MAKARANTAR ISLAMIYYA TA SUBULUSSALAM [KHULAFA'U] DA TASIRINTA A HARKAR ISLAMIYYU A KANO
A cikin hadisin Abu Umaamah Albaahiliy [R.A] wanda Alkhadibul Baghdadiy da Ibnu Abdulbarrin da kuwa wasu suka fitar, Annabi [S.A.W] yana cewa:
..ليحمل هذا
العلم من كل خلف عدوله
Lallai [za a samu] a cikin kowane zango na mamaya [zamani] wadanda za su dauki nauyin wannan addinin, su ne masu nagartarsa...
Daga shekaru 20 aqalla zuwa yau, idan ana batun makarantun Islamiyya a cikin kwaryar Kano, wadanda suka yi qarko ta fuskar ILIMI da INGANCI; in sha Allah KHULAFA'U za ta shigo ciki a sahun gaba!
Jajircewar gogaggun malaman makarantar ta fuskar karantar da TATACCEN ADDININ MUSULUNCI daga TUSHE, da kokarin ginawa dalibai INGANTACCIYAR AKIDA wadda ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] ya karantar da almajiransa [SAHABBAI] su ne manyan dalilan dorewar makarantar!
Duk yadda yau MAKARANTUN ISLAMIYYA suke lalacewa, amma wallahi KHULAFA'U tana nan dai! Zai yi wahala ka samu DALIBI/DALIBA da suka yi KHULAFA'U suka sauke, amma ba su san baqin ALQUR'ANI ba, kamar yadda mafi yawan makarantu suke a yau! Mafi yawan abokaina na ILIMI da RAYUWA suna cikin GWALA-GWALAN kwayayen da KHULAFA'U ta qyanqyasowa duniyar ilimi, su ne ma'aunina wajen fifita makarantarsu akan wadanda mu muka yi!
Wani abu da zai ba ka mamaki ya kai mai karatu; a KHULAFA'U ne kadai za ka ga babban ma'akacin gwamnati, malamin jami'a, likita, dan jarida da sauransu suna shiga aji suna koyar da dalibai ILIMI, abin da ba saba da gani ba, a mafi yawan makarantu a cikin Kano.
Manyan malaman ADDININ MUSULUNCI a Kano, wadanda suka isa a ambata, sun yabi wannan makaranta sun qqaddara ta kuma sun saka mata albarka! Da idanuna na ga masoyina malamina jagora na-gari daga Allah SHAIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM RAHIMAHULLAH ya zo makarantar, kuma ya jinjinawa malaman game da namijin kokarinsu! SHAIKH ABDULWAHHAB ABDALLAH IMAMU AHLUSSUNNAH hafizahullah, duk yadda ya kai da zafi da fada idan ya ga AHLUSSUNNAH suna wani abu na kuskure, sai da ya sallama musu ya jinjinawa jihadinsu! Banda nasu akwai Shaikh Muhammad Nazifi Inuwa, Shaikh Dr. Muslim Ibrahim, Shaikh Professor Ahmad Murtala, Shaikh Aminu Daurawa, Dr. Bashir Aliyu Umar, Dr. Sani Umar R/Lemo da kafatanin malaman مجلس التعاون بين الدعات السلفيين suna tare da makarantar kuma suna cikin al'amarinta.
Yanzu makarantar tana sashin Boko daga Nursery zuwa Primary, tana da bangaren Tahfiz inda ko a kwanan nan ta yaye dalibai mahaddata ALQUR'ANI wadanda ko a haramin Makka za su karanta ALQUR'ANI ba za su ba mu kunya ba, tana da sashen Islamiyya na yamma, sai sashen matan aure! Masallacin MARKAZ MUHAMMAD BIN ABDULWAHHAB da ya zama cibiyar karantar da SUNNAH a yankin GWALE yana karkashin wannan makaranta mai albarka.
Yanzu haka KHULAFA'U tana da dalibai a manyan JAMI'O'IN ADDININ MUSULUNCI na duniya kamar; JAMI'ATUL ISLAMIYYA ta MADINA, JAMI'ATUL AZHAR ta MISRA da makamantansu! Wani karin abin sha'awa da burgewa, a KHULAFA'U akwai irin su MAL. RABI'U DAN-ALJANNA [in sha Allah] turmi sha daka; ya karantar da yayyen mijin kanwata shaqiqiya tun suna yara, ya karantar da qanwata da mijinta tun suna wasan kasa, yanzu haka 'ya'yan kanwata daliban ajinsa ne! Yana da irin wadannan daliban sama da 500!
Ba mu da bakin da za mu godewa daukacin malaman makarantar, sai dai addu'ar Allah ya saka musu da ALJANNA MADAUKAKIYA!
Comments
Post a Comment