HAR YANZU AFIRIKA MUNA SARKA! [Ranar Afirika ta Duniya 26 May]

  Nahiya mai tulin ma'adinai, kasar noma, yawan al'umma, manyan dama-damai, kyakkyawan yanayi da arziki! Mun sha bakar wahala a loton istidmariyya bayan munafikin dan akarada AFRICANUS ya guntsawa turawan JAMUS, BIRTANIYA, FOTUGAL, BELJIYOM da sauransu munafurcin abin da ya zo ya riska na ka6akin arziki da ni'ima. Garnaqaqin Farfesan tarihi Mal. Walter Rodney a cikin HOW EUROPE UNDERDEVELOPED AFRICA ya tona mana asirin yadda TURAWA suka yi mana dirar mikiya, suka ruguza mana shirinmu, duka daidaita mutuncinmu, suka wulakanta mu, suka maishe mu bayi, suka halasta mutuncin matanmu, suka ruguza hatta tsarin shugabancinmu, suka yi cushe a cikin daulolinmu, suka lalata tunaninmu, suka kashe malamanmu da jagororinmu, sannan suka halasta mutuncinmu ta hanyar maishe mu bayi karfi da yaji! Duk da irin CI-GABAN nahiyar Afirika tun gabanin karni na 15, da irin gudunmawarmu ga TURAWA wajen gina musu tattalin arzikinsu, hakan bai sa sun amintar da mu daga JARI-HUJJA [Capitalism] ba. Cinikayyar bayi daga Port of No Return zuwa kasashen Amurka, da Latin da Urubba; shi ne mafi munin wulakanci da kaskanci da turawa suka yi mana, wanda ya ninninka na Larabawa a gabashin Afrika! Zuciya za ta yi kuka idan tajiyi Mal. Rodini Mai Tarihi yana qoqarin gane taqamaimai miliyoyin AFIRIKAWA da aka sayarwa TURAWA da sunan bayi: "One of the uncertainties the basic question of how many Africans were imported. This has long been an object of speculation, with estimates ranging a few millions to over one hundred million." [Page 109].

  Bayan cinikayyar bayi, turawa sun yi qoqari gaya wajen daqile duk wata kafa ta ci-gabanmu ta fuskar fasaha, da yiwa tattalin arziqinmu kisan mummuqe: abin da Shehu Rodney ya kira 'Technological Stagnation and Distortion of the African Economy in the Pre-Colonial Epoch' [Page 108]. Baya ga wannan, sun dasa mana tsarin mulkin mallaka na sunquru [Imperialism], wanda yau shi yake addabarmu tun bayan sun gama kwashe komatsansu a shekarar 1960 kacokan daga nahiyarmu! Wannan shi ne zalunci mafi girma da kisan mummuqe da TURAWA suka yi mana tsawon shekaru sama da dari. Bature MUNAFIKI ne ANNAMIMI da ya hana AFIRIKAWA mu sakata mu wataya a duniya! Da wannan fikirar ne suka haddasa mana rikice-rikecen Kabilanci, Siyasa da Addini a kusan dukkanin Afirika. A shekarar 1993 bayan turawan BELJIYOM [Belgium] sun tashi daga RWANDA, sun haddasa rikicin Kabilanci tsakanin kabilun HUTU da TUTSI, inda HUTU suka kashe 'yan TUSTSI kimanin miliyan daya a kasa da watanni 3, gabanin zuwansu ba a taba sanin wani abu Kabilanci ba a Rwanda! A shekarun 1967-1970 suka haddasa yaqin basasa a Nijeriya [Nigerian-Biafra Civil War], wanda ya samo asali daga juyin mulkin da Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu dukkaninsu Inyamurai kamar yadda dan kabilarsu Mal. Emefiena Ezeani ya tabbatar a cikin littafinsa  'In Biafra Africa Died' [page 21] suka yi yunqurin juyin mulki wanda ya kaisu ga kashe jiga-jigan Arewa guda 2; Sardaunan Sokk Firemiyan [Premier] jihar Arewa da Shugaban Kasa [Prime Minister] Tafawa Balewa, ranar 1 Janairu, 1966: Chikumeka Ojukwu ya shelanta samuwar kasar Biyafra [Biafra], wanda ya sabbaba gumurzun basasa har aka kashe Inyamurai [Igbo] da sauran talakawa 'yan ba ruwana miliyoyi, in ji marubuci Al J. Venter a littafinsa 'Biafra's War [1967-1970] A Tribal Conflict in Nigeria That Left a Million Dead'. Yau yakin Basasar Biyafra ya kare amma Inymaurai sun gina 'ya'yansu da jikokinsu akan wani karin maganarsu "Nwata tonite amaghi ihe mere nna ya, ihe mere nna ya emee ya" ma'an "Duk yaron da ya girma bai san abin da ya faru ga tsohonsa ba, to abin da ya faru ga tsohonsa zai faru gare shi!" Wato kenan su zama cikin shirin ko-ta-kwana! Wannan aqida ta KABILANCI ita tasa marubucin duniya Inyamuri Mal. Chinua Achebe kan ya bar duniya ya wallafa wasiyya ta kundin Biyafra Mai suna 'There Was a Country: A Personal History of Biafra'. Bayansa an samu daruruwan marubutansu suna ta rubuce-rubuce wadanda suke alamta sake rura wutar rikici da yamutsi, kamar yadda dan jaridar nan dan Andalus Frederic Forsyth ya riqa ishara a littafinsa 'The Biafra Story: The Making of an African Legend'. Banda wannan dambarwa, mafi yawan shiyyoyin Nijeriya na fama da rikicin Kabilanci, Siyasa da Addini. Idan aka ware rikice-rikecen Benue, Wukari, Niger-Delta, Lagos, Boko Haram, Barayin Shanu, Garkuwa da Mutane: akwai kuma RIKICIN JOS tsakanin BIROM [Kiristocinsu da Maguzawansu da tsirarun musulminsu] da kuma HAUSA/FULANI [Musulmi], wanda yake sauya salo tsakanin KABILANCI, ADDINI da SIYASA! Matsalar JOS ta rikita marubuci Ahmad Hassan Jos wanda ya kasa tantance taaqamaimai tushenta guda daya a littafinsa 'RIKICIN JOS: Addini ne, Siyasa ne, Ko Kabilanci ne?'.

