ALFANUN RUFE IYAKOKIN NIJERIYA NA KAN TUDU DA HARAMTA SHIGO DA SHINKAFA
Mu 'yan Nijeriya da kullum muke kallon kawunanmu a matsayin wasu qasqantattun mutane mafiya rauni a duniya, mun tsinci kanmu a wani mummunan yanayi da gurgun tunani [lack of ideology] game da SIYASA! Kusan dukkaninmu muna zaton ADAWAR SIYASA ba ta ta6a ba da damar fadin gaskiya kan wanda akewa hamayya! Wannan mugun tunani ne da ya sa mugayen shugabannin duniya irin su Donald Trump, Bladmin Putin, Emmanuel Macron, Angela Michael da makamantansu ke yiwa AFIRKAWA kallon wasu DABBOBI!
Tun ranar 21 ga watan Agusta 2019 da shugaban Nijeriya MUHAMMADU BUHARI ya ba da umarni a rufe iyakokin Nijeriya na kan tudu da haramta shigo da shinkafa, mafi yawan 'yan kasa musamman 'YAN ADAWAR SIYASA suka mayar da batun na SIYASA!
Kasashen duniya ta fuskar TATTALIN ARZIKI sun kasu gida 3; 1- Kasashe Masu Ci-gaba [developed countries] su ne kamar Jamus, Japan, China, Amurka, Rasha, Swizaland, Canada da sauransu. 2- Kasashe Masu Tasowa [developing countries] su ne kamar NIJERIYA da tsarekunta. 3- Kasashe Masu Talauci su kuma su ne masana da masu fashin baki ke ambatonsu cikin alhini! A dunqule dukkanin kasashe masu ci-gaba har ma da matalautan kasashen kullum yunqurinsu shi ne yadda kasashen nasu za su wanzu wajen dogara da kawunansu ta fuskar komai da komai na rayuwa! Kasar Jamus [GERMANY] da ke tsakiyar Turai [central Europe] ta fuskar masana'antu, idan da za a tattara kamfanoni da masana'antu na daukacin kasashen nahiyar Afirika, ba za su kai rabin kamfanonin da JAMUS ta mllaka a cikin kasarta ita kadai ba! Tare da cewa kasar ta shiga cikin baqin kangin talauci bayan yaqin duniya na 1 [First World War]. har zuwa bayan karewar yaqin duniya na 2 [Second World War], ana kallon JAMUS a matsayin wata koma baya cikin manyan kasashen nan na G-7! Banda JAMUS akwai dubban misalai da masu karatu da bincike game da Tarihi, Tattalin Arziki da Siyasa suka sani.
Tun gabanin 1914 [zuwan Turawa NIJERIYA] yankinmu na NIJERIYA yanki ne mai kyakkyawar kasar noma, mafi yawan yankunan kasar na iya yin noma sau 2 a shekara guda! Bayan kasar ta tsaya a matsayin kasa cikakkiya [Republic] ana yiwa kasar tamu kirari da KASAR NOMA [Agrarian Environment]! A loton da Turawan Fotugal [Portugal], Ingila [England], Andalus [Spain] da Beljiyom [Belgium] da 'yan uwansu mugaye suka yiwa yankinmu mulkin mallaka [Colonialism] sun ba wa kasarmu fifiko ne saboda abin da suka gani na KYAKKYAWAR KASAR NOMA [Fertile Soil] da tulin Ma'adinai [Mineral Resources] da kuma uwa-uba MAN FETUR [Petrol]. Manyan garuruwa irin Kano, Fatakwalda Legas su suka zama hedikwatar safarar kayan masarufi da AUDUGA zuwa URUBBA!
Dalilai kwarara daga binciken masana Tarihi [History], Tattalin Arziki [Economy] da Labarin Kasa [Geography] kamar Walter Rodney, Toyin Falola da wasu sun tabbatar da cewa; yankin yammacin Afirika [inda NIJERIYA take] ya taka rawa wajen ginuwa da kafuwar tattalin arzikin nahiyar Turai tun zamanin mulkin mallaka na bakin zalunci [istidmariyya]. A kidayar 2006 [Gwamnatin Obasanjo [1993-2007] an kidaya 'yan kasa kimanin MILIYAN 115 [115 million population]. Yau kuma [2019] bayan shekaru 13 kacal, adadinmu ya kai miliyan 250! Jihar Kano tana da mutane sama da 15, tare da cewa kullum baki na kara kwarara [urban migration] daga wajen jihar da kuma yankunan karkara zuwa birni. Tare da haka, har yanzu noman da ake yi a jihohin AREWA 19, ba ya iya isar jihohin a shekara guda! Kullum 'yan kasuwarmu suna kan hanyar cefano SHINKAFA daga kasashen THAILAND da VIETNAM suna kawota kasar da 2/3 na tutarta ma KORE ne [alamar noma] ne!
Akwai gagarumar matsala idan kasa irin tamu, mai yawan al'umma irinmu, mai yalwatacciyar kasa, mai kasar noma mai kyau; a ce ba ma iya ciyar da kanmu abinci! Yayin da duk duniya ake fama da matsin tattalin arziki [Economic Crises], shi ne lokaci mafi dacewa da ya kyautu shugabannin kasarmu su kalli abin da zai ci-gaba da wanzar da NIJERIYA a matsayin dunqulalliyar kasa mai cin gashin kanta! Kasashen da ba su kaimu karfi ba, ba ma su kama kafarmu a ci-gaba ta kowacce fuska, suna ta yunqurin toshe kasashensu da alkinta arizikin da Allah ya ba su. Kasashen Afirika kannen kannemu wadanda mu muka yi tsayuwar gwamen jaki wajen haihuwarsu irin su Muzambik [Mozambique], Angola, Laberiya [Liberia] da Salo [Sierra Leone]; ba sa kuka irin namu! Tare da cewa, abin da ake juyawa na KUDI a Kano kadai cikin wata guda, ya ninninka abin da kusan 55% na sauran kasashen AFIRIKA ke juyawa a shekara guda kacal!
To don Allah sai yaushe kenan za mu farka???```
Powered by:
Comrade Adam Sharada
Physics department, Bayero University Kano
Comments
Post a Comment