KO KUN SAN WANE SAHABI NE ANAS IBN MALIK KUWA???
بسم الله الرحمان الرحيم
SUNANSA: Anas ibn Malik ibnin Nadhr ibn Dhamdham ibn Zaid ibn Haraamin ibn Jundub ibn Aamir ibn Ghanam ibn Adiyy ibnin Najjaar.
LAKABINSA: Alkhazrajiy [daya daga cikin manyan kabilun Madina guda 2], Al-Ansaariy [mutanen da suka kar6i baquncin Annabi Muhammad [S.A.W] da sahabban sa da suka yo hijira daga Makka].
ALKUNYARSA: Abu Hamzah, kamar yadda Annabi [S.A.W] ya saka masa.
MATSAYINSA: Yana cikin mafi shahara HADIMAN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W], wadanda suka sadaukar da rayuwarsu kacokan wajen taimakawa da daukar dawainiyar kula da Annabin Rahama. Ya shafe shekaru 10 na rayuwar Annabi [S.A.W] a Madina yana yi masa hidima! Ba tare da kosawa ko gajiyawa ba!
Anas ibn Malik [R.A] yana cewa: Annabi [S.A.W] ya zo Madina ina da shekaru 10.
Mahaifiyarsa Ummu Sulaimin [R.A], wadda Annabi [S.A.W] ya hango ta a gidan aljannah [Saheeh Muslim 2456]; ta kawo danta ANAS IBN MALIK [R.A] da kanta gaban Annabi Muhammad [S.A.W], don ya hidimta masa! Annabi [S.A.W] ya kar6i SAYYIDINA ANAS [R.A] kuma ya riqe shi!
Anas [R.A] yana cikin sahabbai 7 mafiya yawan ruwayar hadisai zuwa ga Annabi Muhammad [S.A.W], a cikin littattafan HADISAI na duniyar musulunci. Adadin Hadisansa 2286!
Babu wani fage na ibada, mu'amala, kasuwanci, aure, zamantakewa, akida da dukkan mu'amala, wanda ANAS IBN MALIK [R.A] bai rawaito mana wani hadisi daga Annabi Muhammad [S.A.W] a kai ba! A matsayinsa na dan cikin-gidan ANNABI MUHAMMAD [S.A.W], ya rawaito mana dubban hadisai, wadanda ba don shi din ba, da ba mu da hanyar samun su! Domin sauran SAHABBAI ba sa shiga gidan ANNABI [bayan ayar hijabi], don haka ba su san me ke wakana a cikin gidan ba! Wannan ta sa babu wani littafin HADISI ko TARIHIN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] da aka rubuta ba tare da hakaito ruwayar HADIMINSA ANAS [R.A] ba!
FALALARSA
Dukkanin wata falala da yabo da Allah [S.W.T] ya yiwa SAHABBAN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W], da wadanda Annabi ya yi musu a cikin hadisan sa, to ANAS IBN MALIK [R.A] yana ciki! Haka nan, tulin AYOYI da ingantattun HADISAI game da falalar SAHABBAI 'YAN MADINA, Sayyidina Anas [R.A] yana ciki!
Anas Ibn Malik ya halarci yakin BADAR, wanda Annabi [S.A.W] ya ce "Babu wanda zai shiga wuta cikin wadanda suka halarci BADAR"
Ummu Sulaimin [R.A] ta kawo Anas [R.A] ta ce, ya Manzon Allah ga Anas ka yi masa addu'a. Sai Annabi [S.A.W] ya ce "Allah ka yawaita dukiyarsa da 'ya'yansa, ka shigar da shi aljanna!" Anas ibn Malik [R.A] ya gasgata wannan addu'a ta Annabi [S.A.W], domin sai da ya zama hamshakin attajiri sannan ya tara 'ya'ya da jikoki kusan 100. Yana cewa, "Na ga abu 2 da Annabi [S.A.W] ya roqa min, ina fatan Allah ya ba ni na ukun [aljanna] ranar lahira!"
Ya rasu a shekara ta 91 bayan hijira a Basrah. ko da dai an ambaci sa6ani game da shekarar, amma 91 ta fi shahara. Sunan tabi'in da ya yi masa sallah Qa'dn ibn Mudrik Alkilabiy. Ya rasu a Basrah. Shi ne SAHABI na karshe da ya rasu a Basrah. Kuma shi ne sahabi na biyun karshe cikin SAHABBAN ANNABI MUHAMMAD [S.A.W] a mutuwa! Na karshen mutuwa a cikin SAHABBA shi ne Abud 'Dufail Aamir ibn Waa'ilah [R.A].
Amincin Allah ga hadimin Manzon Allah [S.A.W] ranar haihuwarka da ranar mutuwarka da ranar da za a tashe ka kana mai hidima ga shugaban halitta!
MANAZARTA
~ الإصابة في تمييز الصحابة
Na Ibn Hajr Al-Asqalaniy
[Juz'i na 1 shafi 260, tarjama 277]
~ أسد الغابة في معرفة الصحابة
Na Izzuddeen Aliyyu Ibnul Atheer
[Shafi 277 tarjama 258]
~ الاستيعاب في معرفة الأصحاب
Na Yusuf ibn Abdulbarr Annamiriy
[Juz'i na 1 shafi 109 tarjama 84]
~ صحيح مسلم
Na Imam Muslim ibnul Hajjaaj
~ سنن الترمذي
Na Imam Abu Isah Attirmiziy
DAN UWANKU:
Adam Sharada
29/11/2019
Comments
Post a Comment