Idan muka kara kallon taswirar kasashen Afrika a yau, za mu qara firgita da irin zaman samarkwatai da TURAWA suka yi a cikinmu! Kalli faduwar gwamnatin Ghaddafi a Libya, da yadda yau Libiyawa ke kukan ina ma su sarayar da duk abin da suka mallaka don a dawo musu da ushurin tsarin gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi! Sudan bayan sun datsa ta 2, basu haqura ba sai da suka damalmala SUDAN suka daidait adalin shugaba UMAR ALBASHIR, suka kifar da gwamnatinsa. Haka suka a Misra suka daidaita Husn Mubarak, suka kifar da gwamnatinsa. Tunisiya, Mali da Chadi duka basu ku6uta ba.  Wannan shi ne yaqin sunquru ta fuskar ruguza tunanin mutane [Clash of Ideology], wanda ya zama siyasar diflomasiyyar kasashen ketare [Foreign Policy] a kwanakin gwamnatin Shugaban Amurka sumumu-kasau Barrack Obama. Idan muka sa gilashin hangen nesa, za mu ga kacokan sun hana Nahiyar Afirika zama lafiya, tunda suka qyalla ido suka gano arziqinmu shekaru dubu baya zuwa yau! Kasar Afrika ta Kudu, da ake dan sa wa a gaba, sun dasawa mutanen ta aqidar KYAMAR BAKI [Xenophobia], wadda ta sabbabawa kasar komawa baya sosai ta fuskar diflomasiyya da fada a ji! A nutse idan muka duba, za mu gane cewa: sun raba hankalin mu, sun dasa mana gaba, kiyayyar juna, da rashin mutunta ko girmama juna! A lokacin da kasa irin JAMUS [Germany] da ke tsakiyar Urubba [Europe] ta mallaki Kamfanoni da masana'antu [Industrialization] a cikin kasarta, wadanda da za a tattara na Afirika baki daya, a dukkanin kasashen mu sama da 30, ba za su kai 1/10 nasu ta fuskar adadi, karfi, inganci, ci-gaba da karbuwa a duniya ba! Gwari-gwari; sama ta yiwa yaro nisa!

Ni a zuciyata ina da yaqinin muddin shugabanninmu da talakawanmu a NAHIYAR AFIRIKA za su dauki wasu matakai, lallai za mu iya kwato kanmu, za mu mallaki gashin kanmu, za mu tsara ci-gabanmu, za mu dinke barakarmu, kuma za mu daga likkafar nahiyarmu.

Ina bamu shawara ta fuskoki kamar haka:

1- SIYASA: Allah ya albarkaci Nahiyar Afirika da kungiyar KASASHEN AFRIKA ta AU [African Union] wadda aka haifa tun ranar 25/05/1963, wadda ke da kasashe mambobi guda 30 in ji Mal. Ayo Akinbobola marubucin maqalar International Relation a cikin Elements of Politics [page 352]. Lallai wannan majalisa ta kara kaimi wajen tabbatar da manyan manufofin nan nata guda 5 da suka qunshi: 1- Ci-gaban Afirika ta fuskar hadin kai 2- Tabbatar da tsaftatacciyar rayuwar 'yan Afirika 3- Kare mutuncin kasashen Afrika a matakin duniya 4- Kokarin kawar da duk wani nau'i na mulkin mallaka daga nahiyar Afirika 5- Ha66aka dangantar matakin duniya tsakanin Afirika da Majalisar dinkin duniya UN [Elements of Politics: Page 354-355].

