BARAZANAR FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD GA ADDININ MUSULUNCI
Repost: 28th Jan., 2022
00|| MATASHIYA
Waɗanda suke karanta tarihi sun sani cewa: an yi wani lokaci a tarihi wanda addinin Musulunci sai da ya zauna da ƙafarsa a daular Andalus (Spain) tsawon shekaru 840. Wannan daula ta fitarwa da duniyar musulunci manya-manyan malamai kamar su Ibn Hazm (456 BH), Ibnul Arabiy Almālikiy (638 BH), Ibn Abdulbarr Annamiriy (463 BH), Al-Imamul Ƙurɗubiy (671 BH), da sauransu masu tarin yawa. A shekarar 1492 CE aka kafa dokar fatattakar al'ummar musulmi daga Spain mai suna Alhambra Decree. Manyan masallatai kamar masallacin Ƙurɗuba (Cordoba) aka mayar da su coci gurin zagin Allah (S.W.T). Ta kai bayan an kashe miliyoyin musulmi, hatta waɗanda ke kwance a maƙabarta ma kafirai suka ce ba ma buƙatar ƙasusuwansu! Haka aka tone gawarwakin musulmi aka watsar. Amirul mu'uminana ya wayi gari akan karagar sarauta, amma kafin yamma an saka masa sasari a wuya ana kaɗa masa ƙararrawa a kasuwar bayi!
Shi ya sa adībin malaman Andalus Abul Baƙā' Arrandiy (684 BH) a cikin waƙensa na ta'aziyyar faɗuwar Daular Andalus yake cewa:
وَلِلحَوادِثِ سلوانٌ يُهوّنُها
وَما لِما حَلَّ بِالإِسلامِ سلوانُ
"Duk wani abun baƙinciki akwai wani abu da zai iya sanya ka farinciki bayansa, amma abin da aka yiwa musulunci (na baƙinciki a Spain) ba wani abun farinciki da zai sa a manta da shi."
Mu koma mu karanta رثاء الأنداس ta Abul Baƙā' Arrandiy akwai darussa masu tarin yawa a ciki.
Abin tambaya, meye ya janyo aka yiwa musulmi irin wannan wulaƙancin a Andalus (Spain)?
Masana tarihi cikin musulmi suna cewa daga cikin manyan dalilai akwai:
للنساء نصيب فى سقوط الأندلس وقد تدخل بعضهن فى شئون الحكم فنشرن البغضاء والصراعات من وراء الكواليس، كما نشر بعضهن الفساد والانحلال. ومنهن ولادة بنت المستكفى
Lalacewar tarbiyyar ƴaƴa mata (musulmi) ta hanyar aikata fasadi (zina, maɗigo, bayyana tsiraici da dangoginsu) da raye-raye (harkar fim)......
01|| AMFANI DA MATA A WASAN KWAIKWAYO NA KANNYWOOD
Daga cikin mafi girman hanyoyin da dandazon arnan duniya (Masoniyyah) suka tsara domin ruguza ruhin addinin Musulunci akwai; amfani da mata wajen halasta fasiƙanci da manufar karkatar da tunanin matasa Musulmi zuwa ga saɓon Allah da gwangwajewa da holewa.
Tun a muƙaddimar littafin The New World Order, sai da marubucin R. Epperson ya ambaci yadda Yahudawan Masoniyyah suka tsara yin amfani da mace, don ruguza tarbiyyar al'umma:
"homosexual marriages will be legalized; parents will not be allowed to raise their
children (the state will;) all women will be
employed by the state and not allowed to
be "homemakers"; divorce will become exceedingly easy and monogynous marriage."
(Page xx)
Ga shi nan: Za a halasta auren luwaɗi. Za a sa ƴaƴa su bijirewa iyayensu. Za a sa mata su zama ƴan kwalta (ƴan iska), ta hanyar hana su aure. Za a yi ta yiwa matan aure barbarar tunanin su kashe aurensu. Sannan za a cusawa mutane auren mace 1 tal!
A cikin littafin da Yahudawan Masoniyyah (Freemasonary) suka rubuta mai suna The Protocols of the Learned Elders of Zion, wanda ya ƙunshi kundin tsarin mulkar duniya (Protocols) guda 24. Akwai Protocol na 14 da suka yiwa take da:
The religion of the future. Future conditions of serfdom. Inaccessibility ofknowledge regarding the religion of the future. Pornography and theprinted matter of the future.
Idan muka kalli waɗannan misalai na mummunan hadafin Yahudawan Masoniyyah akanmu, muka kalli yadda ƴan wasan Hausa na KANNYWOOD suka ɗauki gabarar cikawa Yahudawa burinsu, dole hankalinmu ya tashi mu riƙa tuna mummunar faduwar da musulunci ya yi a Andalus.
