"AN ZO WAJEN" A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI
A cikin ALQUR'ANI mai girma a SURATUL ISRA'I aya ta 36, Allah [S.W.T] yana ce mana:
ولا تقف ما ليس لك به علم، إن السمع والبصر والفؤاد كل أولئك كان عنه مسؤلا
"Kuma kada ka tsaya akan abin da ba ka da ILIMI, lallai JI da GANI da kuma ZUCIYA; dukkanin wadannan sun kasance ababen tambaya akanshi [Musulmi]!"
Al-Imamul Bukhariy Rahimahullah a cikin صحيح karkashin كتاب العام, ya qulla babi mai suna باب العلم قبل القول والعمل: Babin yin ILIMI gabanin FADA [Bayyanawa] da kuma AIKI. Sai ya kawo fadin Allah [S.W.T] a cikin SURATU MUHAMMAD aya ta 19:
فاعلم أنه لا إله إلا الله
"Kuma ka SANI; lallai babu abin bauta bisa ga cancanta sai Allah"
Sai Bukhariy ya ce:
فبدأ بالعلم قبل القول والعمل
Sai [Allah] Ya fara da ILIMI gabanin MAGANA [da baki] da kuma AIKI [da ga66ai].
A nan gurin Bukhariy Rahimahullah yana nuna mana WAJABICN neman ILIMI na ADDININ MUSULUNCI game da duk wani abu da za mu aikata a rayuwarmu. Kauracewa neman sanin matsayar Allah da Manzonsa cikin al'amuran rayuwarmu, na cikin dalilan koma bayan da musulmi ke fuskanta a yau.
Abdurrahman Al-Akhdhariy Rahimahullah a cikin مختصر الأخضري [AHLARI/LAHALLARI] yana mana gargadi da fadinsa:
ولا يحل له أن يفعل فعلا، حتى يعلم حكم الله فيه
Kuma ba ya halatta gare shi [Baligi] ya aikata wani AIKI, face ya san hukuncin Allah a cikin shi.
MEYE HUKUNCIN "AN ZO WAJEN" A MUSULUNCI?
Kai tsaye a zahiri ba za ka iya HARAMTA ko HALASTA maimaita wannan sara ko yayi ba! Domin a zahiri ba ya nuna wani abu na KYAU da zai mayar da shi HALAL, ko kuma wani mummunan abu da zai HARAMUN shi!
Sai dai shari'ar Musulunci saboda tsarinta, na qoqqarin mayar da musulmi kacokan ga KARANTARWAR ANNABI MUHAMMAD [S.A WE], ba ta qarfafa biyewa irin wadannan tadodi da lafuzza! Domin yawan biye musu na iya sawa su zama jiki, a saba da su, daga nan sai su rikide su zama abin rigima ga jahilai bayan shudewar zamuna. Wannan ta sa MALAMAN MUSULUNCI ke hujja da zahirin aya ta 19 cikin SURATU MUHAMMAD da muka ambata, wajen karfafar kaurace musu da nesanta musulmi daga aikata su, don kada su tashi daga مباحات والمندوبات su zama ana tada jijiyar wuya wajen hukunta WUTA da ALJANNAH akansu. Kamar yadda mutum-mutumi don tunawa da mutanen kirki 'yan mazan jiya, ya zama sanadiyyar SHIRKA da BAUTAR WANIN ALLAH a cikin AL'UMMAR ANNABI NUHU [A.S], inda suka mayar da ود، سواءا، يغوث، يعوق da نسرا ALLOLI ABABEN BAUTA. Kamar yadda mushirikan Makkah suka ALLANTAR da mutanen kirkin cikinsu: لات، عزى da مناة, gabanin aiko Annabi Muhammad [S.A.W].
TSOKACI
Abu mafi dacewa shi ne mu qauracewa wadannan tsurface-tsurface da sababbin Sara na zamani da ake kira INGAUSA a wajen Masana KIMIYYAR HARSHEN HAUSA. Wannan shi ne fatawar Ibn Hazmin Al-Andalusiy, Shaikhul Islam Ibn Taimiyah, Shaikh Muhammad Ibn Sálih Al-Uthaimeen Allah ya gafarta musu.
Mu shagaltar da kanmu wajen asalin aikin da ke gabanmu. Allah [S.W.T] a cikin SURATUZ ZÁRIYÁT aya ta 56 yana fadi mana:
وما خلقت الجن والإنس إلا ليعبدون
"Kuma ban halicci MUTUM da ALJAN ba sai don su BAUTA min"
Mu shagaltu da yawan ambaton Allah da Salati ga FIYAYYEN HALITTA, mu kula da Sallah da azumi da dukkanin FARILLAI, sannan mu kamanta akan NAFILOLI. Mu kula da haqqin iyaye da makota da kowa. Mu riqa tunawa da MUTUWA da kwanciya a qarqashin tukwane! Sannan mu dage wajen NEMAN ILIMIN ADDINI da na zamani, tare da tsarkake niyya.
Wani mawaki mai hikima yana cewa:
العلم فيه حياة للقلوب ****. كما تحي البلاد إذا ما مسها المطر
ILIMI a cikinsa akwai raya zukata, kamar yadda GARURUWA ke rayuwa yayin da RUWAN SAMA ya sauka a cikinsu.
A koma littattafai kamar:
١- صحيح فقه السنة na Abu Málik
٢- فتاوى نور على الدرب da aka tattara fatawoyin Shaikh Uthaimeen
٣- السنن والبدع المتعلقة بالألفاظ والمفاهيم الخاطئة Fatawoyin Shaikh Uthaimeen
© Adam Sharada
10/04/2020
Comments
Post a Comment