Bayan nan, shugabanninmu su yi qoqari wajen kawar da miyagun dabi'u ta fuskar siyasa da shugabanci musamman CIN HANCI DA RASHAWA, SIYASAR GADO [Political system of rating], da qoqarin wadata kai ga wanda ya samu madafun iko.

2- KABILANCI: Allah [S.W T] shi ne ya yo mu kabilu mabanbanta! Bai kamata bambancin kabila ko yanki, su zama sababin kiyayya da gaba a tsakaninmu ba. Duk sasannin duniya mu muka fi kowa baiwa ta arziqin al'ummomi da al'adu! Mu yi qoqari mu kyautata zamantakewarmu, mu ci-gaba da fito da kyawawan al'adunmu, sannan mu yi aiki tuquru wajen yakar bakin AL'ADU da miyagun TA'ADU a sutturarmu, a abincinmu, a dabi'unmu, a cimakarmu, a iliminmu a komai namu!

3- TATTALIN ARZIKI: Shugabanninmu da manyan attajiran da Allah ya bamu, su fi mayar da hankali wajen kafa masana'antu da Kamfanoni a kasashen mu! Su tsuke kansu daga yo cefane ko zuba hannun jari a kasashen Turai da Asiya. Su wadata mu da duk wasu kayan amfani da dan adam ke bukata. Ta haka ne rayuwa za ta kara sauqi, talauci zai ragu, sannan aikin yi zai samu tsakanin talakawa marasa aikin yi. Wannan zai taimaka wajen kakkabe ta'addanci da yake yiw Nahiyar Afirika barazana!

4- NOMA DA KIWO: Da yawan kasashen mu Allah ya albarkace mu da kasar noma, yalwataccen ruwan sama da tamfatsa-tamfatsan dama-damai na noman rani! Shugabannin kasashen mu da attajiranmu su daure su karfafi Noma da Kiwo domin wadata nahiyarmu da yalwataccen abinci da nama! Ina da yaqinin a cikin shekaru 10 da za mu habbaka bangaren nomarmu, wallahi da sai mun daina yo cefanen shinkafa'yar Kura a kauyukan Tailan [Thailand] da makotanta!

5- ILIMI: Uwa-uba na dorewar kasashen Afrika kenan! Wajibi ne shugabannin kasashen mu da masu zuba jari a harkar ilimi, su kara kaimi wajen habbaka bangaren ilimi tun daga tushe, tare da bashi cikakkiyar kulawa ta kashi 25% na kasafin shekara, ta yadda za mu iya gogayya da kasashen duniya! Ba abin da zai wanzar mana da ci-gaba da zaman lafiya irin ILIMI tsakanin al'ummonimu. Shugabanninmu su takaita fitar 'yan AFIRIKA karatu kasashen Turai. Su karfafi harkar ilimi, su habbaka harkokin bincike  ta hanyar samar da cibiyoyi a jami'o'inmu, sannan a tabbatar da ana amfani da abubuwan da masana suka sha wahalar fitarwa na ilimi.

Ina da yaqinin muddin shugabanninmu za su saka bukatun al'umma a gaban bukatunsu, talakawa za mu daina sayar da 'yancinmu, za a yaki Karuwanci da Lutsu da Shaye-shaye, matasa za su kama sana'a, kowa da kowa zai yiwa kanshi hisabi ya gyara munanan halayensa a sirrance, to nan kusa ba da jimawa ba kasashen Afirika masu man fetur [Petroleum producers] irin Nijeriya za su fara nunawa Amerika da Swizalan [Switzerland] da Cana [China] yatsa a kungiyar OPEC da G11 da makamantansu. In sha Allah ba da jimawa kasashe irin Burundi, Malawi da Cape Verde za su mallaki makamin kare dangi [Nuclear Weapons) Nuclear for War]. Birane irin Kano a Nijeriya da Maputo a Burkina Faso da Cotanou a Republique de Benin; za su yi gogayya ko su kere biranen Berlin na Jamus da Rome na Italiya da Madrid na Andalus. In sha Allah nan ba da jimawa ba unguwanni irin IKEAJA ta Lagos da Kurmin Mashi ta Kaduna da Dambua ta Maiduguri, za su fara gogayya da irin su Ankara ta Turkiyya da Bairro Alto na Portugal da makamantansu! In sha Allah nan gaba kadan garin SHARADA da ke cikin birnin Kano zai yi gogayya da garuruwa irin su Tokyo na Japan da Reinnes na Faransa da Guadalajara a Mexico da Croydon a London.

Da fatan Allah ya shiryi shugabanninmu, ya shirye mu mu mabiyan. Allah ya kakkabe mana TURAWAN YAMMA da duk wani dan kwangilarsu a tsakaninmu. Allah ya bamu arziki da zaman lafiya mai dorewa a nahiyarmu.

#INTERNATIONAL_AFRICAN_DAY
#SON_OF_AFRICA
#AFRICA_MY_HOME
#SWEET_AFRICA

✍🏻✍🏻RUBUTAWA
© Adam Sharada
Kano, Nijeriya
physicsp33@gmail.com
26/05/2020

Comments