ME YA SA AMURKA TA KASHE HAFSAN SOJOJIN IRAN QASIM SOLEIMANI???



Duk wata dasisar yaqar ADDININ MUSULUNCI da AMURKA ke kullawa MUSULUNCI, tana iya yinta wajen zaqulo wadanda za su iya taya ta wannan aikin! Idan ta dauki dan kwangila, ta ba shi kwantaragi, to tana da tsari tsayyaye na lokacin da take so ya biya mata bukatar ta!
Yau a duniya kowa ya sani ana rikici na fatar baka tsakanin IRAN da AMURKA, wanda ya kai ga sanyawa IRAN takunkimin tattalin arziqi! Amurka uwar gulma yau ta fi kowa karfin makami da tattalin arziqi a duniya, amma ba ta ta6a wani yunquri na kaiwa IRAN hari ba, kamar yadda ta yi a IRAQ, AFGHANISTAN, PAKISTAN, KISHMIR, HALAB, BURMA, PHILIPPINES da makamantansu!

Lokacin da AMURKA za ta shiga IRAQI, kawarta da suke munafurci tare wato IRAN ita ta bude mata boda, ta taimaka mata da makamai, sojoji, da aiki na kai tsaye! Ayatullaat Sistani wanda IRAN ta mayar IRAQI don a ruguza SUNNI MUSLIM, yana cikin kanwa uwar gami da sauran AYOYIN KISRA da suka hadu suka yi aiki a IRAQI, inda aka fake da rigima da SADDAM HUSAIN, aka karkashe dubban manyan malaman SUNNA, aka rugurguza ma'adanar manyan littattafan ADDININ MUSULUNCI, aka kona masallatai, aka kashe dubunnan musulmi 'yan ba ruwana! Irin aikin da ALGUNGUMIN DAN SHI'AR NAN IBNUL ALQAMIY ya yi, na hada kai da TATAR aka MURQUSHE MUSULUNCI a BAGHDAD da ma daukacin IRAQI! A rikicin IRAQI, tun daga shigar AMURKA zuwa yau, ba a ta6a komai na 'yan SHI'A ba! Shi ya sa SISTANI da sauran AYOYIN KISRA suka riqa rungumar AMURKAWA, sanda za su bar qasar!

Wani abu da ya qara fitowa fili shi ne; yadda AMURKA ta danka IRAQI a hannun SHI'A lokacin da za ta fita! Tare da cewa SUNNA su ke da rinjaye a kasar! Domin da SHI'A ke da rinjaye, ba yadda za a yi SADDAM ya yi musu irin abin da ya yi musu a kasar!

Bayan IRAN ta ji dadin awalajar POLITICS OF HYPOCRISY da suka kulla da AMURKA, sun tabbatar PLAN din dasisar yaqar ADDININ MUSULUNCI da jagoransu AYATULLAAT KHUMAINI ya tsara na murkushe Makka da Madina, zai samu idan suka hada kai da AMURKA! Wannan ta sa suka qulle qofa! A hannun guda kuma AMURKA ta janyo YARIMA MUHAMMAD BIN SALMAN, ta shiga amfani da shi don cimma manufarta na rugurguza tushen ADDININ MUSULUNCI! Idan muka nazarci rikicin SYRIA, YEMEN, LIBYA da makamantansu za mu gasgata wannan batu!

A baya-bayan nan AMURKA ta murqushe gami da kame shugaban Sudan UMAR ALBASHIR, IRAN munafuka da yake da goyon bayanta, ko jaje ba ta yiwa Musulunci ba zuwa yau! Yau Ina LIBYA ina MISRA? Iran mai makamin kare-dangi ba ta ta6a kai musu dauki ba, ba ta ta6a ma damuwa da Musuluncinsu ba, tunda ba ADDININ FARISA suke bi ba!
Kisan sojan IRAN QASIM SOLEIMANI irin kisan dan jaridar SA'UDIYYAH ne JAMAL KASHOGE! Kashoge dan kwangilar AMURKA ne da ya gaza kai bantensa na alawajar da ya dakko talla, don haka aka kashe shi ta qarqashin qasa, ta hanyar hada baki da wasu jami'an jakadancin SA'UDIYYAH a Istanbul na Turkiyyah! Shi kuma Qasim Soleimani da shi AMURKA da IRAN suka yi amfani wajen ruguza kamfanin mai na SA'UDIYYAH, sai dai TARGET MISSION din bai kai ba! Don haka suka kawar da shi, gudun tonon asiri daga shuganni irin su Rashad Tayyab na Turkiyyah!

Don ku kara yarda da MUNAFURCIN SIYASA tsakanin AMERICA da IRAN; Ayatullaat Khamna'e ya ci alwashin za su dauki fansa! Don Allah ku taya ni zuba idanu nan da shekaru 100, ku ga da gaske IRAN za ta iya kaiwa AMURKA harin ramuwa! Hizbullaat ta LEBNON da HASAN NASARULLAH [Nasarullaat] ke jagoranta tana nan! Muna jiran saukar NUCLEAR WEAPONS [Physics for War] akan YAHUDU DA NASARA, tunda dai an kasa taimakawa MUSULMIN FALASDINU an bige da zanga-zanga a Najaf, Tehran da Gyallesu!


Adam Sharada
03/01/2020

Comments