RANAR YAWAN AL'UMMA TA DUNIYA
Yau Juma'a 11/07/2020 Majalisar Dinkin Duniya [UN], wanda yake maimaituwa duk shekara. A bana UN to mayar da hankali wajen wasu manyan batutuwa da suka shafi jama'a. Biyu daga ciki da na ga dacewar mu yiwa TARKE [Criticism] su ne:
1- TAKAITA HAIHUWA
A gurin YAHUDAWAN DUNIYA, yawan da al'ummar musulmi ke kara yi ba qaramar barazana yake musu ba! A binciken wani Bayahude JEFF DIAMANT wanda cibiyar PEW RESEARCH CENTRE ta wallafa [April 1, 2019] shi da kanshi yana cewa:
" _The two lists show that the global Muslim population is more heavily concentrated in Islam’s main population centers than the global Christian population is for Christianity, which is more widely dispersed around the world. Indeed, about two-thirds (65%) of the world’s Muslims live in the countries with the 10 largest Muslim populations, while only 48% of the world’s Christians live in the countries with the 10 largest Christian populations._ " Wannan ta sa suka qara qaimi wajen ganin sun cimma nasarar takaita haihuwa a tsakanin musulmi.
Mu kuma musulmi shugabanmu da ba shi da tamka; Annabi Muhammad [S.A.W] ya yi mana wasiyya:
"Ku auri mata masu haihuwa. Domin ni zan yi alfahari da yawan al'umma ranar alqiyama!"
Saboda YAHUDU da NASARA su ne mafiya asara da ta6ewar halittun Allah: UN ta daurewa ZINA, LUWADI, MADIGO, GIYA da dukkanin wata kazanta tsakanin al'ummon duniya, saboda su dama burinsu su halakar da mutane daga bin tafarkin Allah! Yau a duniya ba inda aka fi yin CIKIN SHEGE da haife 'ya'yan gaba da fatiha irin kasashen AMURKA da Urubba! Tare da wannan qazantar a tsakaninsu kuma suke qoqarin kautar da tsaftatacciyar hanyar samuwar dan adam ta AURE.
Allah [S.W.T] tuni ya fada mana irin wadannan makirce-makircen na MASONIYYAH da 'yan barandansu a fadinsa:
ولا يزالون يقاتلونكم حتى يردوكم عن دينكم انستطاعوا
"Kuma ba za su gushe ba suna yakarku [ku musulmi] har sai sun raba ku da addinin ku idan za su iya!" [Bakarah: 217]
Wannan mummunan hakan nasu da yardar ba zai cimma ruwa ba.
2- DAIDAITA TSAKANIN JINSI
Majalisar UN algunguma munafuka ta koka game da yadda WAI ake nunawa Mata wariya, ake danne su kuma ake mayar da su baya a wasu kasashe! Wannan tsantsar rashin kunya ne da bankaura irin ta KAFIRAI!
Babu wadanda suka cancanci a soke su wajen rashin girmama jinsin mutane kamar TURAWAN YAMMA, wadanda suka halasta kazantar MADIGO, LUWADI da AUREN JINSI, saboda zukatansu na cike da cutar kafirci da maguzanci! Allah [S.W.T] ya tona musu asiri su da kansu Yahudawan a cikin littafinsu HOMOSEXUALITY AND RELIGION: An Encyclopedia, marubucinsu arne Jeffrey A. Siker ya rubuta a makalarsa [page 146] cewa: "The religious and legal status of same-sex marriages and same-sex unions
has been one of the most controversial and divisive issues within Western culture at the
end of the twentieth century and the beginning of the new millennium." Idan har da kunya, kuna da bakin magana akan DAIDAITA TSAKANIN JINSI A DUNIYA?
Tsiraita Mata akan titunan Albama da New York a Amurka shi ne wayewa da 'yancin? Wannan shi ne daidaita jinsin? Mu a Addininmu na Musulunci Mace wata kadara ce mai katafariyar qima da tsada! Don haka ne ma Allah [S.W.T] ya rufe ado da TSIRAICIN MACE, ta yadda ba wanda zai rabauta da gani ko kusantarta sai mijinta! Musulmi mu qara godewa Allah da ya sanya mu cikin mabiya Annabi Muhammad [S.A.W], wanda shi ne mafi adalci da nagarta a cikin shugabannin da sauran mutanen da duniya ta gani! Shi ne jagora mafi girma da ya tabbatar da DAIDAITO TSAKANIN JINSI!
A cikin addinin Musulunci ba BALARABEN URUBBA daidai yake da BAKIN BA'AUZINI SUDANIY a gurin Allah! Kadai wanda ya fi daraja shi ne wanda ya fi tsoron Allah! Alkur'ani ya tabbatar da wannan ka'idar a cikin ayar da ta ambaci:
إن أكرمكم عند الله أتقاكم
Lallai wadanda suka fi matsayi daga cikinku [ku mutane] a wajen Allah, su masu mafiya taqawa [wadanda suka fi kiyaye dokokin Allah] [Hujraat: 13].
Addininmu na MUSULUNCI bai zo da qabilanci ba! Amma dukkanin sauran ADDINAI 6atattu kamar Kiristanci, Judaism, Skhism, Jainism, Buda da sauran tarkacen sun ginu akan baqin qabilanci! Mu kuwa idan aka koma tarihin shugabanmu Masoyinmu Annabi Muhammad [S.A.W], za a samu girmama jinsin qabilu da kalar fata da yankunan mutane a cikin rayuwarsa da karantarwarsa.
A cikin MATAN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] Nana Safiyyah bnt Huyay [R.A] ba Balarabiya ba ce, ta fito daga cikin Yahudawan Banun Nadheer. kuyanginsa: [S.A.W] akwai Nana Mariyah Alqibdiyyah [R.A] ba Balarabiya ba ce. Nana Raihanah [R.A] itama ba Balarabiya ba ce. Ladaninsa Bilal ibn Rabah [R.A] ba Balarabe ba ne! Sahabi mafi ruwayar Hadisai Abu Huraitata [R.A] ba su hadi gari ko yanki da shugabanmu ba! Haka suke barkatai cikin Sahabbai kamar yadda daliban ilimi suka sani.
Kabilanci da WARIYAR LAUNIN FATA sun kare a AMURKA da URUBBA! Su Martin Luther King sun sha wahalar fafutuka a America wajen nemawa BAKAKEN FATA 'yanci! Amma a baya-bayan nan duk duniya irin kisan da Amurkawa maguzawa suka yiwa BAKAR FATA, saboda WARIYAR LAUNIN FATA [Racial segregation ko Racism]. Misalai suna nan dubunnai da duniya ta kiyaye daga arna makiyan Musulunci da yadda suke azizita wutar wariyar launin fata a kasashensu.
DAURAYA:
Musulmi mu riqa samun kwarin gwiwa game da Addininmu. Mu tashi mu yi karatu na Addini da ba Boko don tunkarar qalubale da ilimi. Sannan mu yi qoqari mu gyara miyagun halaye da dabi'unmu a dukkan komai. Mu gina kanmu wajen dakko ilimi daga duniyar sani zuwa duniyar aiki. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi, ya karya kafirci da kafirai.
©️ Adam Sharada
11/07/2020
physicsp33@gmail.com
Comments
Post a Comment