Za mu kawo misalai guda 5 domin ankarar da al'ummar Musulmi:
1- HANA ƳAN MATA AURE
KANNYWOOD suna hana ƴaƴan musulmi ƴan mata aure, ta hanyar sanya su cikin fim. Matan da galibinsu ko dai sun isa su kai ƴaƴansu ɗakin miji, ko kuma sun tara zuriya suna zaman aure zaman ibada. Amma an dasa musu muguwar fikirar yin sana'ar fim, don su yi suna a cikin al'umma.
2- HALASTA BAYYANA TSIRAICIN MATA
Sanannen hukunci ne daga Alƙur'ani maigirma da Sunnar Manzon Allah (S.A.W) cewa: Haramun ne mace ta bayyana kwalliyarta sai ga wasu ɗaiɗaikun ayyanannun mutane waɗanda nassi ya cire:
وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ ۖ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ ۚ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
(Suratun Nūr: 31)
A daidai wannan lokacin kuma ƴan wasan kwaikwayo na KANNYWOOD sun zama dillallan halasta tsiraicin mata da bayyana adon mata a idon duniya. Yau tsiraicin mace ya zama halal, sakamakon muguwar saƙar mutanen nan dillallan Yahudawa. Yau shigar tsiraici ta zama wata wajibi-wajibi ga ƴan mata musulmi. Wannan kuma ya sabbaba hauhawa da nunnunkuwar zinace-zinace da maɗigo, waɗanda manya-manyan zunubai ne a shari'ar Musulunci.
3- RAWA DA WAƘA
Dukkanin malaman Musulunci da bambance-bambancen mazhabobinsu sun haɗu akan haramcin mace ta yi rawa da waƙa a gaban jama'a. Manyan malamai na wannan zamanin namu kamar Shaikh Uthaimeen, Shaikh Bn Bāz da Shaikh Sāleh Fauzān dukkanninsu sun haɗu akan haramci, ta hanyar istinbaɗi daga cikin nassoshi na shari'ar Musulunci (Alƙur'ani da Hadisi).
A finafinan KANNYWOOD ake zuba ƴaƴan musulmi mata baligai da shigar tsiraici mai motsa sha'awa, suna tiƙar rawa suna jujjuya gaɓɓan jikinsu ana ɗaukarsu a video camera! Ta kai yanzu ba ma kallon wannan masifar a matsayin laifi, saboda an sabar mana da ita.
4- KOYI DA ƊABI'U DA AYYUKAN YAHUDAWA
Daga cikin kashedin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya riƙa maimaitawa gare mu har akan shimfidarsa ta ajali, akwai gargaɗinmu game da kwaikwayon Yahudawa. Finafinan masana'antar KANNYWOOD dalili ne da ke tabbatar da cewa ba su ji wannan gargaɗi da wasiyya ta Manzon Allah (S.A.W) ga al'ummarsa ba!
5- KEƁANTA DA MATA
Mu dai a musulunci irin wanda Annabi Muhammad (S.A.W) ya gadarwa Sahabbai ƴan gatan Allah, su kuma suka rawaito mana; Haramun ne mace ta keɓanta da wanda ba muharraminta ba. Kuma Haramun ne mace ta yi tafiya ba tare da muharraminta ba!
Al-Imamul Bukhariy sarkin malaman Hadisi Rahimahullah a cikin Sahihul Bukhariy hadisi mai lamba ta 3006 daga sahabi Abdullahi Ibn Abbas (R.A):
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ : " لَا يَخْلُوَنَّ رَجُلٌ بِامْرَأَةٍ، وَلَا تُسَافِرَنَّ امْرَأَةٌ إِلَّا وَمَعَهَا مَحْرَمٌ ". فَقَامَ رَجُلٌ فَقَالَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، اكْتُتِبْتُ فِي غَزْوَةِ كَذَا وَكَذَا، وَخَرَجَتِ امْرَأَتِي حَاجَّةً. قَالَ : " اذْهَبْ فَحُجَّ مَعَ امْرَأَتِكَ "
Tun daga tafiye-tafiye zuwa harkokinsu, da killace kansu a guraren ɗaukar fim (location) da sauransu, idan ka ɗora su akan sikelin musulunci na Alƙur'ani da Hadisi za ka tabbatar mutanen nan suna rigima ne da abin da Manzon Allah (S.A.W) ya shekara 23 yana ginawa! Wannan dalili ne da yake tabbatar da KANNYWOOD ma'aikatan Yahudawa ne a tushe da reshe.
Idan za mu yi ta kawo misalai a ƙarƙashin wannan gaɓar, za mu ɗauki lokaci. Amma za mu faɗaɗa a karo na gaba in sha Allah.
02|| ƊAURAYA
Mu tsaya mu yi tunani mu auna wannan masifa da aka mayar da birnin Musulunci irin Kano cibiyar yaɗa ta, da kuma shimfiɗar da muka yi game da dalilin faɗuwar Daular Andalus ta Musulunci. Za mu tabbatar lallai zaune ba ta same mu ba! Da fatan za mu shirya daƙile wannan masifa a tsakaninmu.
© Adam Sharada
28th Jan., 2023
Comments
Post a Comment