUCIYARSA:
مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَىٰ
"Zuciya [ta Annabi Muhammad SAW] ba ta karyata abin da ta gani ba!" [Najm:11]
Allah ya tsarkake shi SAKONSA [Manzanci]:
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ
"Kuma ba mu aiko ka ba, face sai don ka zama jin qai ga talikai [mutane da aljanu]" [Anbiyaa':107]
Rayuwarsa wata katafariyar Jami'a ce da duniya ke ninqaya a cikinta! Dabi'unsa su ne dabi'un dan adam mafiya kyawu da burgewa da aka ta6a gani a tarihin duniya. Amaryarsa Nana A'isha [R.A] ta ba shi shaida da fadinta:
كان خلقه القرءان
"Dabi'unsa su ne ALKUR'ANI!" [Imam Ahmad, Musnad]
Haka zalika, Manzon Allah [S.A.W] ya kasance:
رحيما بالعيال
"Mai jin qan iyalinsa [matansa da 'ya'yansa]" [Abu Dawud Addayaalisiy, Musnad]
Hadiminsa, dan gidansa, almajiransa kuma masoyinsa mai daraja Sayyidina wa Maulana Anas ibn Malik [R.A] ya tabbatar mana da kyawawan siffofinsa:
كان أحسن الناس
"Ya fi kowa kyautatawa cikin mutane [S.A.W]"
وأجود الناس
"Ya fi kowa kyauta a cikin mutane"
وأشجع الناس
"Ya fi kowa jarumta a cikin mutane"
[Ruwayar manyan zakunan nan: Bukhari da Muslim]
Duk wani na aibu ko tawaya da dan adam ke iya samu, bai ta6a samunsa ba kuma ba shi da shi [S.A.W]! Shi ne mai kyautar da ba ya tsoron talauci, ba a tambayarsa ya ce babu. Ya fi kowa kiyaye dokokin Allah! Ya fi kowa adalci da DAIDAITO. Shi ne shugaban da ya bawa mata 'yanci, ya tabbatar da haqqoqin dan adam, ya yaqi qabilanci da WARIYAR LAUNIN FATA, ya yaqi miyagun ayyukan jahiliyya Kamar Zina, Luwadi, Madigo, Fyade, Giya, Caca, cin mushe, kisan kai, da yake-yake.
Ya karantar da Addini tsawon shekaru 23 tskaanin Makkah da Madinah. A loton ba wutar lantarki, babu injinan tattara bayanai. Ba na'urorin nada da adana labarai. Ba kayan sufuri, ba komai na ci-gaban duniya! Amma har yanzu wannan KARANTARWA tana nan bayan shekaru 1440 ba tare da ta yi ko da kura ba! ALKUR'ANI da Allah [S.W.T] ya ba shi a matsayin mu'ujiza, shi ne mafi wanzuwar littafin da ya dawwama a duniya ba tare da an iya sauya ko da wasalinsa ba! Shi ne shugaban da ya tsallake sikelin duniya kakaf! Makiyansa sun masa kyakkyawar shaida tun daga mushirikan Makkah, har zuwa mushirikan Amurka da Burtaniya a yau.
Shaikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah yana cewa:
"Binsa shi ne tsira, yin imani da shi, shi ne lasisin shiga Aljannah ranar Alqiyama" [ALAMOMIN SON MANZON ALLAH (S.A.W) shafi 8]
Za mu ci gaba in sha Allah!
© Adam Sharada
14-07-2020
Comments
Post a Comment